Abubuwan da ba ku sani ba kan hare-haren Benue da suka kashe gomman mutane

Ƴanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

A ƙarshen mako ne aka samu wasu jerin hare-haren ƴanbindiga da suka hallaka mutane da dama a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Hukumomi a Najeriya sun ce hare-haren sun halaka fiye da mutum 100, yayin da ake ci gaba da gano gawarwaki, ana sa ran adadin zai zarta haka.

Jihar Benue na daga cikin jihohin Najeriya da suka yi ƙaurin suna wajen rikicin ƙabilanci da na manoma da makiyaya.

Hare-haren baya-bayan nan biyu da aka kai ranar 13 da 14 ga watan Yuni sun tayar da hankalin ƴan ƙasar, lamarin da ya sa shugaban ƙasar Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta kawo ƙarshen rikicin.

Su wa wane suka ƙaddamar da hare-haren?

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar NEMA ta ce wasu mutane ne da ba a san ko su wane ne ba ɗauke da makamai suka ƙaddamar da hare-haren.

To amma wasu kafofin yaɗa labaran Najeriya da mazauna yankunan da lamarin ya faru sun zargi makiyaya da kai hare-haren.

Cikin wata hira da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Guma, Hon. Orwough Maurice - inda lamarin ya rafu - ya shaida wa BBC Hausa cewa suna zargin Fulani makiyaya da ƙaddamar da hare-hare.

''Saboda mun samu labarin cewa harin da aka kai garin Daudu ana kora shanu aka kai shi'', in ji shi.

Sai dai Fulanin sun musanta hannu a hare-haren, kamar yadda Sakataren ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Mi Yetti Allah a jihar, Ibrahim Galama ya shaida wa BBC Hausa.

''Waɗanda suka kai wannan hari ƴan'tadda ne, babu wani takalmi ko riga ko wani mutum da aka kama, da zai tabbatar da cewa Fulani makiyaya ne'', kamar yadda ya bayyana.

Mutum nawa ne suka mutu?

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar NEMA ta ce kawo yanzu mutanen da suka mutu sadaniyyar hare-haren biyu sun haura 100, kodayake ta ce adadin zai iya ƙaruwa yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Guma ya shaida wa BBC cewa a harin da aka kai garin Yelwatad an kashe mutanen da bai san adadinsu ba.

''Amma a harin da aka kai garin Daudu an kashe sojoji biyu da jami'in sibil difence guda da kuma fararen hula'', kamar yadda ya shaida wa BBC.

Mutanen da suka rasa muhallansu

Ma'aikatan NEMA

Asalin hoton, NEMA

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar, NEMA ta ce kusan iyalai 1,069 - da suka ƙunshi mutum 6,527 ne - suka rasa muhallansu sanadiyyar hare-haren.

Adadin ya ƙunshi mata 1,768 da maza 759 da ƙananan yara 657, matasa 1,870 sai mata masu shayarwa 252 da masu juna biyu 82, da tsofaffi 91.

Daga cikin wannan adadi hukumar ta ce fiye da mutum 3,000 ne ke cikin tsananin buƙatar tallafin muhimman abubuwan buƙatar rayuwa, kamar ruwan sha da magunguna.

Hukumar ta ce tuni jami'anta suka fara tattara kayan agaji domin tallafa wa mutanen da suka gidajen nasu.

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya ta ce har yanzu ba a ga mutane masu yawa ba bayarn hare-haren da ƙungiyar ta ce sun jikka gomman mutane.

''Iyalai da dama an kullesu a gidanjensu tare da cinna musu wuta a gidajensu, mutane da dama sun ƙone ta yadda ba za a iya gae su ba'', a cewar ƙungiyar.

Amnesty ta kuma ce harin ka iya kawo tarnaƙi ga wadatuwar abinci a jihar, saboda da da dama cikin waɗanda harin ya shafa manoma ne.

Tinubu ya bayar da umarnin kawo ƙarshen rikicin

Tinubu

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

Tuni shugaban kasar Bola Tinubu ya bayar da umarni ga jami'an tsaron ƙasar su aiwatar da umarnin farko da ya bayar da samar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Lahadi, Shugaba Tinubu ya umarci shugabannin hukumar tattara bayanan sirri na ƙasar da ƴansanda da sojoji su gaggauta zuwa jihar domin tabbatar da zaman lafiya a cikinta.

Haka kuma shugaban ƙasar ya buƙaci gwamnan jihar, Hyacinth Alia, ya gaggauta shirya gana da ɓangarororin da ke rikici da juna jihar da nufin yin sulhu domin kawo ƙarshen abin da ya kira zubar da jini da ake yi a jihar, da kuma tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyya da kuma al'ummar jihar.

Fafaroma Leo ya yi Allah wadai da hare-haren

Fafaroma Leo XIV

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fafaroma Leo ya bayyana kashe-kashen da ''kisan kiyashi''

Shugaban Dariƙar Katolika, Fafaroma Leo XIV ya yi allah wadai da hare-haren na Benue.

Yayin da yake gabatar da jawabi kafin fara taron addu'i ranar Lahadi a fadar Vatican, fafaroman ya bayyana kashe-kashen da na ''kisan kiyashi masu tayar da hanakli''.

Fafaroman ya kuma nuna damuwa kan halin da rikicin ke jafa al'ummar jihar, musamman waɗanda waɗanda ba su ji ba su gani ba.

Jihar Benue

Jihar Benue na daga cikin jihohin Najeriya da suka jima suna farma da rikice-rikice masu alaƙa da ƙablinaci da na manoma da makiyaya.

Rikice-rikicen da a lokuta da dama ke haifar da asarar rayuwa da dukiyoyi masu dimbin yawa.

A lokuta da dama gwamnati kan yi iƙirarin ɗaukar matakai domin magance matsalar, to amma da alama har yanzu tsugune ba ta ƙara ba.

A cikin watan da ya gabata ma an samu makamancin waɗannan hare-hare a jihar da makwabciyarta jihar Plateau, inda hukumomi suka tabbatar mutuwar mutane da dama.

A ranar 14 ga watan Yuni ne ƙungiyar ƙare haƙƙin bil'adama ta Amnesty international a Najeriya ta yi kira daga hukumomin ƙasar da tare da hukunta mutanen da ke hannu a rikice-rikicen jihar da ke laƙume rayuka da dukiyoyi masu yawa.