Shin 'yan bindiga sun ɓulla jihar Bauchi ne?

Gungun 'yanfashin daji

Asalin hoton, Social Media

Bayanan hoto, Gungun 'yan fashi masu sacewa da garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa sun addabi jihohin arewacin Najeriya da dama
Lokacin karatu: Minti 3

Kisan da 'yan bindiga suka yi wa wasu 'yan banga ko 'yan sa-kai a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ya jawo tambayoyi da kuma damuwa game da yadda ayyukan masu ɗauke da makamai ke faɗaɗa a arewacin ƙasar.

A ranar Litinin da dare ne rundunar yan sanda a jihar ta Bauchi ta tabbatar wa BBC kisan da 'yan bindiga suka yi wa wasu 'yan sintiri sakamakon wani kwanton ɓauna da suka yi wa yan sintirin ranar Asabar a dajin Madam da ke kusa da iyakar Bauchi da jihar Filato.

Artabun ya faru ne a lokacin da jami'an tsaro na sa-kai da ake wa lakabi da "Professional Hunters" suka gamu da 'yan bindigar a ƙauyen Mansur, in ji mai magana da yawun rundunar CSP Ahmed Muhammad Wakili.

Ya ce da ma garin na Mansur mai iyaka da Taraba, da Filato da Gombe wuri ne da ke fama da matsalar ɓarayin daji.

"Sun yi arangama da juna ne a lokacin da yan bangar suke sintiri, a kusa da dajin Badam wanda ya yi iyaka da jihohin Filato, da Gombe, da Bauchi, inda yan bindigar suka yi musu kwanton ɓauna, sannan bangarorin biyu suka far wa juna" a cewar CSP Wakili.

Yayin da 'yan bindigar ke ci gaba da aika-aika a jihohin da ke maƙwabtaka da ita, ana kallon Bauchi a matsayin jihar da babu hare-haren 'yan fashin daji.

A baya, akan samu rikicin ƙabilanci jifa-jifa a jihar ta Bauchi, amma babu rahoton wani babban rikici a jihar a watannin baya-bayan nan.

Mutum nawa aka kashe?

CSP Wakili ya ce ba su kai ga tattara alƙaluman ainihin adadin mutnaen da aka halaka ko suka ji raunuka ba a lokacin da ya yi magana da BBC. Muna ci gaba da nemansa domin jin bayanan da suka tattara.

Sai dai rahotonni sun ce aƙalla mutum 25 ne suka mutu a arangamar.

Jaridar Daily Trust ta ce bayanan da ta tattara sun nuna cewa cikin waɗanda suka mutu akwai 'yan sa-kai tara, da 'yan bindiga biyar, da kuma fararen hula 11 waɗanda 'yan bindigar suka yi garkuwa da su.

"Babu wanda zai iya bayyana anihin adadin mutanen da lamarin ya shafa gaskiya, saboda mutanen da suka rasa ransu fantsama suka yi cikin daji, ɗauke da raunuka a jikinsu," a cewarsa.

"Muna kyautata zaton wasu daga cikinsu ka iya mutuwa, amma mun tura jami'anmu na musamman domin gudanar da binciken."

Zaman lafiya a Bauchi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya ta yi fama da rikice-rikice a baya, ciki har da hare-haren Boko Haram da na ƙabilanci.

Amma ta samu zaman lafiya idan aka kwatanta ta da maƙwabta kamar Filato, da Borno.

Rundunar 'yansanda a Bauchi ta ce ta ce a iya saninsu babu 'yan bindiga a dajin na Badam, inda aka samu arangama a kwanan nan.

"Muna zargin 'yan bidigar sun taso ne daga wani wuri sannan suka yi sansani a yankin. Amma za mu ci gaba da bincike kan lamarin," kamar yadda CSP Wikili ya bayyana.

Rabon da a samu rahoton wani babban hari ko rikici a jihar tun a watan Agustan 2023, lokacin da mazauna garin Gumau da ke ƙaramar hukumar Toro suka ce wani gungun 'yan bindiga na kai hare-hare kan jama'ar wasu kauyuka tare da kashe su da kuma tafiya da dukiyoyinsu.

Jogo Isma'ila Haruna, shi ne ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, ya faɗa wa BBC a lokacin cewa sama da 'yan bindiga 100 ne suka yi sansani a yankin nasu.

A cewarsa, "ana tsammanin har da ''ƴan Boko Haram da masu garkuwa da mutane a cikinsu".