KAI TSAYE, Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 06/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 6 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Abdullahi Bello Diginza

  1. Ƙasashen tekun Fasha sun ce sun daƙile hare-haren sama daga Iran

    Ƙasashen yankin tekun Fasha sun ce, sun dakile hare-hare ta sama da Iran ke kai musu.

    Qatar ta ce ta dakile wani harin jirgin sama maras matuki da aka nufa kan sansanin sojin sama na Al Udeid - wanda shi ne mafi girma na sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

    Saudiyya ma ta ce, ta kakkabo tare da lalata makamai masu linzami guda uku, da aka hari sansanin sojin sama na Yarima Sultan, wanda shi ma, sojin Amurka ke wajen.

    Haka ita ma Bahrain, ta ce ta tare makamai masu linzami uku.

  2. 'Iran ta kasance ba ta da intanet na kwanaki shida'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar Iran ta kasance ba ta da intanet na tsawon kwanaki shida, in ji ƙungiyar masu sa ido kan intanet ta NetBlocks.

    Ƙungiyar ta ce ƙasar tana da “ kaso 1 da haɗin intanet a sa’o’i 144 da suka wuce.”

    Katsewar intanet yana daga cikin abubuwan da ke sanya wahalar rahoton labarai daga ƙasashen waje kan abin da ke faruwa a ciki Iran.

    Haka kuma, gwamnatin Iran ta rufe ayyukan intanet a baya yayin zanga-zangar adawa da gwamnati a farkon wannan shekara.

  3. Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana aiki domin kakkaɓo makaman Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce tana aiki don kakkaɓo sababbin makamai da Iran za ta harba zuwa ƙasar

    “A ɗan lokaci da ya gabata, IDF ta gano wasu makamai da aka harba daga Iran zuwa cikin ƙasar Isra'ila” in ji ta a cikin wani sanarwa da ta wallafa a shafin Telegram.

    An kuma aika wa mutanen kasar “gargadi da umarnin kiyaye kai” ta wayoyin salula“

    An gargadi wadanda suka samu wannan sakon su shiga wani wuri mai tsaro su tsaya har sai an ba da ƙarin sanarwa.

  4. An kama mutum huɗu a Landan kan zargin taimakawa Iran

    ’Yan sanda a Landan sun kama mutum huɗu a wani binciken yaki da ta’addanci da ake yi wanda ke da alaƙa da Iran, a cewar rundunar ’yan sandan Metropolitan .

    ’Yan sandan sun kama wani ɗan Iran da kuma wasu uku masu waɗanda suke da shedar yan kasar Birtaniya da Iran a lokaci guda, bisa zargin taimakawa wata hukumar leƙen asirin Iran.

    Rundunar ta ce binciken ya shafi zargin sa ido da aka yi kan wasu wurare da kuma mutane da ke da alaƙa da al’ummar Yahudawa a Landan.

    Har yanzu ana ci gaba da bincike a yankunan Watford, Barnet, da kuma wani adireshi a Wembley.

  5. China na tattaunawa da Iran kan wucewar tankokin man Qatar cikin aminci

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    China na cikin tattaunawa da Iran domin ba da damar jiragen da ke ɗauke da mai da iskar gas na Qatar su wuce cikin aminci ta mashigar Hormuz, kamar yadda rahoton Reuters ya nuna, bisa ga wasu majiyoyi da ba a ambata sunayensu ba.

    A yayin da aka shiga rana ta bakwai na yakin da ke tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka, dubban jiragen ruwa sun tsaya cak a kusa da wannan muhimmiyar hanya, wacce ke ɗaukar kusan kashi ɗaya cikin biyar na mai da iskar gas na duniya.

    Biyo bayan wannan sabon rikici a Gabas ta Tsakiya, farashin makamashi ya tashi.

    Rahotannin Reuters da Bloomberg sun nuna cewa wani jirgin mai da ake tsammanin na China ne ya wuce ta tekun a ranar Alhamis, duk da cewa BBC ba ta samu tabbatarwa ba tukuna.

    China na ɗaya daga cikin manyan masu sayen mai na Iran kuma ta bayyana rashin amincewa da hare-haren IIsra'ila da Amurka ke kai wa kan Iran.

  6. Majalisa ta gayyaci Kyari kan zargin ɓatan maƙudan kuɗi a NNPCL

    Tsohon shugabna NNPCL

    Asalin hoton, MELEKYARI/NNPC

    Kwamitin kula da asusun gwamnati na Majalisar Dattawan Najeriya ya gayyaci tsohon shugaban Kamfanin Man Fetur na ƙasar, Mele Kyari, domin ya yi bayani kan zargin wasu kuɗaɗe da yawansu ya kai naira tiriliyan 210 da ake cewa ba a yi cikakken bayanin yadda aka kashe su ba tsakanin shekarun 2017 zuwa 2023, lokacin da yake jagorantar kamfanin.

    An gayyaci Kyari tare da tsohon babban jami’in kula da harkokin kuɗi na kamfanin, Umar Ajia Isa, da kuma tsohon babban manajan kula da harkokin zuba jari na kamfanin, Bala Wunti.

    Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada, ne ya bayar da umarnin gayyatar a ranar Alhamis bayan da kwamitin ya duba rahotannin binciken kuɗi da suka shafi kamfanin NNPCL.

    Kwamitin ya kuma yi gargaɗin cewa zai iya fitar da sammacin kama waɗanda abin ya shafa idan suka gaza bayyana a gaban kwamitin a ranar da za a sanar nan gaba.

    Sanata Wadada ya bayyana wannan matsaya ta kwamitin ne yayin da yake yi wa manema labarai ƙarin bayani bayan kammala taron kwamitin.

    A cewarsa, ana sa ran tsoffin shugabannin kamfanin za su bayyana tare da shugabancin kamfanin na yanzu ƙarƙashin jagorancin sabon Babban Darakta, Bayo Ojulari, da kuma masu binciken kuɗi na waje da suka yi aiki da kamfanin a lokacin da ake magana a kai.

  7. Ukraine ta ce Amurka ta nemi taimakonta wajen kawar da harin da ake kai wa yankin Gabas

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya ce Amurka ta buƙaci ƙasarsa ta taimaka wajen kawar da hare-haren da ake kai wa yankin Gabas ta Tsakiya da jirage marasa matuƙa samfurin Shahed, ƙirar Iran.

    Ukraine na ƙera na’urori masu araha kuma masu tasiri sosai wajen kakkabo jiragen sama marasa matuƙa na kai hari, a ƙoƙarin da take na kare kanta daga ruwan bama-bamai da Russia ke yi mata.

    Wannan fasaha da ƙwarewar amfani da ita za su kasance masu amfani sosai ga ƙasashe wajen kare kansu daga hare-haren da Iran ke kaiwa a halin yanzu.

    Zelensky ya yi wa kawayen Amurka a Gabas ta Tsakiya tayin musayar na’urorin, inda shi kuma yake so su ba shi wasu daga cikin na’urorinsu na garkuwar hare-hare ta sama, waɗanda Ukraine ke buƙata.

  8. Yaƙin Iran: Amurka ta sassauta takunkumi kan man Rasha

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta sassauta takunkumin da ta sanya a kan man Rasha, bayan da farashin mai ya tashi saboda yakin na Iran.

    Ta ce za ta bar India ta rika sayen man na Rasha, amma wanda daman tuni yana jiragen ruwan dakon mai da ke teku.

    Ko wannan zai haifar da wani sauyi, wani abu ne na daban. Sakataren baitul-malin Amurkar, Scott Bessent, ya ce an yi hakan ne domin bayar da damar ci gaba da kai mai kasuwannin duniya.

    Ya kuma ce yana fatan Indiya za ta kara yawan man da take saya daga Amurka.

    Barazanar da Iran ta yi, ta kai hari kan jiragen ruwa da ke bi ta Zirin Hormuz, ta sa jirage daina bin yankin, inda ta nan ne ake safarar kashi daya bisa biyar na man duniya.

  9. Amurka da Isra'ila sun ce suna shirin shiga sabon mataki a yaƙin Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka da Isra'ila sun ce suna shirin shiga sabon mataki na gaba a yakin da suke yi da Iran

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce, suna dab da kara karfin hare-haren da suke kai wa Iran din sosai.

    Rundunar sojin Isra'ila kuma ta ce, ta fara, kai abin da ta kira manyan hare-hare a kan cibiyoyi da kayayyaki a Tehran, babban birnin Iran din.

    Shugaban babbar rundunar sojin Amurka, ya ce an kassara duk wani karfi na amfani da kai hari da makamai masu linzami na Iran, na yanzu da kuma na nan gaba.

    Admiral Brad Cooper ya kuma ce Amurka ta nutsar da jiragen sojin ruwa na Iran sama da talatin.

  10. Saudiyya ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da aka harba cikin dare

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar tsaron ƙasar Saudiyya ta ce dakarunta sun kakkaɓo wasu jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami da aka kai harba zuwa ƙasar cikin dare.

    A cikin wasu saƙonni da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X ta bayyana cewa an gano wani makami mai linzami wanda daga bisani aka kakkabo shi tare da lalata shi a kusa da birnin Al-Kharj, da ke kudu maso gabashin babban birnin ƙasar Riyadh.

    Ma’aikatar ta ƙara da cewa a cikin sa’a ta ƙarshe ma an sake kakkabo wasu jirage marasa matuƙa da dama a kusa da birnin Riyadh.

    Jami’an tsaro kasar sun ce dakarun ƙasar na aiki don dakile duk wata barazana da ka iya shigowa cikin ƙasar.

    Ba a bayar da rahoton jikkata ko asarar rayuka ba zuwa yanzu.

  11. Wane ne Mojtaba Khamenei, wanda ake hasashen zai zama jagoran addinin Iran?

    .....

    Asalin hoton, Tasnim News Agency

    Bayan kashe jagoran addinin Iran, Ali Khamenei a hare-haren Amurka da Isra'ila a Iran, sai aka fara tunanin ko ɗan marigayin Mojtaba wanda shi ma yake da ƙarfin faɗa a ji ya rasu.

    Sai da aka yi kwanaki ba a ji ɗuriyarsa ba, kuma babu tabbaci. Sai a ranar Talata 3 ga watan Maris ne kafofin watsa labarai suka tabbatar da cewa Mojtaba yana raye, kuma yana cikin ƙoshin lafiya. Sai dai har yanzu bai fito ba.

    Yanzu yana cikin na gaba-gaba a cikin waɗanda ake hasashen za su iya maye gurbin jagoran addinin ƙasar, kamar yadda kafar Reuters ta ruwaito daga wasu majiyoyi guda biyu a Iran.

  12. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.