Wane tasiri mulkin Trump karo na biyu zai yi ga duniya?

Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump a ranar 22 ga watan Disamba 2024 a jihar Arizona.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Donald Trump
Lokacin karatu: Minti 8

Donald Trump sai sake shiga fadar White House a ranar 20 ga watan Janairu sakamakon nasarar da ya yi a zaɓen shugaban ƙasar Amurka a watan Nuwamba.

Damarsa ta biyu na zama shugaban ƙasar Amurka zai mayar da hankali kan sake fasalin tsare tsaren Amurka na ƙasashen waje, a yayin da ya gudanar da ajandarsa da ya kira '' Amurka a farko'', wanda akwai yiwuwar zai shafi rayuwar miliyoyin mutane da ke ƙasahen waje.

Bari muyi dubi zuwa ga yadda Mista Trump, wanda yayi shugabancin Amurka daga shekarar 2017 zuwa 2021, zai fuskanci wasu manyan matsaloli a duniya.

Ukraine

Mr Trump na magana a tsaye kusa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a wani ɗakin taro a birnin New York a watan Satumban 2024.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A baya, Trump ya yi barazanar katse bayar da tallafin kuɗi ga Ukraine

A lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe, Mista Trump ya maimaita a lokuta da dama cewa zai iya kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine ''a rana ɗaya'', ba tare da ya bayar da bayanin yadda zai yi hakan ba.

Trump ya daɗe ya na suka kan biliyoyin daloli na tallafin soji da Amurka ke bai wa Ukraine tun lokacin da Rasha ta yi mamaya a shekarar 2022.

Hakan ya sanya damuwa a zukatan masu goyon bayan Ukraine kan cewa zai iya tunzura ƙasar sadaukar da wasu ɓangarori na ƙasar saboda a kawo ƙarshen yaƙin.

Mutumin da aka zaɓa ya zama wakili na musamman ga Mista Trump a Ukraine da Rasha, Keith Kellog, ya shaida wa gidan talibijin na Fox News a farkon watan Janairu cewa ya na sa ran za a samu maslaha cikin kwanaki 100.

Mista Kellog ya bayar da shawara a wata takarda da ya gabatar a watan Afrilun bara cewa Ukraine za ta cigaba da samun tallafi daga Amurka ne kawai idan ta amince ta zauna kan teburin tattaunawar neman zaman lafiya da Moscow.

Mista Trump ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin na so ya haɗu da shi, kuma masu taimaka masa na ''shirya hakan''.

Ƙungiyar tsaro ta Nato

Sojoji a tsaye kan motocin yaƙi da tutar Amurka a kansu a lokacin da sojojin Amurka su ka gudanar da wani aikin soji a ranar 5 ga watan Maris kusa da Gniew da ke Poland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mista Trump ya daɗe da cewa mambobin Nato su ƙara ƙuɗaɗen kashewa a ɓangaren tsaro
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙungiyar Nato, wato ƙungiyar ƙawancen sojoji da ta haɗa ƙasashe 32, ciki har da Amurka da Birtaniya da Jamus, na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da Trump ke adawa da su.

Lokacin wa'adin mulkinsa na farko, ya yi barazanar janye Amurka daga ƙungiyar idan sauran ƙasashe mambobin ƙungiyar suka gaza cimma manufar da ake da ita ta kashe kashi 2 cikin 100 na tattalin arziƙinsu na cikin gida a fannin tsaro.

Ya kuma ce Amurka ba za ta samar da tsaro ga duk ƙasar da ba ta biyan kasonta idan aka kawo mata hari.

A farkon watan Janairun 2025, Trump ya yi kira ga ƙasashen Turai da ke ƙungiyar Nato su nunka abin da suke kashewa zuwa kashi 5 cikin ɗari na tattalin arziƙinsu.

Shafin yanar gizo na gangamin yaƙin neman zaɓensa ya ce burin Trump shi ne '' sake yin nazari'' kan manufofi da burukan ƙungiyar Nato.

Ana samun banbancin ra'ayi kan ko Trump zai taɓa janye Amurka daga ƙungiyar ƙawancen.

Sai dai masu fashin baƙi na ganin cewa akwai hanyoyi da dama da zi iya bi wajen rage ƙarfin ƙawancen ba tare da ya fitar da Amurka a cikinta ba- kamar rage adadin sojojin Amurka da ke Turai.

Yankin Gabas ta Tsakiya

Masu zanga zanga a Iran ɗauke da zanen hotunan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump lokacin wani zanga zangar ƙin jinin Isra'ila a Tehran ranar 10 ga watan Janairun 2025

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alaƙar mara daɗi tsakanin Amurka da Iran na daga cikin kalubalen da Trump zai fuskanta a gabas ta Tsakiya.

Mista Trump zai kama aiki ne jim kaɗan bayan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki. Masu taimaka masa sunyi aiki tare da tawagar shugaban Amurka mai barin gado Biden da kuma masu shiga tsakani na Qatar da Masar a kan tattaunawar zaman lafiyan. Shugabannin biyu na iƙirarin su ne suka samar da nasarar yarjejeniyar.

Sai dai za a fuskanci kalubale a gaba wajen aiwatar da yarjejeniyar, musamman kammala matakin ƙarshe wanda ya haɗa da, '' ƙawo ƙarshen yaƙin'' a kalaman Mista Biden.

A wa'adin mulkinsa na farko, Trump ya ƙaddamar da tsare tsare da ke goyon bayan Israila, ciki har da ayyana birnin ƙudus a matsayin babban birnin Isra'ila, tare da mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin daga Tel Aviv.

Gwamnatinsa ta kuma ɗau wasu matakai kan Iran, kamar fita daga cikin yarjejeniyar nukiliya, ƙara sanya takunkumai kansu, da kuma kashe Janar Qassem Soleimani- Kwamandan sojojin Iran da yafi kowanne ƙarfi.

Masu suka na ganin cewa tsare tsaren Trump sun samar da munanan sakamako kan yankin da kuma ware Falasɗinawa.

Trump ya kuma shiga tsakani wajen cimma yarjejeniyar Abraham - yarjejeniya mai cike da tarihi da ta gyara alaƙar diflomasiyya tsakanin Isra'ila da haɗaɗɗiyar daular larabawa da Bahrain da Sudan da Morocco.

Sai dai an amince da hakan ne ba tare da Isra'ila ta amince da ƴancin kan Falasɗinu ba- wani sharaɗi da a baya ƙasashen larabawa suka sanya kan irin wannan yarjejeniyar.

Bayan sanar da tsagaita wuta, Mista trump ya ce zai bunƙasa '' zaman lafiya ta hanyar ƙarfafawa'' a yankin da kuma inganta yarjejeniyar Abraham.

Wannan na iya nufin yin aikin samar da yarjejeniya tsakanin Saudi Arabiya da Israi'ila.

China

Jirgin yakin Taiwan lokacin da ya tashi sama da keta rukunin wasu gidaje, a lokacin atisayen sojin sama a sansaninsu da ke Hsinchu, Taiwan, ranar 7 Nuwambar, 2024

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, China da Taiwan na cigaba na cigaba da gudanar da atisayen sojoji a yayin da zaman ɗarɗar ke ƙaruwa a yankin.

Tunkarar China da Amurka zatayi na da tasiri masu muhimmanci kan tsaro da cinikayya a duniya.

A wa'adin mulkinsa na farko, Trump ya haddasa matsalolin kasuwanci da China.

A wannan karon kuwa, ya ƙaƙaba harajin kusan kashi 60 kan kayyayakin da ake shigowa dasu Amurka daga China.

Ana kallon zabinsa na sakataren harkokin wajen Amurka -Marco Rubio- da mai bayar da shawara kan tsaron ƙasa - Mike Waltz- a matsayin wata barazana ga China kuma hakan ya nuna ƙarara cewa su na kallon Beijing a matsayin babbar barazana.

Lamarin Taiwan ya kasance ya na da matuƙar muhimmanci.

Amurka na cigaba da bayar da tallafin soji ga tsibirin da ke mulkin kansa, wanda China ke kallo a matsyain yankin da ya ɓarke wanda daga bisani zai dawo ƙarƙashin ikon Beijing.

A tarihi, Amurka ta ƙi fitowa fili ta faɗi matakin da zata ɗauka idan China ta yi mamaya a Taiwan, duk da dai Mista Biden ya fi kowani shugaban Amurka ƙarfin hali zuwa yanzu, inda ya ce Amurka za ta kare Taiwan.

A lokacin yaƙin neman zaɓe, Mista Trump ya ce ba zai buƙaci amfani da ƙarfin sojoji ba wajen hana China yi wa Taiwan ƙawanya ba, saboda Shugaba Xi '' na ganin mutunci na kuma ya san inada taurin kai'' - kuma ya ce zai sanya haraji kan ƙayyaykin da ake shigowa dasu daga China idan hakan ya faru.

Sauyin yanayi

Wani bututun mai da ke aiki a ranar 5 ga watan Agustan 2022 kusa da Ventura a California

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana sa rai sabon gwamnatin za ta mayar da hankali kan makamashi mara illa ga muhalli.

An san shugaban Amurka mai jiran gado a matsayin mai shakku kan sauyin yanayi wanda ya bayyana ƙoƙarin bunƙasa amfani da makamashi mara gurbata yanayi a matsayin wata ''yaudara''.

Akwai yiwuwar Trump zai sake janye Amurka daga yarjejeniyar sauyin yanayi na Paris na 2015, wani mataki da wanda ya gabace shi Joe Biden ya warware a 2021.

Kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya sha alwashin ƙara samar da mai domin samar da makamashi mai arha.

Gabanin zaɓen, gangamin yaƙin neman zaɓen Trump sunyi alƙawarin dakatar da 'shigar da ƙara mara amfani'' daga masu fafutukar kare muhalli, cire tallafi kan samar da makamashi daga iska, katse haraji kan masu samar da mai da iskar gas da garwashi, da kuma janye dokokin da Biden ya sanya kan iskar da motoci ke fitarwa.

A yayin da ƙwararru kan sauyin yanayi ke ganin nasarar Trump na zama Shugaban ƙasa babbar koma baya ga ayyukan sauyin yanayi a duniya, sun kuma ce sauyawa zuwa makamashi mara illa ga muhalli na cigaba da shiga cikin tattalin arziƙin Amurka da ma na duniya.

Shige da Fice

Layin baƙin haure a gaban cactii da tsaunuka a iyakar Amurka da Mexico a ranar 7 ga watatn Disamba 2023 a Lukeville da ke Arizona.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rage kwararar 'yan cirani na daga cikin manyan alkawuran da Mr Trump ya yi a lokacin yakin neman zabe

Mista Trump ya sha alwashin mayar da miliyoyin baƙin haure waɗanda su ka shigo Amurka ba bisa ƙaida ba ƙasashensu.

Ya ce zai ƙaddamar da '' aikin korar baƙin haure mafi girma a tarihin Amurka'' a ranar sa ta farko a fadar White House.

Akwai ƙiyasin baƙin haure miliyan 11 da ke rayuwa a Amurka ba bisa ƙa'ida ba, akasarinsu sun shafe shekaru suna rayuwa da kuma aiki a Amurka. Ya ce zai fara da '' masu aikata laifi'', sai dai baiyi ƙarin bayani kan hakan ba.

Mista Trump ya kuma ɗau aniyar kawo ƙarshen bayar da shaidar zama ɗan ƙasa kai tsaye ga duk wanda aka haifa a Amurka, abin da ake kira haƙƙin zama ɗan ƙasa na haihuwa.

A lokacin yaƙin neman zaɓen sa, ya yi amfani da zafafan kalamai kan shigowar baƙin haure, inda ya ce zai kara tsaro kan iyakokin ƙasar, ya kuma ce zai dawo da haramcin shiga ƙasar daga wasu ƙasashe mai cike da ce-ce-kuce da ya sanya a baya, akasari daga ƙasashen musulmai.

Sai dai ƙwararru a fanin shige da fice na ƙasashe na ganin cewa tsare tsaren Mista Trump za su gamu da matsaloli da dama kamar a fannin shairi'a, kuɗi da kuma siyaysa.

Greenland da mashigar ruwa ta Panama

Wasu rukunin gidaje a Disko Bay, ranar 15 ga watan yulin 2024 a Ilulissat da ke Greenland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Trump ya fara bayyanan aniyar sa ce ta siyan Greenland a shekarar 2019 a lokacin wa'adin mulkinsa na farko.

Shugaban Amurkan mai jiran gado ya tayar da ƙura da kalamansa da ya ce ya na so ya siya yankin Greenland kuma ya karɓe ikon mashigar ruwa ta Panama.

Da aka tambayesa a farkon watan Janairu ko zai yanke shawarar cire amfani da soji ko ƙarfin tattalin arziƙi wajen cimma waɗannan buruka, ya amsa cewa: ''A'a, ba zan iya bayar da tabbaci kan kowanne daga cikin abubuwa biyun nan ba''.

Yankin Greenland da ke Denmark da bashi da yawan mutane, wani wuri ne da ke da babban sansanin tsaron sojin sama na Amurka, kuma yankin nada adadi mai yawa na albarkatun ƙasa da ba kasafai ake samunsu a wasu ƙasashe ba waɗanda ke da amfani sosai wajen samar da batura da wasu kayyaykin fasaha.

Denmark ta jaddada cewa yankin ba na siyarwa bane.

A watan Disamba, Mr Trump ya ce Panama na ƙarbar kuɗaɗe masu yaywa da bai kamata ba domin bi ta mashigar ruwan kuma idan ba a daina 'cutar' ba, zai buƙaci a dawo da ita ƙarƙashin ikon Amurka.

Ya kuma ce ya na da damuwa kan China, wadda ta ke yawan amfani da mashigar ruwan wadda kuma ta ke da manyan hannayen jari a Panama.

Panama ta ce ba gudu ba ja da baya kan ikonta kan mashigar ruwar, kuma babu wani katsalandan da China ke yi kan mashigar ruwan.

Ana ganin ba abu mai yiwuwa bane Amurka ta ƙwace iko a waɗannan wuraren, sai dai kalaman Trump na nuna manufar sa ta '' Amurka ce farko'' wata barazana ce da karfin ƙasar a wajen iyakokin ƙasar.