'Matakin daukar ‘yan sa- kai ba tare da fulani ba zai ƙara rura wutar rikicin makiyaya da manoma ne kawai'

Jihar Zamfara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan fashin daji

Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, na cikin jihohin da suka dauki ‘yan sa-kai domin shawo matsalar rashin tsaro da ke addabar jihohin.

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da matakin daukar yan sa-kai sama da 4,000 domin kafa rundunar JTF da za ta taimaka wa jami’an tsaro kawo karshen matsalar .

To sai dai wasu kungiyoyin makiyaya sun yi gargadin cewa matakin gwamnatocci na daukar yan sa-kai ba tare da gwamawa da fulani ba, kara ta’azzaara rikici zai yi.

Shugaban matasa na Kungiyar makiyaya ta Gan Allah a Najeriya, Buba Ɓarti wanda aka fi sani da Buba Minista ya shaida wa BBC cewa matakin zai ƙara rura wutar rikicin makiyaya da manoma ne kawai .

“ Gwamnatoccin baya sun dauki ‘yan sa-kai ko ‘yan banga masu yawa kuma lokacin da aka dauke su matsalar rashin tsaro ta kara ta’azzara ne”. in ji shi.

Shugaban matasan ya yi ikirarin cewa a wancan lokaci hausawa zalla gwamnatin ta dauka a matsayin ‘yan sa-kai kuma a cewarsa wannan abin ya kara tunzura su kuma ya kara wa ‘yan sa-kai karfi suna tunkarar matasan Fulani.

Ya kuma ce idan aka gwama da hausawa da fulani wajan daukar ‘yan sa-kai kwaliya za ta biya kudin sabulu:

“ Idan cikin fulanin akwai wanda ya yi laifi ko kuma akwai wanda ake nema, toh su wadanan yan bangar fulanin su ne za su zo da shi”.

“ Su kuma hausawan idan ana neman mai laifi, za su iya zuwa da shi amma a ce bangaren Fulani an dauko hausawa sun je, su zo da bangaren Fulani wannan tamkar fada ne”, in ji shi.

Matakin amfani da ‘yan sa-kai wani tsari ne da za a iya cewa ya yi tasiri wajen dakile hare -haren mayakan Boko haram a yankin arewa maso gabashi da kuma yan fashin daji a wasu sasan jihohin da ke arewa maso yamma.