Me ya bambanta haɗakar APC da ta ADC?

ADC

Asalin hoton, Atiku/X

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Laraba wasu gaggan ƴan hamayya a Najeriya suka sanar da dunƙulewarsu a jam'iyyar ADC domin yin haɗaka a ƙalubalanci ƙudirin shugaba Bola Tinubu na tazarce a 2027.

Ƴan siyasar, ƙarƙashin jagorancin sanata David Mark, sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi da Rotimi Amaechi da Rauf Argebesola da Malam Nasiru El- Rufai da dai sauran jiga-jigan ƴan siyasa daga kudu da arewacin ƙasar.

Irin wannan haɗaka ce dai a shekarar 2015 ta bai wa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari damar jagorancin ƙasar, sakamakon ƙalubalantar shugaban lokacin mai neman tazarce, Goodluck Ebele Jonathan a ƙrƙashin jam'iyyar APC.

Hakan ne ya sa ƴan Najeriya ke tambayar ko akwai bambanci tsakanin jam'iyyun haɗakar guda biyu?

Sabon salon haɗaka

Malam Kabiru Sufi masanin siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a kano wato CAS ya ce saɓanin haɗakar da aka cimma kafin kafa jam'iyyar APC, inda aka rusa wasu jam'iyyu sannan wasu suka bar jam'iyyunsu kafin aka gina haɗakar, haɗakar ADC ta sha bamban.

"A wannan karon ƴan jam'iyyun ne suka fito daga jam'iyyunsu suka shiga jam'iyyar da take da rijista. Wani salo ma da ya fito a karon farko a siyasance shi ne waɗanda suka shiga jam'iyyar sun tarar da jagoranci a jam'iyyar ADC amma kuma jjagororin suka amince su sauka a yi sabon fasali domin damawa da kowane ɓangare.

Saɓanin a haɗakar da aka yi da ta haifar da jam'iyyar APC, inda ƴan siyasar suka narkar da jam'iyyunsu suka kafa wata sabuwar jam'iyya." In ji Malam Kabiru Sufi.

Malam Kabiru Sufi ya ƙara da cewa wani banbancin da ke tsakanin haɗakar guda biyu shi ne yadda wasu jam'iyyu ke yin barazana ga ƴaƴansu da har yanzu ba su ayyana fitarsu daga jam'yyun ba amma kuma ana ganin su a tarukan hadaƙar ta ADC.

Shammatar jam'iyya mai mulki

Kasancewar jam'iyyun hamayya a Najeriya sun ta yin zargin jam'iyya mai mulki ta APC da kitsa da rura wutar rikici a cikinsu domin ka da su samu kwanciyar hankalin da za su ƙalubalance ta, ya sa ƴan hamayya su fito da wani salo na kawar da hankalin waɗanda suke zargi da ƙoƙarin yi musu ƙafar ungulu.

Da farko dai ƴan hamayyar da dama sun koma jam'iyyar SDP, inda aka yi tunanin can za su koma, kafin daga bisani suka kafa jam'iyya mai suna ADA wadda suka nemi hukumar zaɓe ta yi musu rijista.

To amma ƙasa da makonni biyu da miƙa buƙatar neman rijistar sai kawai aka ji sun bayyana dunƙulewarsu a jam'iyyar ADC, wadda masana ke ganin sun shammaci jam'iyya mai mulki.

Fitattun fuskoki a ADC

ADC

Asalin hoton, Atiku/X

Kusan idan ka cire mutanen irin su Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi da Nasiru El - Rufai da Rauf Aregbesola waɗanda suka shiga haɗakar APC, masana na ganin sabuwar haɗakar na ƙunshe da sabbin fuskokin da ba a taɓa tunanin za su iya barin jam'iyyunsu na asali ba.

Mutane irin su Sule Lamiɗo da Aminu Wali da Peter Obi da David Mark wanda shi ne shugaban haɗakar duk sun kasance a cikin haɗakar duk da dai wasunsu ba su fito fili sun ayyana ficewarsu daga jam'iyyun nasu na asali ba.

Ga jerin fuskokin wasu daga ciki:

  • Atiku Abubakar
  • Peter Obi
  • David Mark
  • Nasir El-Rufai
  • Rauf Aregbesola
  • Sule Lamido
  • Aminu Tambuwal
  • Babangida Aliyu
  • Sam Egwu
  • Liyel Imoke
  • Emeke Ihedioha
  • Abubakar Malami
  • Ambassador Aminu Wali
Shawarar masana
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Malam Kabiru Sufi ya fitar da wasu shawarwari guda biyu da ya ce idan sabuwar haɗakar ta ADC ta bi za ta iya kai wa ga gaci.

Yiwuwar kitso da kwarkwata: Malam Kabiru Sufi ya ce dole ne ƴan jam'iyyar ta ADC su lura da yiwuwar yin kitso da kwarkwata musamman bisa zarge-zargen da ake yi wa jam'iyya mai mulki na haifar da ruɗani a tsakanin jam'iyyun hamayya.

"Duba da hasashen da wasu ke yi shi ne akwai yiwuwar wasu da suka taho daga jam'iyya mai mulki ko kuma ma ba daga jam'iyya mai mulkin ba za ta iya yiwuwa jam'iyyar mai mulki ta aika su domin haifar da tarzoma." In ji Sufi.

Tafiya da sabbin fuskoki: Malam Kabiru Sufi ya ce idan dai har wannan haɗaka ta ƴan hamayya na son samun nasara to dole ne su tabbatar da shigar da matasa da sabbin fuskoki cikin tafiyar. Hakan zai goge sukar haɗakar da ake yi cewar ba za ta sauya zani ba.

Fito da sabbin tsare-tsare: Ya kamata haɗakar su bujuro da wasu sabbin tsare-tsare na samar da sauyi domin tabbatar wa da al'umma cewa za ta sauya zani.