'Ƴanbindiga sun bamu wa'adin kashe mahaifinmu'

INSECURITY IN NORTHEN NIGERIA

Asalin hoton, OTHERS

Lokacin karatu: Minti 2

Wasu ƴan bindiga sun ce sun gaji da rike wani dattijo da suka sace a kan hanyarsa ta zuwa wani aiki na musamman da aka ce majalisar dokokin jihar Zamfara ta tura shi, tun cikin watan Oktoban, 2024.

A ranar Alhamis ne kuma wa'adin da ƴan bindigan suka ɗiba don a kai masu karin kudin fansar dattijon zai cika.

Hakan dai ya biyo bayan biyan kudi naira miliyan 16 da iyalansa suka gagganɗa ne, amma kuma ƴan bindigar suka nemi a kai masu karin wasu kudin naira miliyan 15, da sababbin babura guda biyar.

Al'amarin da ya jefa iyalai da ƴan uwan dattijon cikin mawuyacin hali.

Yanzu haka dai hankali na can tashe dangane da halin da Alhaji Bashir Abara Gummi, wani ma'aikacin gwamnatin tarayya da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara ke ciki.

Wanda 'yan bindiga suka suka sace, kuma suke garkuwa da shi kimanin watanni hudu kenan.

Mashkur Bashir, shine babban ɗan wannan dattijo ya shaidawa BBC cewa, suna cikin tashin hankali, "sakamakon bidiyon da su ƴanbindigar suka saki yana bayani a ciki cewa sun ce sun gaji da riƙe shi idan har ba mu kawo abin da suke buƙata ba zuwa Alhamis za su kashe shi."

Mahaifinmu ya tafi aikin da majalisar dokokin jihar Zamfara ta tura shi ne Abuja, sai ya hadu da wannan iftila'i a wajen Tsafe aka buɗe masu wuta, kowa ya gudu sai shine aka tafi da shi tsawon wata hudu kenan," cewar Mashkur wanda aka yi garkuwa da mahaifinsa a Zamfara.

Mashkur ya ce sun nemi taimakon majalisa da gwamnatin jihar amman babu wani abu da suka yi, "Muna kira ga gwamnatin jihar Zamfara da majalisar jihar da su suka sanya shi aiki, da masu hannu da shuni da su taimaka su fito mana da shi."

BBC ta tuntubi akawun majalisar dokokin jihar ta Zamfara, Mahmud Aliyu ta waya kan wannan batu, inda ya ce ba shi da izinin yin magana da mu a hukumance.

Sai dai duk da haka, ya ce mu kira shi bayan awa biyu da rabi, amma kuma ko da lokacin ya yi, mun yi ta kiran layin wayar tasa, amma ba ta shiga.

Jihar Zamfara dai na fama da farmakin 'yan fashin daji, waɗanda ke satar jama'a domin neman kuɗin fansa, wani lokacin su kona gidaje da dukiya baya ga sace dabbobin al'uma.

Sai dai mahukuntar jihar sun kafa ƙungiyar askarawan Zamfara da ke yaƙar ayyukan 'yan bindigar, amma har yanzu hare-haren na ci gaba da ƙaruwa.