Me ya sa wasu ƴan jam'iyyar PDP ke raba ƙafa?

Sule Lamido, da Atiku Abubakar, da Nyesom Wike, da Aminu Tambuwal

Asalin hoton, Social Media

Lokacin karatu: Minti 3

Wani sabon salon hamayya da masu bibiyar harkokin siyasa a Najeriya suka fara gani shi ne na yadda wasu jiga-jigai a manyan jam'iyyun adawa suka ayyana goyon bayan jam'iyyu biyu.

Matakin nasu ya samo asali ne bayan wasu manyan 'yansiyasa sun dunƙule a jam'iyyar ADC domin ƙalubalantar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta APC, wadda ta fara mulki tun 2015.

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido na cikin jagorori a babbar jam'iyyar adawa ta PDP da suka bayyana cewa za su bai wa hadakar 'yan hamayya ta ADC cikakken goyon baya da zimmar kawar da APC a babban zaɓe na 2027.

"PDP ɗin nan tsatsona ce, gadona ce a siyasance, saboda haka idan na fita saboda wani yaro mai suna Wike, to wa zan bar wa?" in ji shi cikin wata hira da BBC.

Sule Lamido ya ce zai yi hakan ne domin koyi da Ministan Abuja Nyesom Wike, wanda ɗan PDP ne amma kuma yake yi wa APC aiki tun daga zaɓen 2023.

"Saboda haka muna nan a PDP amma kuma muna neman ko dai a gyara ta ko kuma, kamar yadda Wike ke ɗibar wani ɓangarenta ya kai wa Tinubu, mu ma za mu ɗebi wani ɓangarenta mu kai jam'iyyar haɗaka."

"Kwanan nan tsohon Gwamnan Binuwai Samuel Ortom da wani suka je wajen Shugaba Tinubu suka faɗa masa cewa muna PDP amma muna tare da kai, sai mun karya ta [PDP]," kamar yadda ya bayyana.

A makon da ya gabata ne 'yan'adawar suka bayyana dunƙulewa a jam'iyyar ADC, inda suka naɗa tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark (daga PDP) a matsayin shugaba na riƙo, da kuma Rauf Aregbesola (daga APC) a matsayin sakatare na riƙo.

Tsohon gwamnan na Jigawa ya ce akwai "rainin hankali" dangane da yadda ake tafiyar da harkokin siyasa da abin da Wike yake yi a PDP.

Sule Lamiɗo ya nuna cewa halin da Najeriya ke ciki a yanzu ba lokaci ne na nuna ɓangaranci ba, "lokaci ne na duba wane ne ya cancanta a mara masa baya ba tare da la'akari da jam'iyya ba".

Tsohon gwamnan na Jigawa daɗaɗɗen ɗansiyasa ne kuma ya sha yin alfahari a baya cewa bai taɓa fita daga jam'iyyar PDP ba tun da aka kafa ta a shekarar 1998.

Sauran ƴan'adawa da ke raba ƙafa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Nyesom Wike ya fara rigima da shugabancin PDP ne tun bayan zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar domin neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, wanda Atiku Abubakar ya doke shi tare da sauran 'yantakara.

Tun daga lokacin ne kuma Wike ya haɗa kai da Bola Tinubu, wanda ya yi wa APC takara, kuma ya bai wa Wike muƙamin minista bayan samun nasara.

A wata ziyara da ya kai jihar Rivers cikin shekarar 2023 Tinubu ya ce: "Nyesom, ina gode maka saboda gudumawar da ka bayar wajen nasarar da na samu. Ba zan samu hakan ba in ban da irin taimakon da ka bayar."

Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar na cikin manyan 'yan'adawar da suka dunƙule a ADC, duk kuwa da cewa bai riga ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar ba.

Shi ma tsohon gwamnan Sokoto kuma sanata a yanzu, Aminu Waziri Tambuwal, ya jaddada cewa zai ci gaba da riƙe katinsa na jam'iyyar PDP ɗin yayin da zai yi aiki a ADC.

Kamar Lamido, shi ma Tambuwal ya ce "salon siyasar Wike" ne ya sanya shi ɗaukar matakin.

A gefe guda kuma, ɗantakarar jam'iyyar Labour Party (LP) a 2023 Peter Obi, wanda ke cikin jam'iyyar haɗakar, ya ce har yanzu mamba ne shi a jam'iyyar tasu.

Ita ma LP ta daɗe tana fama da rikicin shugabanci, rikicin da ya raba jam'iyyar gida biyu wanda kuma har zuwa yanzu ba a kawo ƙarshensa ba.