Mece ce matsayar ACF kan ƴantakarar shugaban ƙasa ga Arewa a zaɓen 2027?

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya ACF, ta bayyana wasu tsare-tsare kan arewa ga masu neman takarar shugaban kasa a zaɓen 2027.
ACF mai fafutukar kare muradun yankin arewaci ta ce ba za ta fito fili ta nuna goyon baya ga wani ɗantakarar shugaban ƙasa daya ba a zaben 2027, kamar yadda Farfesa Tukur Muhammad-Baba sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar ya shaida wa BBC.
Sai dai ya ce za su diba kuɗurorin ƴantakarar da manufofinsu da kuma alƙawuran da suka ɗauka.
Ya ƙara da cewa nan da watanni masu zuwa ACF za ta gana da masu neman tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar ɗaya bayan ɗaya, don ta tantance manufofi da tanade-tanaden da kowannesu ya yi wa yankin na arewa idan ya ci zabe.
Ya ce zaman da za su yi da ɗantakarar zai tantance shirin da za su yi wa arewa da ma Najeriya baki ɗaya.
"Za mu kira manya-manyan ƴantakarar shugaban ƙasa, mu tambaye su, me za ku yi wa arewa? Ya za ku tabbatar da cewa arewa ba ta yi danasani ba?"
"Za mu saka a mizanin tarihi, sannan me ya dace da arewa sai mu faɗa wa jama'a ga abin da muka gani," in ji Farfesa Tukur Muhammad-Baba.
Ƙalubalen tsaro na cikin manyan matsalolin da suka addabi yankin arewacin Najeriya, baya ga rashin ayyukan yi da talauci da ya yi wa yankin katutu sakamakon durkushewar masana'antu da lalacewar ilimi.
Dalilin ƙin goyon bayan ɗantakara
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
ACF ta ce ba ƙungiyar ba ce ta siyasa amma ƙungiyar ta ce babban muradinta shi ne abin da zai tabbatar da ci gaban yankin arewacin Najeriya.
Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya ce siyasa ra'ayi ne - kowa da irin nasa, "don haka ACF ba za ta fito ta ce ga ɗantakarar da take goyon baya ba, amma za ta bayyana irin kuɗirin da take a yi wa arewa," in ji shi.
Ƙungiyar ACF ta ce za ta faɗakar da al'ummar yankin sannan za ta tattara buƙatun arewa ta miƙa wa duk ɗantakarar da Allah ya ba nasara.
Sannan ƙungiyar za ta ci gaba da tunatar da duk wanda ya yi nasara alƙawalin da ya yi wa yankin arewa domin ya cika, amma ba tare da bayyana matakin da ƙungiyar za ta ɗauka ba ga ɗantakarar da ya gaza cika alƙawarin da ya ɗauka ba.
Amma Farfesa Tukur Muhammad-Baba sakataren yaɗa labarai na ACF ya ce za su tunatar da al'ummar yankin cewa ɗantakara ya yi alƙawali bai cika ba.
Ko a zaɓen 2023 ƙungiyar ACF ta taɓa gayyatar manyan ƴantakarar shugaban ƙasa domin su zo yi bayani kan manufofinsu musamman yadda za su magance matsalolin tsaron da ya addabi yanki arewa da talauci da sauran matsalolin da ke addabar yankin.
Sai dai wasu daga cikin manyan ƴantakarar daga yankin arewaci ba halarci zaman ba, musamman ɗantakarar jam'iyyar PDP tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ɗantakarar jam'iyyar NNPP tsohon gwamnan gwamnan Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.











