Ba zan fice daga jam'iyyar PDP ba - Muftwang

Gwamnan jihar Filato Caleb Muftwang

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Gwamna Caleb Muftwang
Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnan Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, Caleb Muftwang ya musanta rahotannin cewa yana daga cikin gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP da ke shirin komawa jam'iyya mai mulki ta APC.

A kwanan nan ne dai wasu jaridun ƙasar suka ambato shi a cikin gwamnonin da ke shirin sauya sheƙa daga babbar jam'iyyar adawar daidai lokacin da rikicin cikin gida ya dabaibaye ta.

To sai dai , Gwamna Muftawang ya shaidawa BBC cewa ba kamshin gaskiya a wannan zancen:

''Akwai abokina da ya turo man da wannan labari sai na ce ai ba a hana mai farauta neman namun daji''

''Na tabbata sun ga wani abun sha'awa a wurinmu, shi ya sa suke ganin cewa idan muka shiga jam'iyyarsu ta APC za mu kawo mu su ƙaruwa, kamar yadda ku ka karanta a jarida haka ni ma na karanta''

''Yanzu dai ba bu shakka ƴan jarida sun gan ni a zaman PDP kuma ni shugaba ne a cikin jam'iyyar PDP, ban bar ta ba kuma da yardan Allah zan ci gaba da zama a PDP'', in ji shi .

Gwamnan jihar Filato ya ce ma su wannan kiran sun yi haka ne saboda a cewarsa jam'iyyar APC a jihar Filato ba ta yi sa'ar shugabanni ba.

''JamI'yyar APC a jihar Filato ba ta yi sa'ar shugabani ba saboda haka su waɗanda su ke riƙe da APC a tarraya su na marmarin shugabanni na ƙwarai su shigo APC''.

''Akwai kuma waɗanda ba a yi da su a jam'iyyar ta APC waɗanda ke marmarin abubuwan da mu ka yi a Filato da mutane su na murna ''.

''Amma mun sa Allah a gaba a siyasar mu da kuma jama'a. Duk inda Allah ya nufe mu duk inda jama'a suke son mu tafi to wurin zamu je'', in ji shi.

Game da rikicin jam'iyyarsu ta cikin gida da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kuma gwamnan ya ce a zaman da suka yi a baya bayanan sun ɗinke ɓarakar kuma ta koma tarihi.

''Akwai zama na musaman da aka yi da zama na haɗin kai tare da kawar da banbance -banbancen da suka kawo rarrabuwar kawuna a cikin jam'iyya'',

''Ina ji mun kai shekara guda da wani abu muna fama da rigingimun cikin gida amma da yardar Allah mun ƙetare wannan gada. Saboda da haka masu goyon bayan wannan jam'iyya kama daga shugabani da sauran mutane duk suna murna kan zaman da muka yi a baya baya nan . Da yardan Allah wannan ya zama tarihi'', in ji shi.