Luguden wuta ne ya sa 'yan fashin daji neman afuwa

Wasu majiyoyi sun ce luguden wuta da sojojin saman Najeriya ke ta yi kan wuraren da 'yan bandiga suke da kuma maboyarsu a shiyyar arewa maso yammacin kasar, ya sa wasu shugabannin 'yan bindiga a yankin sun nemi a zauna da su, don a tattauna, a yi yarjejeniya, kuma gwamnati ta yi masu afuwa.
Majiyoyin sun shaida wa kafar watsa labaran PRNigeria, cewa har shugabannin 'yan bindigan a jihohin Katsina da Zamfara sun aika wakilai wajen wani taro da aka yi a kauyen Gusami da ke yankin karamar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara.
To sai dai wasu masana sun nuna shaku a kan alamarin.
Barista Audu Bulama Bukarti mai bincike a cibiyar Tony Blair da ke birnin Landan, ya shaidawa BBC cewa akwai bukatar yin taka-tsantsan kan wannan batu.
A cewarsa ‘yan bindigar suka yi haka ne sakamakon ruwan bama bamai ta sama da sojojin Najeriya suke kai mu su a maboyarsu kuma ko a baya ma sun yi haka amma bai yi tasiri ba.
”An yi kokarin yin sulhu da su,har ma wasunsu sun zo an yi bukukuwa, an ce sun mika bindigogi, sai kuma mu ga cewa Angulu ta koma gidanta na tsamiya”, in ji shi.
A baya an samu wasu ‘yan Najeriya da suka hada da tsohon gwamnan jihar Zamfara , sanata Ahmad Sani Yarima, da suka yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sulhu da ‘yan bindigar da suka adabbi jihar da wasu jihohi arewa maso yammacin kasar.
Sai dai masana irinsu Barista Bulama Bukarti sun ce wannan ba shi ne mafita ba. Ya kuma danganta neman afuwar da ‘yan bindigar suka yi kan luguden wutar da ake yi mu sa ta sama. Sai dai ya ce maganar da suka yi akan a yi sulhu da su ba ta taso ba:
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
“ Ta'adancin da suke yi a yankin arewa maso yammacin Najeriya ba maganar sulhu bane, idan sun ji wuta,toh su fito su tuba, su ajiye mukamansu tare da mika wuya ga gwamnati”, in ji shi.
Masanin ya kara da cewa gwamnatin za ta iya mu su afuwa idan suka nuna cewa sun yi nadama kan abubuwan da suka aikata, kuma idan al'umomin da suka dai-daita sun amince a yafe musu.
Sai dai masanin ya nuna shakku akan anniyar ‘ yan bindigar.
“ A taron da suka yi cewa suka yi za su mika wani bangare ne na makamai, za su rike sauran ne don su yaki sauran 'yan bindigar da ke daji”,
“ Sun ce sai sun gama da sauran 'yan bindiga da ba su bada makamai bane sannan za su kawo sauran makaman”, in ji shi.
A cewar masanin wannan ba abu bane da hankali zai dauka, saboda idan so suke su tuba toh makamansu gabadaya ya kamata su kawo, daga nan sai gwamnati ta daukesu ta kai su wurin da ba za’a kai mu su hari ba.
A baya gwamnatin Nijeriya karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua ta yi wa mayaka masu tayar da kayar baya a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur afuwa bayan sun mika wuya tare da ajiye makamansu.











