Sabbin dabaru uku da Boko Haram ta ɓullo da su wajen kai hare-hare

Jirgi maras matuki

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Wasu rahotonni na cewa ƙungiyar Boko Haram - da ta yi ƙaurin suna wajen ƙaddamar da munanan hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula a Najeriya - na sabunta dabarun kai hare-harenta.

Alƙaluman wata ƙungiyar ACLED mai sanya ido kan tsaro da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito sun nuna cewa ya zuwa yanzu Boko Haram ta kai hari sau 333, a yankin arewa maso gabashin Najeriya a wannan shekarar ta 2025.

To sai dai kuma kamfanin samar da tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited ya ce bisa alƙaluman da ya tattara, ƙungiyar Boko Haram ta kai hare-hare har sau 199 daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Satumbar 2025.

Wani abu da masana ke danganata yawaitar hare-haren ƙungiyar shi ne sabunta dabarunta wajen ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula.

A lokaci zuwa lokaci dai Boko Haram kan sabunta dabarun da take amfani da su wajen kai hare-hare, lamarin da wasu ke gani na daga cikin dalilan da suka sa aka kasa kawar da ƙungiyar.

A cikin wannan muƙala mun duba wasu sabbin dabaru da ƙungiyar ta ɓullo da su wajen kai sabbin hare-hare.

Sabbin dabarun da Boko Haram ta ɓullo da su

Dokta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security mai nazarin al'amuran tsaro a yankin sahel, ya ce dabaurin da ungiyar ke amfani da su a yanzu, dama wasu ta dae tana amfani da su, sai dai kawi ta sabunta byadda take amfani da su.

Dabarun da ungiyar ke amfani da su a yanzu sun haɗa da:

Amfani da jirage marasa matuƙa

Jirgi maras matuƙi

Asalin hoton, DJI

Bayanan hoto, Ƙungiyar na amfani da jiragen don tattara bayanan sirri da kai hari

Dokat Kabiru Adamu ya ce mayaƙan Boko Haram sun jima sun amfani da jirage marasa matuƙa, sai dai a kullum suna ƙara samun ƙarin fasahar amfani da su.

Ya ce suna amfani da jiragen marasa matuƙa wajen yin abubuwa kamar haka:

Tattara bayanan sirri: Masanin tsaron ya ce mayaƙan ƙungiyar kan yi amfani da jiragen wajen samun bayanan ida sojoji suke domin ƙoƙarin kauce wa haɗuwa da su.

Kai hare-hare: Dokta Kabiru Adamu ya ce mayaƙan Boko Haram kan yi amfani da jiragen marasa matuƙa wajen ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro da fareren hula.

''Kodayake har yanzu mayaƙan ƙungiyar ba su laƙanci yadda ake kai hari da ire-iren waɗannan jiragen ba'', in ji masanin tsaron.

Harin taron dangi

Wata dabara da ƙungiyar Boko Haram take amfani da ita a baya-bayan nan - wadda kuma Kabiru Adamu ya ce ta jima - iyta ce dabarar kai hare-haren taron dangi a lokaci guda.

Dabara ce da suka amfani da nau'ikan hare-hare kamar biyu ko uku a kan wuri guda, kamar yadda ya yi ƙarin bayani.

''Da fari za su iya jefa bom, bayan fashewarsa, sannan mayaƙanta da ke wurin su buɗe wuta da makamai, ko su turo jiragen marasa matuƙa, su kai hari'', in ji shi.

Kai hare-hare wurare mabambanta a lokaci guda

Mayaƙan Boko Haram

Asalin hoton, .

Wata dabara da ba a saba ganin ƙungiyar na amfani da ita ba ita ce kai hari wurare daban-daban amma a lokaci guda.

Dokta Kabiru Adamu ya ce a karon farko ƙungiyar ta yi amfani da wannan dabara a makon da ya gabata.

''Ta ƙaddamar da hare-hare har guda uku kan sansanonin soji, biyu a jihar Borno, ɗaya kuma a jihar Yobe, kuma duka a lokaci guda suka kai su'', in ji shi.

Shin sabbin dabarun na yi mata aiki?

Dokta Kabiru Adamu ya ce dangane da ko dabarun na aiki, akwai abubuwa guda biyu da za a yi la'akari da su.

''Na farko shi ne ikirarin da sojojin Najeriya suka yi na kashe kusan mayaƙa 50 cikin wadanda suka kai harin, inda ikirarin sojojin ya tabbata to dabarunsu ba sa aiki'', in ji shi.

Amma kuma ya ce a gefe guda su ma mayaƙan sun wallafa hotuna da bidiyoyin irin ɓarnar da suka yi wa sojojin a shafukan sada zumunta.

''To in da gaske ne waɗannan hotuna da suke nuna sun ƙona wasu motocin, to za a iya cewa dabarun nasu an aiki, kamar yadda suka tsara'', kamar yadda ya bayyana.

Me ya sa ƙungiyar ke yawan sabunta dabarun yaƙin?

Dokta Kabiru Adamu ya ce yawan sabunta dabarun yaki da ƙungiyar Boko Haram ke yi ba ya rasa nasaba da alakarta da manyan ƙungiyoyi iyayenta.

"Alal misali ita ƙungiyar Boko Haram tana da alaƙa da ƙungiyar Al-qaeda, yayin da ita kuma ƙungiyar ISWAP ke da alaƙa da uwar ƙungiyar IS, to duka ƙungiyoyi suna samun dabarun yaƙi da waɗannan manyan ƙungiyoyin'', in ji shi.

''Baya ga wannan kuma akwai wasu sassa a waɗanna ƙungiyoyi, waɗanda ba su da wani aiki sai kula da dabarun yaƙi, don haka suma suna aiki ba dare ba rana domin samar wa ƙungiyoyin sabbin dabarun yaƙi'', in ji shi.

Me ya kamata sojoji su yi?

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, DEFENSE HQ

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban kamfanin Beacon security ya ce abin da ya kamata sojoji su yi shi ne kar su jira sai Boko Hamar ta samu sabbin dabarun yaƙi sannan su yi tananin yadda za su magance hakan.

  • Ƙarfafa hanyoyin tattara bayanan sirri

''Yana kyau kullum a ce cikin tunani sojojin suke na yadda za su daƙile dabarun waɗanna ƙungiyoyi, kamata ya yi a ce kullum su ne a gaba'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa yana da kyau sojoji sun ƙarfafa hanyoyin tattara bayanan sirri, domin magance bazaranar waɗannan ƙungiyoyi.

"Alal misali akwai uwayen ƙungiyoyin nan kamar al-Qaeda da IS galibi waɗannan ƙungiyoyi da umarninsu suke aiki, to yana da kyau sojojin su ƙarfafa hanyoyin samun bayan sirri na irin umarnin da waɗannan ƙungiyoyin ke bayarwa'', in ji shi.

Haka kuma masanin tsaron ya ce galibi waɗannan ƙungiyoyi kan musayan bayanan sirri na dabarun yaƙi, ''to nan ma yana da kyau sojojin sun yi ƙoƙarin yadda za su samu waɗanann bayanai na sirri'', in ji shi.

  • Toshe hanyoyi huɗu da ƙungiyoyin ke numfasawa

Dokta Kabiru Adamu ya ce akwai akwai abubuwa guda huɗu da suka zama su en tamkar hanyoyin da waɗannan ƙungiyoyi ke numfasawa ko shaƙar isa, ''to dole sojoji su yi ƙoƙarin toshe su'', in ji shi.

Waɗannan abubuwa sun haɗa da:

  • Hanyoyin da suke samun kuɗaɗe
  • Hanyoyin da suke samun makamai
  • hanyoyin da suke ɗaukar sabbin mayaƙa
  • hanyoyin walwalarsu, wato yadda suke zirga-zirga
  • A sanya al'umma cikin yaƙi da ƙungiyoyin

Dokta Kabiru Adamu ya ce yana da kyau a sanya gwamnonin jihohi cikin aikin yaƙi nda irin waɗannan ƙungiyoyi, da kuma sauran jama'a.

''Akwai tanade-tanaden dokokin da ake da su an yaƙi da ta''addanci, da wasu gwamnonin da dama ba su sani ba, don haka yana da kyau a sanar da su, domin su fahimta'', in ji shi.