Dambarwa ta barke tsakanin majalisar tarayya da gwamnonin Zamfara da Benue

Asalin hoton, PSN
Gwamnonin jihohin Zamfara da Benue, Dauda Lawal da Hyacinth Alia, sun ce ba za su amsa gayyatar da Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafe na Majalisar Wakilai ta Tarayya ya yi musu ba, inda suka bayyana shakku kan halaccin gayyatar.
An gayyaci gwamnonin da majalisun dokokin jihohinsu ne domin su bayyana a gaban kwamitin bisa zargin saba kundin tsarin mulki da kuma gazawa wajen gudanar da mulki.
Duka jihohin biyu na fama da matsalar tsaro da kuma rikici tsakanin wasu 'yan majalisar dokokin jiha da kuma gwamna.
Gayyatar na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban kwamitin yada labarai da korafe-korafe na majalisar wakilan, Chooks Oko, ya fitar ranar Juma'a uku ga watan Mayu.
An tsara zaman saurarensu ne a ranar takwas ga watan Mayu, don neman bayani daga gwamnonin da kuma majalisun dokokin jihohinsu a kan batutuwan da suka shafi dakatar da wasu 'yanmajalisa da tabarbarewar tsaro.
Haka kuma gayyatar ta bukaci sanin ko suna da ja kan kudurin majalisar wakilan na karbe ikon gudanar da ayyukan majalisun jihohin biyu, kamar yadda sanarwar ta ce sashe na 11(4) na kundin tsarin mulkin Najeriyar na 1999 ya bayar da dama, idan har hakan ya zama dole.
A jihar Benue, akwai takaddamar dakatar da wasu 'yanmajalisar jihar 13, wadanda ba sa jituwa da gwamnan jihar.
An dakatar da 'yanmajalisar ne saboda sun nuna kin amincewa da dakatar da babban mai shari'ar jihar Maurice Ikpambese, da gwamnan ya yi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A jihar Zamfara kuwa abin ya fi kamari inda aka samu majalisa biyu, inda wasu 'yanmajalisa tara suke ikirarin damar ci gaba da aikinsu duk da cewa an dakatar da su.
'Yanmajalisar tara karkashin jagorancin wani shugaban na bangaren da ba ya jituwa da gwamnan, sun bukaci gwamnan da ya gabatar da kasafin kudin jihar na wannan shekara ta 2025, inda suka kafe cewa suna da hurumin ci gaba da aikinsu.
To amma mataimaki na musamman ga gwamnan jihar ta Zamfara Mustapha Jafaru Kaura, ya sheda wa BBC cewa babu wata takardar gayyata da gwamnan jihar ko kuma majalisar dokokin suka samu daga 'yan majalisar wakilan na tarayya game da wannan gayyata, illa dai kawai sun ga wannan magana ne a kafafen sada zumunta da muhawara
Haka kuma ya kara da cewa bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya majalisar tarayya ba ta da hurumin gayyatar wani gwamna ya je gabanta a kan duk wata matsala.
''Tsarin daunin iko tsakanin matakan gwamnatoci a tsarin mulkin Najeriya ya wajabta wa duk wani gwamnan jiha cewa majalisar dokokin jiharsa ce zai gabatar wa duk wani kudurin kasafin kudi ko wani abu, kuma su ke bayar da dama cewa sun yarda a yi kaza ko ba su yarda ba,'' in ji shi.
Ya kara da cewa,'' wannan shi ake yi amma ba wai majalisar tarayya ta ce tana gayyatar gwamnan jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal Dare ko kuma gwamnan jihar Benue ba a kan abin da ya shafi majalisar dokokin jiharsu ba.''
''Wannan labari ne maras tushe balle makama, labari ne na kanzon kurege,'' in ji Jafarun.
''Idan majalisar dokoki ta kasa ba ta san abin da ya kamata ba, shi ma Gwamna Dakta Dauda bai san abin da ya kamata ba? Ai abin da yake cikin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa shi ake yi,'' a cewarsa.
Wadannan jihohi biyu - Zamfara da Benue sun kuma kasance cikin matsaloli na rashin tsaro da ya ta'azzara.
Daga cikin matsalolin tsaron da suka fi addabar jihar Benue ita ce ta rikicin makiyaya da manoma, inda ake fama da kashe-kashe da barnata dukiya.
Da yake magana kan gayyatar wani jami'in gwamnatin jihar ta Benue wanda ya ki yarda a bayyana sunansa saboda ba a ba shi izinin magana a kan gayyatar ba ya sheda wa jaridar Punch cewa , tuni gwamnatin jihar na nazari a kai.
Ya kuma ce gwamnatin na dubawa ta ga ko majalisar wakilan ta tarayya tana da hurumin gayyatar gwamnan da kuma 'yanmajalisar jihar.
Bayanai dai sun nuna cewa majalisar dokokin ta tarayya na nazari ta ga ko lamarin ya kai a shiga tsakani ta karbi ikon gudanar da aikin majalisun dokokin jihohin biyu na Zamfara da kuma Benue.











