Cutuka biyar da ake ɗauka ta jima'i da yadda za a magance su

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Abdalla Seif Dzungu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili
- Aiko rahoto daga, Nairobi Kenya
- Lokacin karatu: Minti 6
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce cutukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i (STIs) na daga cikin manyan matsalolin da fannin lafiya ke fuskanta, yayin da a kowace rana ake samun fiye da mutum miliyan guda da ke kamuwa da cutukan waɗanda ake warkewa daga gare su.
Cutukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i, da ake samu a cikin farji da dubura ko jima'i da baki, kan haifar da mummunar matsalar da ta shafi lafiya.
A duk lokacin da aka yi maganar cutar da ake ɗauka ta hanyar jima'i galibi mutane kan yi tunanin cutar HIV, to amma akwai wasu cutuka masu hatsari da ake ɗauka ta hanyar jima'i baya ga HIV.
Ga wasu jerin manyan cutaka biyar masu hatsari da ake dauka ta hanyar jima'i da yadda za a warke daga gare su.
Gargaɗi: An tsara labarin nan ne domin faɗakarwa kawai. Amma don neman shawara ko yadda za a warke daga cuta a tuntuɓi ƙwararren likita.
1. HIV/AIDS
AIDS matsananciyar cutar ce da ake samu sakamakon ƙwayoyin cuta masu karya karya garkuwar jiki (HIV).
A cewar WHO, ƙwayar cutar HIV kan raunata garkuwar jiki, ta yadda garkuwar jikin za su kasa yaki da duk wata cuta da ta tunkari jiki.
Akan yaɗa cutar HIV ta hanyar haɗuwar jinin wanda ke ɗauke da cutar, ko ta hanyar maniyyi ko ruwan cikin farjin mace.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Babu takamammen magani na cutar HIV/AIDS, amma akwai magunguwan da za su rage kaifin cutar, tare da taƙaita bunƙasarta a jikin wanda ya kamu da ita.
Ga wasu mutanen da suka kamu da cutar HIV sukan fuskanci wasu alamomi da suka hada da zazzafi da rashin kuzari da ciwon gaɓoɓi ko ƙuraje ko tari da kasala da ciwon maƙogoro da sauransu bayan mako biyu zuwa huɗu da kamauwa da cutar.
To amma idan suka fara shan magani ba za su ƙara ganin waɗannan alamomi ba na tsawon shekaru.
Ƙwayar cutar HIV kan yaɗu ta yadda za ta yi yaƙi da garkuwar jiki har sai ta raunana shi.
Idan ba a magance ta ba, ƙwayar HIV kan bunƙasa har ta kai ga samar da cutar AIDS a cikin shekara takwas zuwa 10, lamarin da zai sa kowace cuta ta tunkari jikin mutum sai ta yi nasara, saboda an raunana garkuwar jiki.
Yadda za a magance ta
Ba a warkewa daga cutar HIV/AIDS, to amma akwai magunguna da ke rage kaifin cutar, ta yadda ba za ita bunƙasa har ta kai ga zama AIDS ba.
Ta hanyar shan magani ,masu ɗaukar da HIV da yawa a Amurka ba su kamu da AIDS ba.
2. Cutar hanta nau'in B da C
Cutar hanta nauyin B da C wasu cutaka ne da ke haifar da kumburin hanta. Ana ɗaukar duka waɗannan nau'ikan cuta biyu ta hanyar jini, to amma cutar nau'in B akan ɗauke ta hanyar wasu nau'ikan ruwa da jiki ke fitarwa kamar maniyyi.
Duka cutukan biyu kan haifar da cutuka da ke jimawa da wadanda ba sa jimawa a jiki.
Matsanancin cutukan biyu, kan haifar mummunar matsalolin hanta, kamar kansar hanta da ƙuraje-ƙurajen hanta.
Haka kuma akan dauki cutar ta hanyar jima'i, sannan kuma uwa kan yaɗa cutar zuwa jaririnta a lokacin haihuwa, ko ta hanyar amfani da sirinji guda da mai ɗauke da cutar a lokacin allura.
Yadda za a magance ta
Babu wani cikakken maganin cutar ciwon hanta nau'in B, amma akwai nau'ikan wasu magunguna da kan taimaka wajen daƙile cutar tare da rage lalacewar hantar.
Akwai riga-kafin da ake yi kuma likitoci na son mutane su yi domin kariya daga cutar hanta nauyin B.

Asalin hoton, Getty Images
3. Ƙurajen al'aura
Cutar kurajen al'aura da aka fi sani da Herpes ko (HSV) cuta ce da ke haifar da kuraje a al'aura da bakunan masu ɗauke da cutar.
Cuta da ke saurin yaɗuwa ta hanyar haɗuwa fata.
Akwai nau'ikan cutar herpes har guda biyu
Nau'i na farko shi ne HSV-1 wadda ke yaɗuwa ta tsosar baki, kuma sukan haifar da wasu nau'ikan cutuka a cikin baki.
Haka kuma takan haifar da kuraje a farji. Cutar nau'in HSV-1 ta fi kama manyan mutane.
Nau'i na biyu na cutar HSV-2 na yaduwa ta hanyar jima'i, kuma ita takan haifar da kurajen al'aura.
Yadda za a magance ta
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, (WHO), akwai magungunan da ake amfani da su a farkon samuwarta don rage kaifinta.
Idan aka dauki matakin tun a farkon samuwar cutar, hakan zai sa a samu raguwar kaifin wahalar da ake sha a lokacin alamomin cutar, amma ba warkewa daga gare ta ba.
Magance cutar a lokacin fara ganin almominta zai taimaka wajen taƙaitata musamman cikin kwanaki biyun farko na samuwarta.
Akwai magungunan da ake amafni da su a wannan mataki da suka haɗa da acyclovir da famciclovir da kuma valacyclovir.
Shan ƙaramin adadi na ɗaya daga cikin waɗannan magunguna a kowace rana, kan taimaka wajen rage yawan bayyanar alamominta.
A cewar WHO, ana mutanen da ke fukantar zafi da masu son rage hatsarin yaɗa cutar su riƙa shan magani.
4. Cutar sanyi ta sipilis
Sifilis ƙwayar cuta ce da ke haifar da ƙuraje a al'aura ko baki, kuma takan yadu zuwa sauran sassan jiki idan ba a magance ta ba.
Wannan cuta ce da ake ɗauka ta hanyar jima'i, kuma tana da kariya ana kuma iya maganceta. Idan ba a maganceta ba, takan haifar da mummunar matsala ga lafiya.
Da yawa cikin mutanen da ke ɗauke da cutar ba sa ganin wasu alomomi, wasu ma ba su san suna ɗauke da ita ba.
Cutar Sifilis a lokacin da mace ke da juna biyu kan sa a riƙa haifar jarirai babu rai, ko su mutu bayan ƴan kwanaki da haihuwarsu, ko kuma a haifi jariran da rauni ko tabo a jikinsu.
Amfani da robar kariya yadda ya kamata a lokacin saduwa kan taimaka wajen hanaɗaukar cutar.
Yin gwajin cutar a kai akai zai taiamaka wajen fara amfani da magungunanta idan mutum ya ziyarci asibiti.
Yadda za a magance ta
Ana magance cutar sanyi ta sifilis. Don haka mutanen da ke fargabar suna ɗauke da ita, su tuntuɓi likitoci a sibiti.
Idan a farkon cutar ne ana maganceta da allurar benzathine penicillin (BPG).
BPG shi ne magani na farko da ake kashe cutar a matakin farko, kuma shi kadai ne WHO ta amince a yi wa masu juna biyu da ke ɗauke da sifilis.
A mataki na biyu na yaƙi da cutar, likitoci kan yi amfani da doxycycline da ceftriaxone ko azithromycin waɗanda magungunan kashe ƙwayoyin cuta ne.
Ana kuma amfani da BPG wajen yaƙi da cutar in ma ta kai wasu matakan, amma kuma ana buƙatar a sha da yawa.
Akan sha maganin sau guda a mako, har tsawon mako uku a jere.
Allurar BPG kan taimaka wajen hana yaɗa cutar sifilis daga uwa zuwa jariri.
Akwai buƙatar gaggauta yi wa jariran da aka haifa da cutar - ko waɗanda uwayensu ke ɗauke da cutar - magani, domin kauce wa samun matsalolin lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
5. Ƙaiƙayin matse-matsi
Ƙaiƙayin matse-matsi cuta ce da ake iya ɗauka ta hanyar jima'i da ake samu daga ƙwayar cuta mai suna 'Chlamydia trachomatis'.
Cuta ce da ake iya maganceta ta hanyar magungunan kashe ƙwayoyin cuta, amma idan ba a magance ta ba, takan iya haifar da matsalolin lafiya, musamman ga mata.
Wanna cuta na yaɗuwa ta hanyar ruwan al'aurar mace ko maniyyi.
A wasu lokuta cutar Chlamydia ba ta da alamomi, lamarin da ya sa take da wahalar ganowa da wuri. To amma idan alamomin suka bayyana sun haɗa da fitar da ruwa daga mafitsara ko al'aurar mace, da zafi lokacin fitsari, a wasu lokutan kuma zafi a mara da maraina.
Yadda za a magance ta
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHo ta ce ana warkewa daga cutar ƙaiƙayin matse-matsi.
Ana magance cutar ƙaiƙayin matse-matsi da ba ta yi tsauri ba ta hanyar amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta, da suka haɗa da doxycycline ko azithromycin.
Amma ana sake kamuwa da cutar idan wanda kake jima'i da shi bai warke ba, don haka amfani da roibar kariya a lokacin jima'i kan taimaka wajen daƙile kamuwa da cutar.
Jariran da aka haifa da cutar ƙaiƙayin ido, akan ba su maganin azithromycin.
Ana bai wa mutanen da suka sha maganin shawarar dakatar da jima'i har na tsawon kwana bakwai bayan shan maganin, ko kuma su yi amfani da ribar kariya.
Haka kuma ana bai wa masu cutar shawarar su riƙa sanar da wanda suka yi jima'i da shi domin ya yi gwaji kuma ya sha magani.
An samu wannan bayani ne daga majiyoyin Hukumar Lafiya ta Duniya.











