Yadda 'yanbindiga suka kashe masallata 28 a jihar Katsina

Asalin hoton, Getty Imaages
Bayanai na ƙara fitowa game da harin 'yanfashin daji da ya kashe kusan mutum 30 a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya yayin da suke tsaka da sallah a wani masallaci.
Wasu mazauna yankin Gidan Mantau na ƙaramar hukumar Malumfashi sun shaida wa BBC Hausa cewa lamarin ya faru ne da asubahin ranar Litinin, inda tuni aka yi jana'izar mutum 28.
"Muna tsaka da sallah suka buɗe mana wuta, mutum 28 muka yi wa jana'iza ciki har da mahaifina," in ji wani mutum da muka ɓoye sunansa cikin kuka da share hawaye.
"A gida suka ritsa shi [mahaifin], suka kulle shi a ɗaki, suka zuba fetur kuma suka kunna wuta."
Wani mutumin daban ya ce maharan sun ƙona mata da ƙananan yara a cikin gidaje "tare da sace kusan mutum 100".
Sai dai rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar ta ce mutum 15 aka kashe a harin.
"Bayan mutum 15 da suka mutu akwai kuma bakwai da suka ji rauni, sannan sun kunna wa wasu gidaje wuta," kamar yadda kakakin rundunar DSP Abubakar Sadik ya shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba su kama kowa ba amma matakan da suka ɗauka "sun kawo natsuwa a yankin".
"Muna ci gaba da gudanar da bincike domin kama waɗanda suka aikata wannan aika-aika, amma zuwa yanzu ba mu yi nasarar kama kowa ba."
Mazaunin yankin ya ce mutum biyar ne suke kwance a asibiti zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
"Ya ake so mu yi da rayuwarmu ne wai? Ɓarayin nan an san su, an kuma san inda suke, kuma ba fasa aikinsu suke yi ba," kamar yada wani mazaunin yankin ya koka.
A ranar Alhamis da ta gabata ma rahotonni sun ce wasu 'yanfashi sun kashe wani jami'in ƙaramar hukumar ta Malumfashi a gonarsa, kuma suka sace tsohon kansila.
Baya ga kisan, 'yanbindigar sun kuma far wa garuruwan Gidan Boro da Tuge, da Dayi da misalin ƙarfe 8:00 na yamma.













