'Yadda aka kashe matata da yarana shida'

Hukumomi a Najeriya sun fara bincike kan kisan wata mata mai suna Fatima Abubakar da ƴaƴanta shida, ɗaya daga cikin kashe-kashe na bayan-bayan nan da ya ja hankalin al'umma, musamman a arewacin Najeriya.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumomi suka ce wasu matasa sun kutsa gidan Malam Bashir Haruna da ke Unguwar Chiranci Ɗorayi da ke birnin Kano tare da yin kisan, lamarin da ya jefa al'ummar jihar cikin alhini.
Tuni shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da lamarin, sannan ya bayyana alhini, tare da kira da a gaggauta gudanar da bincike domin tabbatar da hukunci.
Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin mummunan rashin imani da rashin tausayi, wanda ya girgiza al'umma da ma ƙasa baki ɗaya kuma ya saɓa wa ƙa'idojin bil'adama.
Tinubu ya nuna matuƙar alhini kan wannan mummunan iftila'in, tare da miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan.
Shugaban ya kuma yaba wa rundunar ƴansandan Najeriya bisa gaggawar ɗaukar matakin da ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin.
Ya umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a cikin kisan a gaban kotu.
'Na bar wa Allah'
BBC ta samu zantawa da mijin matar da aka kashe tare da ƴaƴanta mai suna Bashir Haruna, wanda ya ce ya ɗauki lamarin a matsayin jarabawa daga Allah, sannan ya ce ya miƙa komai zuwa ga Allah.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewarsa, "Ina godiya ga dukkan waɗanda suka mana ta'aziyya da jaje. Allah ya saka musu da alheri, Allah ya saka musu da gidan aljanna."
A game da yadda lamarin ya faru, ya shaida wa BBC cewa lokacin baya gida, domin "na riga na fita daga gidan na tafi kasuwa wajen sana'ata."
Ya ce waɗanda ake zargi da aika-aikar sun shirya ne suka shiga gidan, "tun da Allah ya taimaka an fara gano waɗanda ake da zargi da aikata kisan, ka ga na gida ne. Sun shiga gidan ne sai suka kulle," in ji shi.
Hukumomin ƴansanda sun bayyana cewa ɗaya daga cikin mutanen da aka kama bisa zargin hannu a kisan mutanen bakwai yana da dangantaka da iyalan.
Malam Haruna ya ce a lokacin da ya fita daga gida, sai ya tafi kasuwa, "na saro kaya na koma shago, amma da na fita ma wayata babu caji. Sai daga baya ne aka faɗa min cewa in yi sauri in tafi gida. Ina zuwa ne na ga abin da Allah ya yi."
Sai dai ya ce ya amince da lamarin a matsayin ƙaddara, "Lallai irin wannan za ka ji ba daɗi, amma na san Allah ne ya kawo. Na bar wa Allah. Ni na san dama Allah ne ya kawo jarabawa kuma dama asali gare shi muke."
Gwamnati ta kafa kwamiti
A nata ɓangaren, gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan.
Gwamnatin ta bayyana kisan a matsayin "mummunan aiki na rashin tausayi da rashin imani wanda ya girgiza zukatan al'ummar jihar tare da zama babban cin zarafi ga bil'adama da doka".
A cikin wata sanarwa da babban lauyan jihar kuma kwamishinan Shari'a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN ya ce bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, gwamnatin jihar ta miƙa ta'aziyyarta ga iyalan mamatan da daukacin al'ummar Kano.
''Gwamnati na tare da iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa ba za a bar su su kaɗai ba a wannan mawuyacin lokaci," in ji sanarwar.
Gwamnatin ta yaba wa rundunar ƴansandan jihar bisa gaggawar ɗaukar matakin bincike da ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin.
A cewar sanarwar, "wannan mataki na nuna ƙudirin hukumomin tsaro na tunkarar aikata laifuka da dawo da amincewar jama'a ga tsaro da adalci."
Gwamnatin ta jaddada cewa za a gudanar da shari'ar cikin gaggawa da ƙwarewa ta hannun Ofishin Babban Lauyan Jihar, inda za a kafa tawagar lauyoyi ta musamman domin tabbatar da adalci.
Waɗanda ake zargi
Tuni dai rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da kama wasu mutane uku da ake zargi da kisan.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Lahadi, ya ce kamen ya biyo bayan wani samame da jami'an ƴansanda suka gudanar bisa umarnin sufeto janar na ƴan sandan ƙasa Kayode Egbetokun.
Sanarwar ta ce, an kama waɗanda ake zargin ne bayan a wani aiki da aka gudanar da daren ranar Asabar 17 ga watan Janairu.
Ƴansandan sun ce bayan binciken farko da aka gudanar wanda aka bayyana a matsayin jagoran ƙungiyar, wanda ɗan'uwa ne ga matar da aka kashe, kuma rundunar ta ce ya amsa laifin sa.
Rundunar ta ƙara da cewa gungun matasan na da hannu a wasu munanan kashe-kashe da aka ji a jihar a baya.
Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da tufafi da ke jiƙe da jini, da wayoyin hannu guda biyu na wanda aka kashe, da adda, da kulake, da wasu kuɗaɗe da sauran makaman da ake zargin an yi amfani da su domin aikata kisan.
Rundunar ƴan sandan ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, inda ta ƙara da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.










