Me gargaɗin ADC kan masu shiga cikinta domin takarar shugaban ƙasa ke nufi?

David Mark

Asalin hoton, Social Media/David Mark

Lokacin karatu: Minti 5

Jam'iyyar haɗaka ta ADC ta fito ƙarara ta gargadi wasu ƴaƴan jam'iyyar game da bayyana sha'awarsu ta tsayawa takarar shugaban ƙasa tun yanzu, tana mai cewa babu wanda za su fifita.

Shugaban jam'iyyar David Mark, na wannan magana ne bayan wasu da ake ganin za su nemi takara a jam'iyyar kamar Peter Obi da Rotimi Amaechi da wasu na hannun daman Atiku Abubakar, suka nuna cewa za su tsaya takara a zaɓe mai zuwa.

Bayanai sun nuna cewa wasu daga cikin ƴan tafiyar ta ADC na gunaguni ta ƙarƙashin ƙasa ta yadda tuni wasu jagororin tafiyar suka nuna kwaɗayinsu a fili na neman shugabancin ƙasar, saboda a cewarsu hakan ya yi wuri, kamata ya yi a tsaya a gina tafiyar ta yi ƙarfi tukuna kafin a fara wannan batu.

Haka kuma ana ganin wannan ne yasa shugaban jami'yyar ADC ta ƙasa kuma tsohon shugaban Majalisar dattawa Sanata David Mark ya fitar da sanarwa inda ya ke jan hankalin ƴaƴan jam'iyyar akan haka tare kuma da bayyana cewa ba za su fifita kowane daga cikinsu ba.

Wani abu kuma kuma da ke jan hankali a daidai wannan lokaci a jam'iyyarta ADC shi ne yadda wasu da ke nuna alaƙarsu da ita ke cewa, za su yi angulu da kan zabo wato za su kasance tare da ADC da kuma jam'iyyunsu na ainihi da suke ciki.

Me jiga-jigan ADC ke cewa?

Dr Umar Ardo ɗaya daga cikin jiga-jigan ƴan siyasar hammaya da suka samar da wannan haɗaka ya shaidawa BBC cewa abinda ya kamata masu wannan ra'ayi su mai da hankali a kai shi ne yadda za su fidda ƙasa daga cikin ƙunci:

''Ya kamata duk wani wanda ya ɗauki ra'ayi a kan cewa Najeriya na cikin ƙunci kuma gwamatin da take ciki yanzu ba ta nuna alamun za ta fidda ƙasar daga cikin wannan kuncin ba, ya kamata a tsaya tabbatar da cewa abinda mu ke nema shi ne mu fitar da ƙasar nan daga cikin ƙunci''

''Don haka dukkanmu mu ajiye duk wani buri ko buƙata na tsayawa zaɓe a yanzu. Sannan siyasa ta na yadda ta ke fitar da wanda ya cancanta, don haka a cikin dukkanmu nan duk wanda siyasar ta fitar a kan shi ya fi cancanta, sai a haɗe a bi shi'' in ji shi.

Haka zalika Dr Umar Ardo ya ƙara da cewa tun daga matakin da suke ci gaba da ɗauka a yanzu ba su da wata fargabar cewa kwaliya za ta biya kuɗin sabulu a wannan sabuwar haɗaka ba:

''Alummar ƙasa suna cikin matsala, za su san inda ya kamata kuma duk inda alumma suka nuna , to ta nan za mu bada goyon baya '' in ji shi.

Me ke haifar da rububin takarar shugaban kasa a ADC

Atiku, Obi, Amaechi
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Yakubu Haruna Já'e wanda shi ne shugaban sashen nazarin kimiyar siyasa na jam'iar jihar Kaduna ya ce waɗanda suka nuna wannan sha'awa ta tsayawa takara kowannensu na da wannan buƙata shi yasa suka haɗe a jam'iyyar:

''Dama inda ka kalli abun za ka fahimci cewa kowane daga cikinsu yana da buƙatar ya tsaya takara shi yasa aka haɗe ita jam'iyyar amma suna nuna cewa sun fake ne da ƙoƙarin yadda za a yi su ƙwatar wa ƙasa da ƴancinta daga hannun wannan gwamnatin da su ke ganin tana gallazawa alumma.

"Kuma lokaci ya yi da za su fara tsare-tsaren su saboda idan suka yi jinkiri rigima za ta ɓarke mu su ta cikin gida''

Masanin ya jadada buƙatar ganin cewa jam'iyyar ta bi ƙa'ida wajen fitar da waɗanda suka cancanta:

Su sakar ma kowa ƴanci, ya yi abinda ya kamata na wajan neman takara kuma abi abin da jam'iyya ta tsara domin idan suka koma suna bada tikiti inda ake hana kowa takara, na bar wa wane ko kuma a rubuta a ce su wane da wane za su tsaya takara to ita ma za ta ɓarke kamar irin waɗancan''.

''Akwai yiwuwar sabuwar jam'iyya za ta iya bada mamaki matuka, saboda mafiya waɗanda aka fusata su a jamiyya mai mulki da kuma jam'iyya hammaya su ne suka fito su ka haɗe'' in ji shi.

Sai dai wasu sun nuna damuwa game da ci gaban dunƙulewar wannan haɗaka a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya saboda kusan dukannin jagororinta da wasu ke ganin cewa ba lallai waɗanda za su rasa tikitin takarar shugaban ƙasa su ci gaba da ba ta haɗin kai ba ne.

Me ke kawo barazanar rushewar jam'iyya?

Masana dai na cewa wannan sabuwar jam'iyyar za ta iya bada mamaki, amma fa sai idan an guji batun hana kowa takara, a ce wai mutum guda za a bai wa tikiti.

Sunan ganin kada a kawo batun mubaya'a kowa ya fito ya gwada sa'arsa sannan mai rabo a mara masa baya.

Kwararru na cewa a galibin lokuta ana amfani da karfi a ce dole a bi mutum guda, kuma hakan ke tarwatsa jam'iyya ko haifar da rabuwar kawuna.

Sannan sun nuna cewa siyasar Najeriya a kullum sabon salo take ɗauka kamar abin da ake gani a yanzu na raba kafa ko Anti-party da 'yansiyasar ƙasar suka ƙirƙira a kwanan nan.

'Raba kafa da siyasar aƙida'

A baya da wuya a ga mutum ya fito yana cewa zai yi anti-party ko yana yaƙar jam'iyyar da ya ke ciki ganin cewa akwai dokoki da ikon korar mutumin da aka samu da wannan dabi'a.

Amma a yanzu tun bayan da ministan Abuja, Nyesom Wike ya gwada hakan har ake ganin ya yi nasara, to ana iya cewa kowa na neman rungumar wannan sabon salo.

Farfesa Abubakar Kari da ke nazartar harkokin siyasa a Najeriya ya ce wannan salo mugunyar al'ada ce da ba za ta haifar da alheri ga waɗannan jam'iyyu ba.

Ya ce rashin ɗaukan mataki da ingiza mai kantu ko ziga daga jam'iyyar mai mulki ke ruguza komai.

"Babu kunya babu tsoron Allah jam'iyya mai mulki na taka rawa a rigingimun da 'yan adawa ke fama da su, sannan wasu ma daukan nauyinsu ake yi su je su tarwatsa 'yanadawar."

Sai dai a nashi ra'ayin Farfesa Kamilu sani Fagge masanin harkokin siyasa a Najeriya, cewa yake rushewar siyasar aƙida ce matsalar, saboda a baya al'umma kishin ƙasa ake bai wa fifiko, amma a wannan zamanin biyan bukatun kai ya fi karfi.

Ya ce yanzu yanayi ne na kasuwar bukata, mutane na shiga siyasa ba tare da sannin akidarta ko manufofi ba, sannan su kan su jam'iyyu ba su da alkibila sama da batun kama madafun iko.

Don haka dole ne duk wanda ya shiga ya ga bai samu abin da ya ke so ba ko biyan bukata, zaɓin biyu ne, ko ya fita ko ya yi mata anti-party wato raba kafa.

"Idan mutum zai dau jam'iyyar da ta zame masa gata, ta masa riga da wando amma ya fice, ya ci amana saboda rashin wata dama, to ko shaka babu mutane sun san cewa idan sun dora su kan mulki, zai ci amana saboda biyan bukatar kansa.

Bakin masanan dai ya zo ɗaya cewa hannunka baya ruɓewa ka yar, shi ya sa suke cewa dukkanin jam'iyyin kama daga APC da PDP da ma sabuwar haɗaka ta ADC duk kanwar ja ce.