Abin da ya sa Ganduje ya yi murabus daga mukaminsa — APC

Asalin hoton, PT
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi ƙarin haske kan dalilan da suka sa Abdullahi Umar Ganduje, ya sauka daga muƙamin shugabancin jam'iyyar a wani yanayi na ba-zata.
Mutane dai sun yi zargin ruwa ba ya tsami banza, ko kuma dai da walakin goro a miya amma uwar jam'iyyar ta yi watsi da wannan hasashe.
Daraktan yaɗa labarai na jam'iyyar ta APC, Bala Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa babban dalilin da Ganduje ya bayar a game da murabus din na sa shi ne batun kiwon lafiya.
Ya ce," Ganduje ya nemi a amince ya sauka daga mukamin shugaban jam'iyya saboda ya mayar da hankali wajen kula da lafiyarsa."
Bala Ibrahim, ya ce „ Duk mutumin da ya haura shekara 70 dole ne ya yi taka-tsan-tsan domin kula da lafiyarsa domin ganin cewa tafiya ta yi kyau.”
" Shugaban kasa ya amince da murabus din na Ganduje haka suma 'yan kwamitin gudanarwa na jam'iyya suma sun amince, kai kowa dai ya amince da cewa matakin na Ganduje ya yi daidai ya je ya kula da lafiyarsa yayin da ita kuma jam'iyya za ta mayar da hankali wajen yin abubuwan da za su kara karfafata da samun nasara a zabukan da ke tafe." In ji shi.
Bala Ibrahim ya ce zargin da ake cewa ruwa ba ya tsami banza, ko kuma dai da walakin goro a miya a game da murabus din na Ganduje, duk ba gaskiya bane.
Ya ce," Duk abin da ba a tabbatar da shi ba haka kuma bincike ma bai tabbatar da shi ba to zato ne kuma zato zunubi ne ko da ya tabbata."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daraktan yada labaran jam'iyyar ta APC, ya ce "Game da batun wanda zai maye gurbin shugaban jam'iyyar da Sauka, dama jam'iyya na da kundin tsarin mulki wanda ya yi tanadi irin wannan wanda idan shugaban jam'iyya ya Sauka daga mukaminsa to za a zabi Daya daga cikin mukaddansa biyu wanda Daya daga arewa Daya kuma daga kudu to sai a bawa wanda ya fito daga yankin da shugaban da ya yi murabus ya fito a bashi rikon kwarya kafin a gudanar da zaben wanda zai gaji kujerar."
Ya ce," A wannan hali mukaddashi na arewa tun da Ganduje daga shiyyar ya fito wanda shi ne Bukar Dalori, shi ne zai rike kujerar na wucin gadi har lokacin da aka zabi sabon shugaban jam'iyyar."
Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga muƙamin shugabancin jam'iyar ne bayan kwashe ƙasa da shekara biyu yana jagorancin jam'iyyar.
Murabus din nasa na zuwa ne bayan wani rudani da aka samu kimanin mako ɗaya da ya gabata a lokacin taron jam'iyyar ta APC na arewa maso gabashin ƙasar.
A lokacin taron, wasu daga cikin ƴan jam'iyyar sun nuna fushi kan rashin bayyana sunan mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima a matsayin wanda zai mara wa Tinubu baya a takarar shugaban ƙasa ta shekara ta 2027.










