Rayuwar mutanen Benue a cikin hotuna

Kalli hotunan rayuwar mutanen Benue daga cikin tsarabar Haruna Tangaza da Yusuf Yakasai da Abdussalam Usman Abdulkadir, tawagar BBC da ta ziyarci Makurdi.

Rayuwar mutanen Benue
Bayanan hoto, Benue Jiha ce da ke alfahari da noma musamman noman Doya da Rogo da kayan marmari.
Rayuwar mutanen Benue
Bayanan hoto, Ana noman wake da waken Soya da Shinkafa 'yar Benue da Dawa da Ridi da kuma Gyada.
Rayuwar mutanen Benue a cikin hotuna
Bayanan hoto, Tsohuwar gadar kogin Benue a Makurdi babban birnin jihar.
Rayuwar mutanen Benue
Bayanan hoto, Baya ga manyan kabilun Benue kamar Tiv da Idoma da Igede akwai kuma Fulani da Hausawa a Makurdi.
Rayuwar mutanen Benue a cikin hotuna
Bayanan hoto, Ana yi wa dabbobi sheda don kada su bata, yayin da Benue ta haramta yawo da dabbobi don kiwo domin dakile rikicin makiyaya da manoma.
Rayuwar mutanen Benue a cikin hotuna
Bayanan hoto, Wasu makiyaya sun koma suna kiwon tsare, a yayin da ake ganin wannan ce hanyar magance rikicinsu da manoma da satar shanu a Benue.
Rayuwar mutanen Benue a cikin hotuna
Bayanan hoto, Sunan Jihar Benue ya samo asali ne daga Kogin Benue bayan raba jihar da Filato a 1976. Masunta a Benue na amfani da kwale-kwale domin kamun kifi yayin da wasu ke aikin kwadagon dibar yashi.
Rayuwar mutanen Benue a cikin hotuna
Bayanan hoto, Mata kamar Maza, na aikin leburanci da noma a Benue
Rayuwar mutanen Benue a cikin hotuna
Bayanan hoto, "Rediyo abokin hira," duk da yana kan sana'arsa ta kamun kifi a Kogin Benue amma wannan Dattijon labaran BBC Hausa ba su wuce shi
Rayuwar mutanen Benue a cikin hotuna
Bayanan hoto, Tawagar BBC Hausa ta ratsa Kogin Benue a kwale-kwale a yayin da suke kokarin hada rahotanni a Makurdi.