Gudunmawar masu kuɗi a yaƙi da 'yan fashin daji a Katsina

Za a iya cewa tura ta kai bango a jihar Katsina, arewa maso yammacin Najeriya game da matsalar tsaro da rikicin 'yan fashin daji ya haddasa.
Domin kuwa tuni al'ummomi suke ƙoƙarin nema wa kansu mafita game da wannan ƙalubale, wani abu da ya yi daidai da umarnin tsohuwar gwamnatin jihar da ta nemi "mutane su ɗauki makamai su kare kansu".
Yankin Bakori, tamkar sauran yankunan jihar ne da wani lokaci darensu ke zama daidai da rana, ma'ana hare-haren da ake kai wa cikin dare ke sa mutane su zauna ido biyu ba sa iya rintsawa.
Sai dai wani bawan Allah da ake kira Muhammad Bello Bakori da ke da hali da kuma zuciyar taimakawa ya yunƙura don tallafa wa 'yan bijilanti da makamai domin su kare yankinsu.
Jajirtaccen ɗan kishin al'ummar, yana ƙoƙarin haɗa kan mutanen yankin musamman ma dai matasa masu jini a jika, da ba su horo da ƙarfafa musu gwiwa kan dabarun kare kai, a matsayin wata hanya da za su ɗora a kan ƙoƙarin hukumomi.
Cikin hirarsa da BBC ya bayyana yadda suke zaɓo matasa daga cikin al'umma da irin yadda ake tantance su da ba su horo.
"Wannan yaƙi ne na kare kai da iyaye da dukiyoyinmu, ba yaƙi ne na son zuciya ba.
"Bakori, nan iyayena suke. kabarin da aka binne su nan yake, dole mu tashi mu kare martabar waɗannan abubuwa masu daraja," in Bello Bakori.
Bello ya ce karkararsU ce ta kama da wuta shi ya sa yake sadaukar da kai domin ceto ta.
'Yadda muke ɗaukar matasa 'yan sa kai'
Duk matashin da yake son ya yi aikin sa kai wato bijilanti, sai an samu bayanai daga mai garin da yake, ma'ana sai sun biyo ta hannu masu garinsu domin tabbatar da ingancinsu, in ji Malam Bello.
"Jami'an tsaro da masu garuruwansu ne ke tantance su.
"Kullum ina yi musu nasiha kada su yi amfani da wannan dama su yi abin da ba daidai ba, mu yi komai don Allah.
Yaƙi muke da zalunci kada a samu azzalumi a cikin mu, idan akwai azzalumi Allah Ya bayyana shi Ya tona masa asiri," in ji Bello Bakori.
Bita da maganganun samar da ƙwarin gwiwa na daga cikin abubuwan da suke yi wa matasan a kowanne lokaci.
A cewar Muhammadu Bello duk wanda ya samu kan sa cikin irin wannan aikin yana buƙatar a rika sabunta masa tunani.
'Kayan aikin da muke da su na zamani ne'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da cewa ba wani taimako da suke samu a gwamnatance ko da kuwa a matakin ƙaramar hukuma amma aikin waɗannan 'yan sa kai yana tafiya yadda ya kamata.
Bello Bakori ya ce shi ya sai wa waɗannan matasa wayar salula mai tsarin da ake kira oba-oba 150 irin ta jami'an tsaro domin sauƙin sadarwa.
Ya samar musu da bindigu masu filogi kamar 70, da kuma filogi 1000 haka kuma ya samar musu da harsashi irin wanda mafarauta suke amfani da su.
"Kwalliya na biyan kuɗin sabulu, domin kuwa ko a kwanakin baya da aka sace wasu shanu kimanin 60 da suka shiga dajin sai da suka ceto su ciki har da mutumin da aka yi garkuwa da shi," in ji shi.
Malam Bello ya ce gudun wani abu ya faru da ba a san wa ya aikata ba, ko wacce bindiga akwai lambarta kazalika da yawan harsashin da aka bai wa kowa.
Muna amfani da na'urar CCTV da ke nuna ɗaukar dare, ba kawai da rana take aiki ba har dare tana nuna duk wani abu da ke kewayen inda muka sanya ta.
Yankin arewa maso yamma dai na fama da matsalolin tsaro duk da dai cewa hukumomin yankin na cewa suna iya bakin ƙoƙarinsu.
Al'umar yankin ba su yanke ƙauna ba, ganin cewa an samu sauyin gwamnati a duka jihohin da ke yankin, wanda kyakkyawan fatan samun sauyi ya mamaye burinkansu.











