Yadda ƙananan hukumomin Katsina ke yin sulhu da ƴan bindiga

Asalin hoton, Getty Images
Ƙaramar hukumar Safana a jihar Katsina ta shiga jerin ƙananan hukumomin da suka amince su yi sulhu da 'yan bindiga, domin kawo ƙarshen tashin hankali a yankin.
Wannan mataki ya biyo bayan irin yarjejeniyar da hukumomin Jibiya da Batsari da Dan Musa suka ƙulla a baya, wacce ta kawo raguwar hare-hare da tsaro ga mazauna yankunan.
Yarjejeniyar ta ba da damar manoma su koma gonakinsu cikin kwanciyar hankali, 'yan kasuwa su yi kai kayayyakinsu zuwa kasuwanni, da kuma bai wa 'yan bindiga damar zuwa asibitoci da kasuwanni da yin zirga-zirga ba tare da tsangwama ba.
Shugaban ƙaramar hukumar Safana, Abdullahi Sani Safana, ya bayyana cewa ba 'yan bindigan da kansu ne suka nemi a yi sulhu.
Ya ce hakan ya faru ne saboda nasarar da aka gani a hukumomin da suka riga suka shiga wannan tsarin.
"Mun kafa ƙa'idoji a tsakanimu, inda muka amince cewa za su daina kai hare-hare a duk fadin ƙaramar hukumar Safana, kuma su sako duk mutanen da ke hannunsu."
"Ƴan bindigar kuma sun nemi mu gyara musu madatsun ruwa da dam-dam domin shayar da dabbobinsu, tare da gyaran asibitoci da makarantu da islamiyyoyi domin koyar da 'ya'yansu ilimin zamani da na addini," in ji shi.
Abdullahi ya ce sakamakon wannan mataki da ya ƙarfafa gwiwar 'yan bindigan,sun buƙaci ƙananan hukumomin Kurfi da Dutsinma su shiga cikin yarjejeniyar, kuma ya ce yana da yaƙinin cewa nan ba da jimawa ba za su amince.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar wani mazaunin garin Safana, Iliyasu Sani, al'umma na amfana sosai daga wannan sulhu.
"Yanzu muna fita kasuwa cikin natsuwa, muna noma ba tare da tsoro ba, harkokin yau da kullum suna tafiya yadda ya kamata. Idan na kwatanta da shekaru uku da suka gabata, yanzu zaman lafiya ya dawo," in ji shi.
Masani kan harkokin tsaro, Dr Kabiru Adamu, ya bayyana cewa matsin rayuwa da rashin tsaro ne suka tilasta wa al'umma neman mafita da kansu.
"Jama'a sun gaji da halin da ake ciki, kuma hukuma ba ta kare su yadda ya kamata. Duk da cewa gwamnatin Katsina ta sha nanata cewa ba za ta nemi sulhu da 'yan bindiga ba, ta bayyana cewa idan 'yan bindigan suka nemi sulhu tare da ajiye makamai, ba za ta hana ba," in ji shi.
Dr Kabiru ya ƙara da cewa, idan aka tabbatar da bin ka'idoji da tsayawa a kan alƙawura, wannan sulhu na iya zama matakin farko na wanzar da zaman lafiya na dindindin a yankin.
Masanin ya ƙara da cewa wannan sulhun da Safana ta shiga na iya zama wani sabon babi na farfaɗo da rayuwar al'umma a yankin, inda manoma, 'yan kasuwa da talakawa za su koma harkokinsu cikin kwanciyar hankali.
Amma zaman lafiya zai tabbata ne kawai idan an tabbatar da cewa dukkan ɓangarorin sun tsaya tsayin daka kan abin da aka cimma, musamman wajen daina laifuka da tabbatar da tsaro ga kowa da kowa in ji shi.










