Ƙasashe biyar da Trump zai iya kai wa hari bayan Venezuela

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Tom Bennett
- Lokacin karatu: Minti 4
Babban abin da ke ɗaukar hankali a wa'adin mulkin shugaban Amurka Donald Trump na biyu shi ne muradunsa na harkokin ƙasashen waje.
Ya aiwatar da barazanar da ya yi wa Venezuela ta hanyar kama shugaban ƙasar da matarsa a gidansu da ke Caracas a wani hari da Amurka ta kai ƙasar cikin dare.
Amurka dai ta gabatar da Shugaba Maduro da mai ɗakinsa a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda huɗu masu alaƙa da safar miyagun ƙwayoyi da makamai.
Sai dai Mista Maduro ya musanta duka zarge-zargen da ake yi masa.
Baya ga Venezuela akwai ƙasashe da dama da Trump ke nuna wa yatsa, wani abu da masana ke hasashen cewa komai zai iya faruwa da su.
Wannan ya sa BBC ta rairayo wasu ƙasashe da ake tunanin Trump zai iya far wa bayan Venezuela.
Greenland
Wani tsibiri ne mai ɗimbin albarkatu da ke cikin ƙasar Denmark, wanda Amurka ke da muradi a c ikinsa.
Tuni Amurka na da sansanin soji a tsibirin, kuma tuni Shugaba Trumpo ya nuna sha'awarsa ta mallakar tsibirin baki ɗaya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Muna son yankin Greenland saboda dalilai na tsaron ƙasarmu", kamar yadda ya shaida wa ƴanjarida, yana mai cewa tuni ''jiragen ruwan Rasha da China suka yi wa yankin kawanya ta ko'ina''.
Tsibiri ne mai cike da albarkatun ma'adinai, da ake ƙera manyan wayoyin hannu na zamani da motocin laturoni da kayan aikin soji.
Tsibirin wani muhimmin wuri a arewacin Atalantica, inda ta nan ake iya shiga muhimman wurare na tekun, kuma ana sa ran nan gaba kaɗan yankin zai kasancen hanyar da jiragen dakon kaya za su riƙa zirga-zirga.
Cikin martanin da ya mayar wa Trump, Firaministan yankin Jens Frederik Nielsen ya bayayna ƙudirin Amurkan na mallakar yankin a matsayin ''abin da ba zai yiwuwa'' ba
"Baba wata matsin lamba, babu wasu maganganu, babau kuma batun mamaya marar dalili. Muna maraba da tattaunawa ta hanyar lalama, kuma hakan zai faru ne kawai ta hanyoyin da suka dace bisa tanadin dokokin duniya,'' in ji shi.
Colombia
Sa'o'i bayan harin Venezuela, Shugaba Trump ya gargaɗi Shugaban ƙasar Colombia Gustavo Petro da ya yi "karatun ta nutsu".
A matsayinta na makwabciyar Venezuela daga Yamma, Columbia ƙasa ce ɗimbin albarkatun rijiyoyin man fetur a ƙarƙashin ƙasa, sannan kuma babbar mai arzikin zinare da azurfa ce da ma'adinan emeralds da platinum da kuma coal.
Sai dai ƙasar ta kasance wani babban yanki da ake safarar miyagun ƙwayoyi, musamman hodar ibilis.
Tun bayan da Amurka ta fara kai hare-hare kan ƙananan jiragen ruwa a yankin Karebiya da gabashin Fasifik, kan abin da Trump ya bayyana ba tare da hujja ba cewa suna ɗauke da miyagun ƙwayoyi - aka riƙa samun takun saƙa tsakanin Trump da shugaban ƙasar mai tsattsauran ra'ayi.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne Amurka ta sanya wa Shugaba Petro takunkumi, saboda zarginsa da barin gungun masu safarar ƙwayoyi na ''harkokinsu'' a ƙasar.
"Ba za mu bar shi ya jima yana aikata hakan ba'', a cewar Mista Trump.
Da aka tambaye shi ko Amurka za ta kai hari Columbia, sai Trump ya ce ''Hakan zai yi min kyau''.
A baya Colombia babbar ƙawar Amurka ce a yaƙin da safarar miyagun ƙwayoyi, inda take karɓar miliyoyin daloli a kwaoce shekara na taimakon soji don yaƙi da masu safarar ƙwayoyin.
Iran
Yanzu haka Iran na fuskantar gagarumar zanga-zangar ƙin jinin gwamnati, kuma tuni Trump ya yi gargaɗin cewa zai iya kai hari ƙasar cikin dare idan har ƙasar ta yi kuskuren kashe masu zanga-zangar.
"Muna nan mun sanya idanu a kansu. Idan suka fara kashe masu zanga-zangar kamar yadda suka yi a baya, Amurka za ta kai musu hari mai muni,'' kamar yadda ya shaida wa manema labarai a cikin jirginsa.
Amurka ta jima tana yi wa Iran barazanar kai wa gwamnatinta hari, bayan da a shekarar da ta gabata ta kai wa tasoshin nukiliyarta hari.
Lamarin ya zo ne bayan Isra'ila ta ƙaddamar da manyan hare-hare da nufin wargaza shirin iran na ƙera makamin nukiliya, lamarin da ya haifar da yaƙin kwana 12 tsakanin ƙasashen biyu.
A wata ganawa da ya yi da Firamistan Isra'ila a gidanda da ke Mar-a-Lago a makon da ya gabata, an ce Iran na daga cikin manyan batutuwan da suka tattauna.
Kafofin yaɗa labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa Netanyahu ya nuna alamun kai wa Iran sabbin hare-hare a 2026.
Mexico
Batun ''gina katanga'' tsakanin Amurka da Mexico na daga cikin baututuwan da suka sanya Trump samun nasara a zaɓen 2016.
A ranarsa ta farko bayan komawa shugabancin Amurka a karo na biyu a 2025, ya sanya hannu kan dokar sauya sunan tekun Mexico zuwa ''Tekun Amurka''.
Ya sha nanata iƙirarin cewa hukumomin Mexico ba sa yin abin da ya kamata wajen dakatar da ƙwararar miyagun ƙwayoyi da ƴan-cirani ba b isa ƙa'da ba zuwa Amurka.
Yayin da yake jawabi a ƙarshen makon da ya gabata, Mista Trump ya ce miyagun ƙwayoyi na ''shigowa'' Amurka ta kan iyakar Mexico, kuma ''ya kamata mu yi wani abu'', yana mi cewa masu safarar ƙwayoyin da ke ƙasar sun yi ''ƙarfin gaske''.
Shugaban ƙasar Mexico, Claudia Sheinbaum ya sha fitowa bainar jama'a yana watsi da duk wani shirin Amurka kan man ƙasarsa.
Cuba
Ƙasar wadda tsibiri ce bai murabba'in kilomita 145 da ke kudancin jihar Florida , ta kasance ƙarƙashin takunkuman Amurka tun farkon shekarun 1960.
Haka kuma ƙasar ta kasance babbar ƙawar Shugaban Venezuela Nicolas Maduro.
A ƙarshen makon da ya gabata Shugaba Trump ya bayyana cewa babu buƙatar ɗaukar matakin soji kan Cuba, saboda tuni ƙasar ta ''ruguje''.
"Bana tunanin muna buƙatar ɗaukar wani mataki", in ji shi. "Saboda ƙasar kamar ta gama faɗuwa."
"Ba na tunanin ko za su iya farfaɗowa, amma Cuba kam ai yanzu ba ta da ko sisi,'' in ji Trump.
"Dama daga Venezuela suke samun kuɗi, daga man Venezuela suke samun taro da kwabo."
Venezuela na fitar da kusan kashi 30 cikin 100 na manta zuwa Cuba, wani abu da ke barazana ga rushewar Cuban idan gwamnatin Maduro ta faɗi.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio - wanda ɗa ne ga ƴan ciranin Cuba - ya jima yana kiran samun sauyin gwamnati a Cuba.
A ranar Asabar ya faɗa wa manema labarai cewa ''Inda a ce a Cuba nake zaune kuma ina cikin gwamnati, to da zan damuda halin da gwamnatin ke ciki , ko da kaɗan ne''.
"Idan shugaban ya yi magana, ya kamata ku ɗauke ta da muhimmanci," in ji shi.











