Yunƙurin haɗewar jam'iyyun adawa ba ya tayar mana da hankali - Dalori

Asalin hoton, OTHERS
Sabon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa da ya kama aiki ranar Litinin, Ali Bukar Dalori, ya lashi takobin jagorantar jam'iyyar don kai wa ga nasara.
Dalori, wanda kafin ɗarewarsa kujerar, shine mataimakin shugaban jam'iyyar na Arewacin ƙasar, ya ce zai yi ƙoƙarin haɗa kan ƴaƴan jam'iyyar da kuma yi wa kowa adalci, ba tare da nuna wani fifiko ba.
A hirarsa ta farko da BBC bayan kama aiki a matsayin shugaban jam'iyyar APC, Dalori ya ce za a yi ƙoƙarin shawo ɓarakar da ta kunno kai tsakanin mambobin jam'iyyar a matakin jihohi da mazabu da ƙananan hukumomi:
''Dole na tashi na nuna wa duk ƴan siyasar APC cewa na yi iyakacin gwargwadona wajan sasanta waɗanda suka samu matsala da juna''
'' Zan zauna da su ko kuma na naɗa wakilai waɗanda za su je su samesu a shirya wannan tafiya fiye da na da domin siyasa ta na buƙatar mutane kuma siyasa ta na buƙatar kula da mutane'', in ji shi.
Game da babban taron jam'iyyar APC ta ƙasa da aka tsara gudanarwar a wannan shekara, shugaban jamiyyar na riƙo bai bayana lokacin da taron zai gudana ba saboda a cewarsa abu ne da ke buƙatar shawarar jiga-jigan jam'iyyar.
''Akwai manya -manyan wanɗanda ya kamata mu yi shawara da su, waɗanda su ne za su bada umarni a kan ko taron zai gudana ko kuma a'a''
Sai dai a bayanne ta ke cewa jam'iyyar na fuskantar ƙalubale musaman a matakin jihohi, idan aka dubi abubuwan da suka faru a yankin arewa maso gabashin ƙasar a baya baya nan wanda yanki ne da shugaban jamiyyar ta APC ya fito amma Hon Dalori ya ce duk abubuwa ne da siyasa ta gada:
'' Siyasa ta gaji haka, duk bakinmu ɗaya kuma kanmu a haɗe yake kuma har yanzu muna aiki da dukansu,'' in ji shi.
Shugaban jam'iyyar ta APC ya yi iƙirarin cewa tsoro game da makomar siyasar wasu manyan ƴaƴan jam'iyyun adawa na cikin dalilan da suka sa suka sauya sheƙa zuwa jamiyyar APC mai Mulki.
''Ban dan wani abu ba , sun tsorata, in suka tsaya a can, ba za su yi zaɓe ba, sun zo su bi mu ne domin samun biyan buƙatunsu ne'',
''To ina ganin fashewar da ake tsamani, ba za ta faru ba domin mun ɗinke ta da zare mai ƙarfi wanda ba zai tsinke ba''
Ya kuma bayyana ƙoƙarin haɗewar da wasu jagororin hammaya suke yi a matsayin wani abu da ba zai yi tasiri ba kuma ba zai tayar mu su da hankali ba.














