‘ADC ta karɓe tsarin jagorancin PDP a jihohin Yobe, Adamawa da Gombe’

Asalin hoton, XELRUFAI
Bayanai sun ce a yanzu haka jam'iyyar ADC da ƴan haɗaka da wasu jagororin ƴan hamayya suka dunƙule a ƙarƙashin inuwarta ta fara karɓe tsarin jagorancin jam'iyyar PDP a jihohin Yobe da Adamawa da kuma Gombe.
Sun ce an samu ƴan PDP da dama da suka sauya sheƙa zuwa ADC, ciki har da waɗanda suka riƙe manyan muƙamai a baya.
A jihar Adamawa wasu daga cikin ƙusoshin jam'iyyar da suka riƙe mukamai a matakai daban daban na jiha tuni suka sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar ƴan hadaka ta ADC inda kawo yanzu shugabannin jami'yyar PDP a ƙananan hukumomi goma a cikin jihar suka fice daga cikin jam'iyyar.
Hon Umar Jada tsohon mai bai wa gwamnan jihar Adamawa shawara wanda ke cikin waɗanda suka koma jam'iyyar ADC ya shaidawa BBC cewa shugaban ƙaramar hukumar Girei shi ne na baya baya nan da ya sauya sheƙa:
''Na baya baya nan shi ne shugaban ƙaramar hukumar Girei wanda daga kan mataimakin shugaban PDP har zuwa Exco da shugabannin ƙananan hukumomi 10 sun ajiye muƙaminsu a jam'iyyar PDP sun koma jam'iyyar ADC '' in ji shi
A jihar Yobe bayyanai sun ce tuni wasu daga cikin manyan jagoroin jam'iyyar PDP suka yi fatali da ita, suka tsunduma jam'iyyar ta ADC.
Adamu Maina Waziri tsohon jagoran jam'iyyar PDP a jihar ta Yobe na cikin waɗanda suka sauya sheƙa:
''Akwai shugabanni na tsohuwar jam'iyyata ta PDP waɗanda suka sauka da kuma masu ci, da suka zo suka yi musabaha, suka ce sun bar muƙaminsu da jam'iyyar PDP, sun koma ADC''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
''Na tuntuɓi ƙananan hukumomi guda 17 waɗanda sun aiko wakilai, daga kowace ƙaramar hukuma domin halatar tarurukan''
''Ina tabattar ma ka nan da kwanaki kaɗan za mu yi babban taro wanda jiga -jigan wasu jam'iyyun za su zo su bayyana kansu sun dawo ADC'' in ji shi .
Sai dai jam'iyar hammaya ta PDP ta ce ficewar da wasu ƴaƴanta a waɗannan jihohi suka yi bai tayar ma ta hankali ba .
Ibrahim Abdullahi mataimakin mai magana da yawun jam'iyyar PDP ya ce wasu tsirarun mutanen ne ke komawa ADC
''Idan aka samu ƴan tsiraru sun fito sun ce sun tafi, wannan ba abin mamaki ba ne saboda sun ga madugunsu guda ya tafi, kamar a Adamawa ba za ka yi tunanin mutum kamar Atiku a ce ba shi da ƴan muƙarraban da ba su kai sun kawo ba, waɗanda za su bi shi, haka ya ke a Gombe, haka ya ke a Yobe''
''Amma idan ka yi magana a kan Sokoto ko arewa ta tsakiya duk ba bu wanda ya damu da taron nasu, saboda haka ba mu damu ba, ko a jikinmu'' in ji shi.
Wannan dai na zuwa ne yayin da jam'iyyar ADC ta zargi wasu da ke cikin gwamnatin jam'iyyar APC mai mulki da yunƙurin tarwatsa shirinsu na hamaya da suke yi .
Hakan dai na cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar Bolaji Abdullahi ya fitar yana mai bayyana cewa an gayyaci tsoffin shugabbanin jam'iyyar ADC na jihohi da manyan ƙusoshin kwamitin zartarwar na jihohin arewa maso gabashi da kuma arewa maso yamma don yin wata ganawa ta sirri da manyan jami'an gwamnatin tarayya.
Kawo yanzu dai jam'iyyar APC mai mulki ba ta ce komai ba kan wannan zargin ba.












