Askarawan Zamfara ba za su wuce gona da iri ba - Gwamna Dauda

Gwamna Dauda Lawal Dare

Asalin hoton, @Daudalawal001

Gwamnan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya Dr Dauda Lawal Dare ya kawar da duk wata fargaba game da rundunar 'yan sa-kai da ya ƙaddamar a jiharsa mai fama da matsalar ƴanbindiga.

A ranar Laraba ne gwamnatin Zamfara ta ƙaddamar da wata runduna rundunar ta mutum fiye da 2,600, mai suna `Askarawan Zamfara' da za ta yi yaƙi da ƴanbindiga masu fashin daji da satar mutane.

Gwamna Dauda ya ce ya ja kunnen dakarun nasa, a yayin da masana da wani ɓangare na al'umma ke nuna fargaba game da ƴan sa-kai kada su zama alaƙaƙai yayin yaƙi da ƴanbindiga da kuma bayan ɗaƙile su.

Gwamnan ya shaida wa BBC cewa an bi ƙa'idojin doka kafin ƙaddamar da rundunar.

"Kuma mun jaddada ma su ƙa'idojin da za su bi, ba wai za su je su yi zalinci ko kashe mutane ba, kuma na yi imanin za su bi umarni,"

"Mun tabbatar da cewa mun tantance waɗannan matasa da aka yaye ta hanyar amfani da jami'an tsaro da kuma sarakuna, saboda haka dukkan wadanda muka ɗauka mun san komai game da su," in ji Gwamna Dauda.

Gwamnan ya ce sun yi tsarin yadda za su yi aiki tare da jami'an tsaro domin ƙara ma su ƙwarin guiwa.

"Za su yi aiki tare da ƴansanda da sojoji da jami'an Civil Defence ba wai za su tafi su yi abin da suka ga dama su ƙadai ba," in ji shi.

Ya ƙara da cewa: "Dukkaninsu sun yi rantsuwa da Al-Qur'ani kan za su yi aiki tsakani da Allah.

Ya ce tun lokacin da aka fara horar da su ake biyansu albashi tare da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da biyan duk wani haƙƙi nasu duk wani abu na kyautatawa, saboda haka "ba mu fargabar za su zama ɓatagari."

Ya ce kuma har da tsarin yin ritaya aka tanatar wa Askarawan kamar yadda tsarin kowane aiki gwamnati yake.

Jihar Zamfara ta daɗe tana fama da matsalar ƴanbindiga ma su kashewa da fashin daji da tayar da gari da kuma satar mutane.

Kuma gwamnatocin baya sun ɗauki irin wannan mataki na samar da ƴan sa-kai da nufin magance matsalar amma kuma suka ƙara rurawa da yin ƙamarin matsalar, kasancewar wani ɓangare na ƙabilun jihar na zarginsu da wuce gona da iri.

Masana na ganin akwai bukatar mahukunta su yi tsari ta yadda ƴan sa-kan ba za su wuce iyakokinsu ba, tare da inganta mu su rayuwa gudun kada su zama alaƙaƙai ga al`umma.

Haka kuma a ɗauki matakai na tabbatar da ba su zama annoba ba bayan sun kammala aikin dakile ƴan bindiga a jihohin nasu.