Wane ne ɗan tsohon shugaban Boko Haram da aka kama a Chadi?

Wani mutum zaune riƙe da takarda mai ɗauke da sunansa

Asalin hoton, Zagazola Makama/X

Lokacin karatu: Minti 3

Bayanai na ci gaba da fitowa kan kamun da jami'an tsaron Chadi suka yi wa Muslim Muhammad Yusuf, ƙaramin ɗan marigayi tsohon shugaban ƙungiyar Jama'atu Ahlis-Sunna Lidda'Awati Wal-Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram a Najeriya

An kama Muslim Yusuf ne tare da wasu mutum huɗu da ake zargi da kasancewa mambobin ƙungiyar, a cewar Zagazola Makama, wani mai bincike kan ayyukan ƙungiyar Boko Haram a Tafkin Chadi.

Makama ya ce hukumomin Chadi sun kama Muslim Mohammed Yusuf, ba tare da sanin ainihin wane ne shi ba, har sai da hukumomin leƙen asirin Najeriya suka sanar da su ta hanyar rundunar haɗin gwiwar ƙasashen Tafkin Chadi da ke yaƙi da Boko Haram, (MNJTF).

Bayanai na cewa Muslim - wanda ƙani ne ga shugaban ƙungiyar ISWAP, Habib Yusuf da aka fi sani da Abu Mus'ab Al-Barnawi - ya kasance wanda ke jagorantar mayaƙa masu iƙirarin jihadi a Chadi da suka ɗauki lokaci suna kai hare-hare a ƙasar.

An dai cafke mayaƙan a lokacin wani samamen da jami'an tsaron Chadi suka ƙaddamar.

'Yana ƙarami lokacin da Boko Haram ke ganiyarta'

Bayanai sun nuna cewa Muslim Mohammed Yusuf na yaro ƙarami a lokacin da jami'an tsaron Najeriya suka halaka mahaifinsa, bayan sun kama shi a maɓoyarsa.

Barista Audu Bulama Bukarti, mai bincike kan harkokin tsaro a ƙasashen Afirka ya ce lokacin da Boko Haram ke tashe, Muslim yaro ne ƙarami da bai san komai ba.

Ya ƙara da cewa sunan nasa ba sanannen suna ba ne, kodayake hakan ba ya rasa nasaba da amfani da sunan da ba na ainihi ba, a cewar Bukarti.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Idan ka kula sunan da aka kama shi yanzu, suna ne da ya yi kama da na mutanen Chadi, kuma babu mamaki ya yi hakan ne domin ya yi ɓad-da-bami'', in ji shi.

Masanin tsaron ya ci gaba da cewa hakan ya sa sunansa bai yi fice a tafiyar ƙungiyar Boko Haram ba.

''A lokacin da Boko Haram ta fara yaƙi a 2009 akwai wani bidiyon Mohammed Yusuf da ya ɓulla tare da wani yaro da bai wuce shekara biyar ba - da a ciki aka ji shi yana huɗuba da Larabci yana kafirta mutane - to babu mamaki wannan yaron ne'', in ji Bukarti.

Bukarti ya ce Mohammed Yusuf yana da ƴaƴa masu yawa, kuma da dama cikinsu mazaje ne.

"Kuma da dama cikin ƴaƴansa musamman manyan irinsu Habib da ake wa laƙabi da Abu Mus'ab Al-Barnawi sun taka muhimmiyar rawa a ayyukan ƙungiyar Boko Haram''.

Abu Mus'ab Al-Barnawi ya samu saɓanin aƙida da tsohon shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau har ma ya ɓalle daga ƙungiyar tare da yin mubaya'a ga ƙungiyar IS.

Bayan mubaya'ar tasa ne aka ba shi jagorancin reshen ƙungiyar a yankin Afirka ta Yamma da ake yi wa laƙabi da ISWAP.

Wace rawa Muslim ke taka wa a ISWAP?

Wasu mayaƙa cikin motar akori kura

Asalin hoton, AFP

Barista Audu Bulama Bukarti ya ce bayanai sun nuna cewa Muslim Muhammad Yusuf shi ne shugaban ƙungiyar ISWAP a ƙasar Chadi.

Masanin tsaron ya ce kodayake sunansa bai yi fice ba, amma kasancewarsa jagoran ISWAP a Chadi, to za a iya cewa yana da hannu a hare-haren da ƙungiyar ke kaiwa a ƙasar.

Me kama shi ke nufi ga yaƙi da ISWAP?

Barista Bukarti ya ce kama Muslim babbar nasara ce ga dakarun ƙasashen yankin Tafkin Chadi da ke yaƙi da ƙungiyoyin ISWAP da Boko Haram.

Ya kuma ce hakan ya nuna cewa jami'an tsaron Najeriya da Chadi sun fara amfani da dabarun tattara bayanan sirri.

''Idan ka kula tun da aka fara ƙungiyar Boko Haram baya da Muhammad Yusuf ba a taɓa kama wani fitaccen jagoranta da ransa ba''.

''To ka ga yau idan aka ce an kama ɗan gidan Muhammad Yusuf da ransa kuma a Najeriya an kama shugabannin ƙungiyar Ansaru guda biyu a ƴan kwanakin nan to za ka yaba wa jami'an tsaron tare da yarda cewa sun fara amfani da bayanan sirri'', in ji Bukarti.

Haka kuma masanin tsaron ya ce kama Muslim zai sanyaya wa mambobin ƙungiyar gwiwa.

''Idan suka ga an kama ɗaya daga cikin manyan jagororinta to za su iya razana, kuma tsoro zai shiga ransu, za su riƙa kaffa-kaffa kada a kama su domin ba su san irin bayanan da za a samu a kansu ba'', in ji masanin tsaron.

Ya ƙara da cewa kamun nasa kuma zai iya gurgunta ƙungiyar koda kuwa na ɗan lokaci ne.

''Domin akan samu rigingimun shugabanci idan aka kama ko kashe ɗaya daga cikin jagororin, kuma a wasu lokutan hakan zai sa wasu su ɓalle, abin da zai sa ƙungiyar ta rasa alƙibla'', in ji shi.

Dr Bukarti ya kuma ce kama shi da aka yi zai sa jami'an tsaro su tatsi bayanai masu muhimmanci game da ƙungiyar da maɓoyar mayaƙanta, da irin shirye-shiryenta.