Trump ya nanata aniyarsa ta iya ƙaddamar da hari a Najeriya

Shugaban Amurka Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 7

Donald Trump ya jaddada cewa Amurka za ta iya tura dakaru Najeriya ko kuma kaddamar da hare-hare domin hana abin ya kira kisan Kiristoci da ake yi.

Ya shaida wa manema labarai cewa ba zai bari a ci gaba da kisan ba.

"Ana kashe kiristoci da dama a Najeriya kuma adadi da yawa, ba zan bari a ci gaba ba." in ji Trump.

Fadar gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi maraba da samun hadin kan Amurka wajen yaƙi da mayaka masu tsattsaran ra'ayin addini tare da musanta cewa mayakan sun fi kashe kiristoci.

A watan da ya gabata Amurka ta saka Najeriya cikin jerin kasashen da take da damuwa da su kan take ƴancin addini.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar, Mista Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkaɓe abin da ya kira ƴanta'adda masu kishin Islama da ke aikata ta'asa.

Ya kuma yi barazanar dakatar da duk wani taimakon Amurka ga Najeriya.

Tuni Najeriya ta yi watsi da ikirarin cewa ana kashe kiristoci ba gaira ba dalili a yankin arewacin inda galibi musulmi suka fi yawa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A bayanin da Mista Trump ya wallafa a kafar sadar zumuntarsa ta Truth a ranar Asabar ya ce ya ba ma'aikatar tsaron Amurka umarnin ta fara shirin ɗaukar mataki kan Najeriya - "Idan har gwamnatin Najeriya ta bari ana ci gaba da kashe Kirista," in ji shi.

Shugaban wanda ke ɗa'awar samun lambar yabo ta zaman lafiya a duniya ya kuma yi mummunan kalamai ga Najeriya inda ya ce "Amurka za ta shiga cikin ƙasar da a yanzu ta wulakanta."

Tun a ranar Juma'a Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa "ana kashe dubban kiristoci a Najeriya kuma masu tsattsauran ra'ayin Islama ne ke da alhakin kisan," ba tare da ya bayar da wata hujja ba.

Wasu yansiyasar Amurka ne suka fara hura wutar zargin inda a watan Maris ɗanmajalisar Amurka Chris Smith ya yi kiran a saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake da damuwa a kansu.

Haka ma a watan Oktoba Sanata Ted Cruz da ɗanmajalisar wakilai Riley Moore dukkaninsu ƴan Republican suka zargi gwamnatin Najeriya da yin ko oho da kisan da ake yi wa kiristoci.

Wannan matakin ya ƙara wa masu da'awar ana kashe kiristoci ƙwarin guiwa a Najeriya tare da ƙara ingiza su a kasar da ta yi fama da rikicin ƙabilanci da na addini a baya da kuma ke ci gaba da tasiri a wannan zamanin na tsarin siyasa a kasar.

Najeriya dai ta tade tana fama da tashe-tashen hankula da dama wadanda masana suka ce ana kashe Kiristoci da Musulmai ne ba tare da bambancewa ba.

Me gwamnatin Najeriya ta ce?

Tinubu

Asalin hoton, Tinubu X

Gwamnatin Najeriya ta musanta iƙirarin cewa ta kasa kare rayukan mabiya addinin Kirista daga hare-hare bayan barazanar Donald Trump ta ɗaukar matakin soji.

Ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriya Daniel Bwala, ya shaida wa BBC cewa mayaƙa na kai hare-hare ne kan kowa ba tare da bambancin addini ba.

Ya ce Najeriya za ta yi maraba da haɗin kan Amurka wajen yaƙi da matsalar.

Tun da farko shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar ya ce ikirarin ba ya nuna gaskiyar yanayin Najeriya.

"Yancin gudanar da addini ya kasance ginshiki da aka sanmu da shi kuma zai ci gaba da kasancewa haka," in ji shugaba Tinubu.

Tun da farko ma'aikatar harakokin wajen Najeriya ta musanta iƙirarin Trump da kuma zargin ana kisan kiristoci a Najeriya a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.

"Ƴan Najeriya suna da ƴancin gudanar da addininsu yadda ya kamata, kuma suna gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba," a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ce a ƙarƙashin mulkin Tinubu, gwamnatinsa na ƙoƙari sosai wajen yaƙi da ta'addanci da ƙarfafa gwiwa da kare rayuwar al'umma ba tare da nuna bambanci.

Gwamnatin ta ce Najeriya za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka da ƙasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Najeriya dai ƙasa ce mai yawan Musulmi a yankin arewaci da kuma kirista a yankin kudancin kasar.

Kasar ta daɗe tana fama da matsalolin tsaro, musamman rikicin Boko Haram da ya kashe dubban mutane tare da raba sama da mutum miliyan biyu da muhallansu a yankin arewa maso gabashi.

Najeriya kuma na fama da matsalar yanfashin daji da ke satar mutane domin kuɗin fansa a yankin arewa maso yammaci.

Akwai kuma rikicin makiyaya da manoma a yankin arewa maso tsakiya, wanda ake alaƙantawa da addini tsakanin manoma kiristoci da kuma Fulani makiyaya musulmi.

Ko a wa'adinsa na farko, shugaba Trump ya taɓa saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake da damuwa da su, amma wanda ya gaje shi Joe Biden ya cire Najeriya daga cikin jerin ƙasashen a 2021.

Amurka na da iko?

Sai dai a daidai lokacin da ake ganin ci gaba da nazarin batun na Trump, masana ne suke ta tafka muhawara kan yiwuwar aiwatar da bazaranar ta shugaban na Amurka da kuma abin da haka ke nufi.

Kundin tsarin mulkin Amurka, sashe na 8 ya ce majalisar ƙasar tana da ikon 'ayyana yaƙi da yin dokokin da suka danganci mamaye ƙasa da teku.'

Sai dai kundin na Amurka ya tanada cewa majalisar tsaron ƙasar ce take da wuƙa da nama kan tsare irin matakin da ƙasar za ta ɗauka domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a wata ƙasa ta duniya.

A ɗayan ɓangaren kuma, Majalisar Ɗinkin Duniya ta sha nanata cewa ba za ta lamunta a yi amfani da ƙarfi kan wata ƙasa ba, sai dai domin kare kai.

Me doka ta ce kan wata ƙasa ta afka wa wata?

A game da abin da doka ta ce game da afka wa wata ƙasa, BBC ta tuntuɓi Barista Audu Bulama Bukarti, masani kan shari'a da tsaro a ƙasashen Afrika, inda ya ce Amurka ba ta hurumin kutsa wa Najeriya domin yaƙi da ta'addanci sai da izini.

A cewarsa, "Amurka ba ta da ikon afka wa Najeriya domin Najeriya ƙasa ce mai zaman kanta wadda take da cikakken ƴanci, kuma idan muka duba sassa daban-daban, ciki har da sashe na farko na dokokin kundin majalisar ɗinkin duniya, musamman sashe na farko wato UN Declaration ke nan za mu ga cewa ta tabbatar wa da kowace ƴancinta kuma ta haramta wata ƙasa ta faɗa wa wata ƙasa."

Ya ce haramun ne kai-tsaye a dokokin ƙasa da ƙasa Trump ya afka wa Najeriya ko kuma ya ce zai zo ya yi wani abu na yaƙi da kowace irin kowace irin ƙungiya ba tare da izinin Najeriya ba.

"Hatta jiragen Amurka su shigo sararin samaniyar Najeriya ko shigo ƙasar ba tare da amincewar ƙasar ba haramtacce abu ne."

Shawarwari huɗu ga gwamnatin Najeriya

Sai kuma masanin shari'ar ya ce idan Amurka ta yi gangancin kutsen, abubuwa da dama za su iya faruwa "domin kuwa ɗaya daga cikin alhakin da doka ta ɗora wa gwamnatin Najeriya shi ne kare ƴancin iyakoki da ƴancin ƙasar, saboda haka ka ga ke nan idan Trump ya afka wa Najeriya, ya zama tilas ke nan a kan Najeriya ta yi amfani da sojojinta da makamanta wajen kare kanta."

Sai Bulama ya ce wannan abu ne mai matuƙar wahala saboda a cewarsa Najeriya ta san Amurka ta fi ƙarfinta.

"Amma Najeriya za ta iya garzayawa Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi majalisar ta yi Allah-wadai da abin, sannan ta ta umarci Amurka ta fice daga ƙasar. Amma shi ma wannan ba lallai ya faru ba, tunda ko da majalisar ta yi kudurin, Trump zai iy yin biris kuma ba za ta iya wani takabus wajen fitar da shi ba."

Amma Bulama ya ce yana ganin Trump na cika baki ne, "domin ina ganin zai yi wahalar gaske ya kai hari ba tare da izinin Najeriya ba, sai dai irin harin da suka riƙa kai wa Iraki da Syria, su turo jirage su jefa bama-bamai su gudu, kuma irin wannan ba zai samar da nasarar da ake buƙata ba. Kuma su kansu majalisun Amurka za su taka masa birki."

A ɓangaren matakan da ya kamata Najeriya ta ɗauka, Bulama ya jero wasu abubuwa da ya ce suna da matuƙar muhimmanci:

  • Taka-tsantsan: "Kada su biye wa Trump wajen mayar masa da martani a kafofin sadarwa. Hakan zai iya fusata shi."
  • Diflomasiyya: "Najeriya ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen ilimantar da Trump da gwamnatin Amurka cewa matsalar tsaro a Najeriya tana shafar musulmi da kirista ne. Akiwa ƙididdiga ciki har da wani na gano a binciken da na yi digirin digirgir ɗina da ke nuna cewa an fi kashe musulmi a hare-haren Najeriya, kuma an kai hari kan maallatai sama da coci-coci."
  • Ilimantarwa: "Ya kamata gwamnatin ta ilimantar da ƴan Najeriya idan Trump ya ɗauki matakin daina ba ƙasar tallafi, misali na maganin HIV, ba a kan musulmi kaɗai zai tsaya ba. Haka ma idan aka daina sayar wa Najeriya da makamai, matsalolin tsaro za su ƙaru ne a ƙasar baki ɗaya."
  • Yaƙi da matsalar tsar da gaske: "Duk da mun san cewa ba da gangan gwamnati take bari ana kashe mutane ba, amma lallai mun yi amannar akwai sakaci."