Ko Tinubu ya samu nasarar sulhunta Wike da Fubara?

Asalin hoton, Bayo Onanuga
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da Ministan Abuja, Nyesom Wike da dakataccen gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara da dakataccen shugaban majalisar jihar, Martins Amaewhule, inda shugaban ya jagoranci sulhu da sasanci a tsakaninsu.
Wannan ya sanya mutane na nuna kyakkywar fata bayan abin da ya faru na ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers, wani abu da wasu suka bayyana a matsayin karan-tsaye ga dimokuraɗiyya.
Bayan ganawa da shugaban ƙasar, jagororin siyasar biyu sun yi jawabai masu nuna alamun cewa a shirye suke su mayar da wuƙaƙensu cikin kube.
Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ya ce, "mun amince mu yi aiki tare. Yanzu komai ya wuce. Da ma asali mun fito ne daga gidan siyasa ɗaya, kuma a matsayinmu na ƴan'adam, muna samun saɓani, sannan an yi sulhu. Yanzu komai ya wuce, babu wani saɓani kuma".
A baya masharhanta da dama sun riƙa ɗora wa Wike laifi kan caɓewar rikicin siyasa a jihar ta Ribas, inda ake zargin shi da hana ruwa gudu da ƙoƙarin yin kaka-gida a siyasar jihar duk da cewa zamaninsa ya wuce.
A nasa jawabin, Siminalayi Fubara ya ce "rana ce mai matuƙar muhimmanci domin zaman lafiyar jihar Rivers. Za mu yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da zaman lafiya."
A ranar 18 ga watan Maris na shekarar nan 2025 ce Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar Rivers, inda ya dakatar da gwamna da ƴanmajalisar jihar, sannan ya naɗa gwamnan riƙo a jihar domin jan ragamar mulkin jihar na wata shida.
A lokacin, Tinubu ya ce ya yi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, inda a cewarsa ba zai zuba ido yana kallo rikicin siyasar jihar ya wuce gona da iri ba.
Sai dai matakin ya janyo masa suka a fagen siyasar, musamman daga ɓangaren ƴan hamayya, inda suka zarge shi da yunƙurin amfani da takalmin ƙarfe domin daɗaɗa wa Nyesom Wike.
Daga cikin waɗanda suka soki matakin dakatar da zaɓaɓɓan gwamnan akwai tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El-Rufai da Femi Falana da ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya da sauransu.
Ba wannan ba ne karon farko da aka sanya dokar ta-ɓaci a Najeriya ba, domin a ranar 14 ga watan Mayun shekarar 2013, shugaban ƙasar na wancan lokacin, Goodluck Jonathan ya ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihohin arewa maso gabas saboda rikicin Boko Haram, sai dai a wancan lokacin ba a dakatar da gwamnonin ba.
Asalin rikicin

Asalin hoton, Bayo Onanuga
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rikici ya fara ne tsakanin Ministan Abuja Nyesom Wike da magajinsa, Siminalayi Fubara bayan sabon gwamna ya ɗare kan karagar mulki, inda aka fara jin ka-ce-na-ce a tsakaninsu.
Sai a lokacin zaɓen shugabannin jam'iyyar PDP na jihar saɓani ya ƙara fitowa zahiri, bayan ɓangaren Wike ya lashe zaɓukan, lamarin da masu goyon bayan gwamnan suka ce ba za ta saɓu ba, domin a cewarsu, gwamna ne jagoran jam'iyya a jihar.
Daga bisani rikicin ya sake ɗaukan sabon salo a lokacin zaɓen ƙananan hukumomin jihar, wanda aka yi a bara inda ɓangaren Wike suka ce ba za a yi ba, ɓangaren gwamna ya ce sai an yi, lamarin da ya sa aka je kotu, aka samu hukunce-hukunce mabambanta.
Daga bisani gwamnan ya dage sai an yi zaɓen, inda aka yi zaɓen sannan jam'iyyar APP wadda ake tunanin gwamna Fubara ya goya wa baya, ta lashe kujera 22 daga cikin ƙananan hukumomiN jihar guda 23.
Haka kuma rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar, inda mafiya yawan majalisar, su 27 suke tare da da Wike, sauran kuma guda uku suke tare da gwamna.
A lokacin ne ƴanmajalisar na hannun damar Wike suka sanar da komawa APC, inda sauran ukun na gefen Fubara suka sanar da cewa guda 27 sun rasa kujerarsu, lamarin da aka je kotu har aka kotun ƙoli, wadda ta dawo musu da kujerarsu, sannan ta soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Sai dai kafin nan, Fubara ya gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin jihar a gaban ƴanmajalisar da suke tare da shi, su uku, sannan ya sanya hannu a kasafin kuɗin, sannan ya rantsar da shugabannin ƙaramar hukumomin jihar, wanda aka zaɓa a zaɓen mai cike da taƙaddama.
Ana cikin haka ne Kotun Ƙoli ta soke zaɓen, sanan ta mayar da ƴanmajalisar jihar na hanun damar Wike su 27, sannan ta buƙaci a dakatar da ba Rivers kuɗin kasonta na wata-wata har sai Fubara ya sake gabatar da kasafin kuɗin jihar a gaban ƴanmajalisar mau rinjaye, lamarin da ya dawo da rikicin ɗanye.
Ana cikin wannan yanayi ne ƴanmajalisar dokokin jihar suka zargi gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu da saɓa wa ƙa'idar aiki da kuma ƙin amfani da hukuncin kotun ƙoli.
Ƴan majalisa 26 na jihar ta Rivers sun yi waɗannan zarge-zarge ne a wasu takardun koke biyu da suka tura wa shugaban majalisar, Martin Amaewhue.
Sun ce sun ɗauki matakin nasu ne "bisa dogaro da sashe na 188 na kudnin tsarin mulkin Najeriya na 1999", wanda ya tanadi cewa dole ne a samu kashi ɗaya cikin uku na ƴan majalisa su goyi bayan koken sannan kuma a tantance ainahin laifukan.
Yunƙurin tsige gwamnan ya tayar da ƙura, inda ya sake jefa jihar cikin tashin hankali, har aka fara samun labaran fashe-fashen bututun man fetur.
A daidai lokacin da ake batun tsige gwamnan ne, Tinubu ya sanar da dakatar da gwamnan da sauran zaɓaɓɓu tare da sanya gwamnan riƙo a jihar, bayan ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar.











