Su wane ne sabbin hafsoshin tsaron da Tinubu ya naɗa?

..

Asalin hoton, DEFENCE HQ

Lokacin karatu: Minti 4

Shugaba Bola Tinubu ya tuɓe hafsan hafsoshin Najeriya, Janaral Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron ƙasar, a wani sauyi a tsarin jagorancin sojjin ƙasar domin inganta da ƙarfafa sha'anin tsaro a Najeriya.

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar mai sa hannun ɗaya daga cikin masu taimaka wa shugaban a harkar watsa labarai, Sunday Dare, Tinubu ya yi musu fatan alkairi tare da bayyana sunayen sabbin hafsoshin da za su maye gurbin waɗanda aka sauke ɗin.

Sunayen sabbin hafsoshin tsaro:

  • Janar Olufemi Oluyede - Hafsan hafsoshi.
  • Manjo Janar W Sha'aibu - Hafsan sojojin ƙasa.
  • Air Vice Marshall S.K Aneke - Hafsan sojin sama.
  • Rear Admiral I. Abbas - Hafsan sojin ruwa.
  • Manjo Janar E.A.P Undiendeye - Shugaba sashen tattara bayan sirri na soji.

Janar Olufemi Olatubosun Oluyede

Janar Olufemi Olatubosun Oluyede

Asalin hoton, Defence Headquaters

Janar Olufemi Olatubosun Oluyede - Shi ne sabon hafsan hafsoshin Najeriya wanda Tinubu ya naɗa domin maye gurbin Manjo Janar Christopher Musa.

Kafin naɗin nasa, Janar Olufemi mai shekaru 57 shi ne wanda ya maye gurbin Manjo T. A Lagbaja, tsohon hafsan sojin ƙasa wanda ya rasu sakamakon doguwar jinya a ranar 4 ga Nuwamban 2024.

An haifi Oluyede a garin Ikene na jihar Ekiti kuma ya shiga kwalejin aikin soji ta NDA da ke Kaduna a 1987. Oluyede na ɗaya daga cikin sojojin da aka yaye daga aji na 39.

Manjo Janar Waidi Sha'aibu:

Manjo Janar Waidi Sha'aibu

Asalin hoton, DEFENCE HQ

Manjo Janar Waidi Sha'aibu: Shi ne sabon babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya wanda ya maye gurbin tsohon hafsan sojin kasa, Manjo Janar Gold Chibuisi.

Manjo Janar Waidi wanda ɗan asalin jihar Kogi ne. Ya kasance tsohon kwamanda na operation hadin kai kuma tsohon tiyata kwamanda ne a Arewa maso Gabas.

Manjo Janar Waidi na ɗaya daga cikin sojojin da aka yaye daga aji na 41.

Air Vice Marshall S.K Aneke:

Air Vice Marshall S.K Aneke

Asalin hoton, DEFENCE HQ

Air Vice Marshall S.K Aneke: Shi ne sabon babban hafsan sojin sama da Tinubu ya naɗa a ranar Juma'ar nan domin maye gurbin tsohon hafsan sojin sama, AVM H.B Abubakar.

Enenke ɗan jihar Enugu ne da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Enenke ya riƙe matsayin ,ataimakin kwamandan kwalejin horas hafsoshin tsaro ta NDA da ke Kaduna.

Yana ɗaya daga cikin sojojin da aka yaye daga ajin 41 na kwalejin horas hafsoshin tsaro ta NDA da ke Kaduna.

Rear Admiral I. Abbas:

Rear Admiral I. Abbas

Asalin hoton, Defence HQ

Rear Admiral I. Abbas: Shi ne sabon hafsan sojin ruwan Najeriya. Idi Abbas ɗan jihar Kano ne wanda yake da gogewa a fagen daga musamman abin da ya shafi magance matsalolin satar mai da harkokin tsaro da suka jiɓanci ruwa a yankin Neja Delta..

Hafsoshin da Tinubu ya naɗa a 2023

..

Asalin hoton, Defence Headquaters

A watan Yunin 2023 ne shugaba Tinubu ya rushe hafsoshin tsaro da ya gada daga gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari inda kuma ya naɗa sabbin mutanen da suka maye gurbin tuɓaɓɓin.

Jerin sunayen hafsoshin tsaron da aka naɗa a 2023:

  • Mallam Nuhu Ribadu – Babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.
  • Manjo Janar Christopher Musa – Hafsan hafsoshi.
  • Manjo T. A Lagbaja – Hafsan sojin ƙasa.
  • Rear Admirral E. A Ogalla – Hafsan sojin ruwa.
  • AVM H.B Abubakar – Hafsan sojin sama.
  • DIG Kayode Egbetokun – Sifeto Janar na ƴansanda
  • Manjo Janar EPA Undiandeye – Shugaban sashen tattara bayanan sirri na soji.

Bisa jadawalin tsaffin hafsoshin, za a fahimci cewa tsohon hafsan sojojin sama, Manjo T.A Lagbaja shi ne wanda ya rasu a ranar 4 ga wtaan Nuwamban 2024, inda kuma Janar Olufemi Oluyede ya maye gurbinsa.

A yanzu haka Janar Olufemi Oluyede ya samu ƙarin girma inda ya maye gurbin Manjo Janar Christopher Musa a matsayin Hafsan hafsoshin Najeriya.

Me ya sa Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Fadar shugaban ta Najeriya ta ce ta gudanar da sauye-sauyen ne da manufar inganta da sake ƙarfafa tsarin tsaro a ƙasar.

Sai dai da dama ƴan Najeriya na ganin sauyin ba zai rasa nasaba da raɗe-raɗin yunƙurin juyin mulki da kafafen watsa labaran Najeriya suka rinƙa rawaitowa ba, inda suka alaƙanta dakatar da faretin ranar ƴancin Najeriya da kuma binciken wasu sojoji guda 16 bisa zargin kitsa juyin mulkin.

Ko da a makon da ya gabata sai da Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta fito ta ƙaryata batun juyin mulkin inda ta ce ba gaskiya ba ne.

"An dakatar da faretin Ranar 'Yanci ne saboda a bai wa shugaban ƙasa damar halartar wani taro a wajen Najeriya, da kuma mayar da hankali wajen yaƙi da ta'addanci da 'yanfashin daji," in ji wata sanarwar hedikwatar tsaron Najeriya.

To sai dai kuma dangane da binciken da ake yi wa sojojin 16, hedikwatar tsaron ta ce abu ne na yau da kullum da ta saba yi lokaci zuwa lokacin.

"Binciken da ake yi da ya shafi manyan sojoji 16 wani abu ne da aka saba yi lokaci zuwa lokaci a cikin gida domin tabbatar da ɗa'a da ƙwarewar aiki a tsakanin sojojin," in ji sanarwar.