Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 10/01/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 10/01/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. An tsaurara matakan tsaro a sassan Uganda gabannin zaɓe

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Kwanaki biyar gabanin zaɓen Uganda, an jibge tarin jami'an tsaro a Kampala babban birnin ƙasar.

    A sassa daban-daban na birnin, an ga jami’an tsaro na yin jerin gwano, yayin da motocin sulke ke girke a wurare daban-daban.

    Muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin Uganda, Kanar Chris Magezi, ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na X da ke nuna jami’an soji na sintiri a cikin birnin a cikin motoci masu sulke.

    "Babu wani dalili na fargaba. Duk da haka, ba za mu lamunci barazanar tashin hankali a lokacin zaɓen daga wasu ƴan siyasa da magoya bayansu ba," Col. Magezi ya rubuta a shafinsa na X.

    Galibi zaɓuɓɓukan ƙasar Uganda na baya sun zo da tashe-tashen hankula, waɗanda yawanci suka kasance here-here kan ƴan adawa da magoya bayansu.

    A farkon makon nan ne mai magana da yawun ƴan sanda Kituuma Rusoke ya musanta zargin cewa jami’an tsaro na yiwa ƴan siyasan adawa da magoya bayansu barazana.

    Sama da masu kaɗa ƙuri'a miliyan 20 ne ke shirin fitowa rumfunan zaɓe a mako mai zuwa, a ranar 15 ga watan Janairu, domin zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisar dokoki.

  2. Ana gudanar da aikin ceto mutane bayan zaftarewar ƙasa a Philippines

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu aikin ceto na fafutukar don gano mutane da dama da har yanzu ba a gansu ba sakamakon zaftarewar ƙasa a wani wurin zubar da shara a tsakiyar ƙasar Philippines.

    Magajin garin birnin Nestor Archival ya bayyana cewa an ji ɗuriyar waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin tarkace a wurin da lamarin ya fi muni birnin Cebu, kwanaki biyu bayan faruwar lamarin.

    Kawo yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane huɗu, inji Archival, yayin da wasu 12 kuma su ke asibiti.

    Magajin garin ya ƙara da cewa aikin ceton da ake gudanarwa yana fuskantar ƙalubalen rashin isassun kayan aiki.

    Wurin zubar da shara na Binaliw ya ruguje a ranar Alhamis yayin da ma'aikata 110 ke aiki, in ji jami'ai.

    Ƴan uwan ​​waɗanda suka ɓace suna ta dakon jin labarin inda suke.

    Fiye da ma'aikatan da ke aikin zubar da shara 30 ake tunanin sun ɓace.

  3. Zanga-zangar Iran na ci gaba da ƙazancewa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Iran, jami'an kiwon lafiya a asibitoci biyu sun shaida wa BBC cewa cibiyoyinsu sun cika da waɗanda suka ji raunuka.

    Wani likita ya ce asibitin ido na Teheran ya shiga cikin yanayin tashin hankali, yayin da BBC kuma ta samu rahoto daga wani likitan da ke wani asibitin cewa ba su da isassun likitocin fiɗa da za su iya jure kwararowar waɗanda suka ji rauni.

    A ranar Juma'a shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran na cikin "babban matsala" ya kuma yi gargaɗin "ka da ku fara harbi saboda mu ma za mu fara harbi".

    A cikin wata wasiƙa da ta aike wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Amurka da mayar da zanga-zangar abin da ta kira "ayyukan tada zaune tsaye da kuma ɓarna mai yawa".

    Zanga-zangar adawa da gwamnati da ta ci gaba a ranar Juma'a, ta gudana a wurare da dama, inda ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama biyu suka bayar da rahoton cewa an kashe masu zanga-zangar aƙalla 50.

  4. An maido da lantarki a Kyiv kwana guda bayan harin Rasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An dawo da wutar lantarki a Kyiv bayan da injiniyoyi suka kashe dukkan na'urorin wutar lantarkin birnin bayan wani harin bam da Rasha ta kai.

    Katsewar ya kuma kawo dakatar da tsarin rarraba ruwan sha da na na'urorin ɗumama gidaje a babban birnin ƙasar ta Ukraine. Lamarin ya kuma shafi harkokin sufurin jama'a da ke amfani da lantarki.

    Ana hasashen yayain sanyi zai ƙara muni cikin mako mai zuwa.

    Kai hare-haren bam kan cibiyoyin samar da makamashi a lokacin hunturu wata dabara ce da Rasha ta yi amfani da ita tun farkon mamayar da ta ke yi wa Ukraine.

  5. An ci gaba da zanga-zanga a Amurka bayan jami'an tsaro sun kashe wata mata

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Ana ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Amurka yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula sakamakon harbin da wani jami'in shige da fice (ICE) ya yi wa wata mata a birnin Minneapolis a ranar Laraba.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ƴan cirani sun ce ana shirin gudanar da zanga-zanga fiye da dubu a faɗin ƙasar a ranakun Asabar da Lahadi.

    An samu mabambantan bayanai game da kisan Renee Nicole Good, inda gwamnatin Trump ta ce jami'in ya ɗauki matakin ne don kare kansa bayan da Ms Good ta yi kansa mota da niyyar take shi.

    Jami'an yankin dai sun dage kan cewa matar ba ta da wani haɗari a tattare da ita.

    Masu shirya zanga-zangar sun ce zanga-zangar ta ƙarshen mako za ta yi alhinin mutuwarta da kuma ƙara nuna buƙatar kawo ƙarshen tsare baƙi da ake yi ba bisa ƙa'ida ba.

  6. An fitar da zakarun Crystal Palace daga Gasar FA Cup

    Palace

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Macclesfield da ke buga gasa mai daraja ta shida a Ingila ta yi waje rod da Crystal Palace, wadda ke riƙe da kofin FA, a gasar ta bana.

    Magoya bayan Macclesfield sun cika filin saboda murna a lokacin da alƙalin wasa ya hura tashi daga wasan.

    Kungiyar ta Macclesfield ta doke Palace da ci 2-1 a wasan da ya shiga tarihi a gasar.

    John Rooney - wanda ƙanini ne ga tsohon ɗan wasan Ingila Wayne Rooney ne kocin kungiyar ta Macclesfield -wadda ke kudancin Manchester.

  7. Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da sake gina babbar kasuwar jihar

    Gwamman Sokoto

    Asalin hoton, Ahmad Aliyu/X

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ƙaddamar da sake gina kasuwar jihar da ta yi gobara shekaru biyar da suka gabata.

    Yayin ƙaddamar da sake gina kasuwar, Gwamna Ahmad Aliyu ya bayana takaicinsa kan yadda ya ce gwamnatin jihar da ta gabata ta kasa sake gina kasuwar, maimakon hakan ma ta bayar da wani ɓangare na filin kasuwar jingina ga wani banki.

    Gwamnan ya ce yadda kasuwar ke bayar da gagarumar gudunmowa a fagen tattalin arzikin jihar bai kamata a wofantar da ita ba.

    A watan Janairun 2021 ne dai babbar kasuwar ta Sokoto ta gamu da iftila'in mummunar gobara, lamarin da ya jefa ƴan kasuwa da dama cikin mawuyacin hali, yayin da wasu suka koma wasu kasuwannin.

    ''Bayan da gwamnatinmu ta zo ta kafa kwamitin bincike, inda bayan dogon nazari gwamnati ta ƙudiri aniyar biyan kuɗin jinginar, inda kawo yanzu muka kammala biya, kasuwar ta kuma dawo hannunmu'', in ji shi.

  8. Ƴan'awaren Yemen sun musanta soke ƙungiyarsu

    Babbar ƙungiyar ƴan'awaren Kudancin Yemen ta musanta batun cewa za ta rushe kanta bayan wakilanta sun halarci wata tataunawa a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce sanarwar da aka yi a gidan talbijin na Saudiyya ''ba ta da tushe'', kuma an tilasta yinta ne.

    A makonnin baya-bayan nan an ga yadda ƙungiyar STC - da ke samun goyon bayan UAE - ta karɓe iko da wasu yankuna masu yawa a kudancin Yemen.

    Sai dai a baya-bayan nan ƴan'awaren sun rasa iko da wuraren a hannun dakarun gwamnati da ke samun goyon Saudiyya.

  9. DSS ta kama jami'inta da ake zargi da sace wata yarinya a Jigawa

    Jami'in DSS

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta sanar da kama wani jami'inta da ake zargi da sace wata yarinya yar jigawa tare da tilasta mata barin addinin musulunci sannan ya rika lalata da ita har ta haihu.

    A makon nan ne wata kotu a Haɗeja da ke jihar Jigawa ta bayar da umarnin kamo jami'in tare da bincikarsa kan wanna zargi da ake yi masa kan yarinyar mai shekara 16.

    Cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan hulda da jama'a ta hukumar ta DSS, Favour Dozie ta fitar aka kuma wallafa a shafin hukumar, DSS ta ce tana gudanar da bincike game da lamarin.

    ''Muna kuma tabbatar da cewa an kama jami'in mai suna Ifeanyi Onyewuenyi, ba Ifeanyi Festus ba kamar yadda umarnin kotun ya nuna'', in ji sanarwar.

    Hukumar ta ce wannan ɗabi'a da ke zargin jami'in nata da aikatawa ya saɓa wa ƙa'idoji da dokokin aikin DSS, inda ta sha alwashin bayyana wa duniya sakamakon binciken da take yi kan jami'in.

    Rahotonni sun ce jami'in ya sace yarinyar tsawon shekara biyu da suka gabata inda ya ci gaba da ɓoyeta a hannunsa, bayan tilasta mata komawa adinin Kirista, ya kuma riƙa lalata da ita har ta haihu.

  10. Sojojin Siriya sun dakatar da ayyukansu a arewacin Aleppo

    Rundunar sojin Siriya ta ce ta dakatar da ayyukanta a wata gunduma da ke arewacin Aleppo, inda aka shafe tsawon kwana huɗu ana samun rikici tsakanin sojoji da mayaƙan Ƙurɗawa

    Sojojin sun ce za su kori mayaƙan Kurɗawa zuwa birnin Tabqa.

    Sai dai mayaƙan Kurɗawan sun musanta cewa dakarun gwamnati sun ƙwace iko da unguwar Sheikh Maqsoud - wuri na ƙarshe da mayaƙan ke da ƙarfi a birnin Aleppo.

    Gwamnan birnin ya ce mutum 150,000 rikicin ya raba da muhallansu.

  11. Hotunan masu zanga-zanagr ƙin jinin gwamnati a Iran

    Masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An shafe tsawon daren jiya ana gudanar da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Iran
    Masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Dakarun sojin ƙasar sun ce za su kare ƙasar daga abin da suka kira masu zanga-zangar da ke son tayar da hargitsi a ƙasar.
    Masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Iran ta zargi ƙasashen yamma da ingiza masu zanga-zangar
  12. Ethiopia za ta gina sabon baban filin jirgin sama

    Abiy Ahmed

    Asalin hoton, AFP

    Firministan Ethiopia, Abiy Ahmed ya ƙaddamar da aikin ginin wani sabon babban filin jirgin sama mafi girma a tarihin Afirka

    Babban filin jirgin saman na Bishoftu za a gina shi tazarar kilomita 45 daga Addis Ababa, babban birnin ƙasar.

    Idan an kammala aikin zai zama ƙari kan filin jirgin Addis Ababa da ake da shi yanzu.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Abiy ya ce sabon filin jirgin zai mayar da ƙasar zama ɗaya daga cikin manyan ƙasashen masu ƙarfin sufurin jiragen sama.

    Ana sa ran kammala aikin gina sabon filin jirgin nan da shekarar 2030.

  13. Ɗan tsohon sarkin Iran ya buƙaci masu zanga-zanga su mamaye birnin Tehran

    Reza Pahlavi

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗangidan tsohon gidan sarkin Iran - da ke zaman gudun hijira a Amurka - ya buƙaci masu zanga-zangar adawa da gwamnatin ƙasar su ƙara mamaye tare da ƙwace manyan sassan birnin Tehran.

    Reza Pahlavi ya yi kiran ƙara fitowar masu zanga-zanga, yayin da yace yana shirin komawa ƙasar.

    Katsewar intanet da aka yi a faɗin ƙasar ya taiƙata zanga-zangar.

    Da safiyar yau ne dakarun sojin ƙasar suka sha alwashin kare muradun ƙasar da gine-gine da dukiyoyin gwamnati.

    Wasu likitoci a wasu asibitocin ƙasar biyu sun shaida wa BBC cewa asibitocinsu sun cika da majinta - da suka ji rauni sakamakon zanga-zangar, ciki har da masu raunin harbin bindiga.

    Iran ta zargi Amurka da kitsa zanga-zangar, zargin da Washintong ɗin ta musanta.

    Shugaba Trump ya sha alwashin kai hari ƙasar idan aka kashe masu zanga-zanga.

  14. Ko Super Eagles za ta iya kai semi fainal a Afcon?

    Wasu yan wasan Super Eagles

    Asalin hoton, X/Super Eagles

    Najeriya ta barje gumi da Aljeriya a wasan zagayen ƙwata fainals yau Asabar a birnin Marrakech a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Morocco.

    Najeriya ta kai matakin ne bayan cinye duka wasannin rukuni na uku ta ja ragama da lashe dukkan wasa uku da maki tara.

    Sannan ta yi waje rod da Mozambique a gasar a wasan zagayen ƴan 16 bayan ta zura mata kwallo 4-0.

    Ita kuwa Aljeriya mai Afcon biyu da ta ɗauka a 1990 da kuma 2019, ta kai zagaye na biyu a wasannin bayan lashe dukkan karawar rukuni na biyar da haɗa maki tara.

    Daga nan ta fitar da Jamhuriyar Congo da cin 1-0 a zagaye na biyu a minti na 119 ta hannun Boulbina daf da za a tashi a karin lokaci.

  15. Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin ƙarfafa dakarun ƙasar

    Tinubu

    Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta alƙawarta sake ƙarfafa dakarun tsaron ƙasar domin magance matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan ƙasar.

    Mataimakin Shugaban Ƙasar, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a lokacin taron addu'o'i na musamman ga dakarun tsaron ƙasar da aka gudanar a Babban Masallacin Juma'a na ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

    Shettima ya yaba wa gudunmowar da sojojin ƙasar da suka mutu a bakin aikinsu na kare kima da mutuncin ƙasar, da kuma kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

    An gudanar da taron addu'o'in ne a wani ɓangare na bikin ranar tunawa gudunmowar da dakarun tsaron Najeriya ke bai wa ƙasar.

    Gwamnatin ƙasar ce ta ware ranar 15 ga kowane watan Janairu domin karrama dakarun tsaron ƙasar.

    Kalaman mataimakin shugaban ƙasar na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara samun barazanar tsaro a ƙasar, inda a yan kwanakin nan ma shugaban Amurka ya yi barazanar sake kai hari Najeriya.

  16. Likitocin Edo sun dakatar da aiki 'sai an ceto' mambobinsu da aka sace

    Likitocin Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Likitocin Najeriya rashen jihar Edo ta ce sun dakatar da aiki har sai hukumomin ƙasar sun ɗauki matakin kuɓutar da wasu mambobinta biyu da ƴanbindiga suka sace a kan hanyarsu da zuwa wurin aiki a jihar.

    Ƙungiyar ta ce ta ɗauki matakin ne domin ganin an kare rayukan duka sauran mambobintu da ke faɗin jihar.

    Sakataren ƙungiyar Likitoci ta ƙasar, Dokta Mannir Bature Tsafe ya shaida wa BBC cewa bayan sace likitocin biyu, da aka yi garkuwa da su tare da ɗaya daga cikin ‘ƴan’uwansu, bayanan na cewa an ma kashe ɗan’uwan.

    ‘’Wannan ne ya ɗaga hankali mambobinmu a matakin ƙasa, musamman waɗanda ake aiki a jihar Edo’’, in ji shi.

    Ya ƙara da cewa ƙungiyarsu ta ɗauki matakin sanar da gwamnati halin da ake ciki da kira ga jami’an tsaro don kuɓutar da likitocin biyu.

    ‘’Don haka muka dakatar da aiki har sai mun ga irin ƙoƙari da hoɓɓasan da jami’an tsaro za su yi don tunkarar matsalar’’, kamar yadda ya yi ƙarin bayani.

  17. An sake shafe dare ana zanga-zangar adawa da gwamnati a Iran

    masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Iran sun sake shafe tsawon dare sun gudanar da gangami a kan manyan titunan biranen ƙasar, tare da nuna bijirewa ga mahukuntan ƙasar.

    Wasu bidiyoyi da aka aike wa BBC duk da katsewar intanet a ƙasar, sun nuna masu zanga-zangar na rera waƙoƙin martani ga jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.

    Rahotonni na nuna cewa zanga-zangar ta yi matuƙar muni a wasu yankunan ƙasar, inda wani likita ya ce ya yi wa wasu masu zanga-zangar da dama da aka harba magani.

    Ana kallon wannan zanga-zanga a matsayin ruruwar tashin hankali mafi muni tun shekaru da dama a Iran.

    Iran dai na zargin Amurka da rura wutar zanga-zangar wajen rikiɗewa daga ta lumana zuwa tashin hankali.

    A nasa ɓangare Shugaba Trump na Amurka ya ce shi ma zai iya harbin bindiga kamar yadda ake harbin masu zanga-zanga.

    Tuni dai wasu ƙasashen yamma suka yi kira ga Iran ta bar ƴan ƙasar su yi zanga-zangarsu.

  18. Abin da ya sa muke son mallakar Greenland - Trump

    Greenland

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Amurka na son ‘’mallakar’’ tsibirin Greenlanda ne domin hana ƙasashen Rasha da China ƙwace yankin.

    Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Juma’a, Mista Trump ya ce ‘’ƙasashe na son mallakar yankin, don haka dole mu kare aukuwar hakan’’.

    ‘’Za mu yi hakan cikin ‘’ruwan sanyi’’ ko ta amfani da ƙarfi’’, kamar yadda ya bayyana.

    A baya-bayan nan Fadar White House ta ce tana duba yiyuwar sayen yankin daga ƙasar Denmark, amma duk da haka ta ce ba ta yanke shawarar haƙura da mamayar yankin da ƙarfi ba.

    Denmark da tsibirin na Greenland dai sun bayyana cewa yankin ba na sayarwa ba ne.

    A baya-bayan nan dai tsibirin Greenland na jan hankalin manyan ƙasashen duniya sakamakon irin tarin albarkatun ma’adinan da ke daskare a yankin.

  19. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safoyar wanna rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.