Yadda al'ummar Funtua ke cikin mawuyacin hali saboda hare-haren 'yan bindiga

Asalin hoton, OTHER
Al'ummar karamar hukumar Funtua da ke jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya na cikin yanayi na fargaba da zaman dar-dar bayan da matsalar tsaro ke ci gaba da da da kamari a yankunan kananan hukumomi goma sha daya na shiyyar karamar hukumar, inda bayanai suka ce a 'yan kwanakin baya-bayan nan 'yan bindiga sun kashe mutane da dama, sannan kuma sun sace mutum fiye da 200.
Al'amarin dai ya hana manoma da dama na yankin yin noma a daminar bana, kamar yadda suka saba, a sakamakon hare-haren 'yan bindiga.
Hakan kuwa na aukuwa ne duk da matakan tsaro da hukumomin da abin ya shafa suke bayar da tabbacin suna bi don shawo kan matsalar.
Yanzu haka dai yawaitar hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa yau da kullum, ta jefa jama'ar shiyyar Funtuwa cikin halin kaka-nika-yi.
Wani mutumin yankin da BBC ta zanta dashi ya ce a yanzu haka jama'ar yankin Funtua na cikin tashin hankalin da ya misaltuwa.
Ya ce," Tun da 'yan bindiga suka fara kai hare-hare kusan shekara 10 a wasu yankuna na Katsina, jama'ar Funtua bas u taba ganin tashin hankali da hare-haren 'yan bindiga kamar a wannan lokacin ba."
" Baya ga Funtua wannan matsalar ma na faruwa a kananan hukumo kamar Matazu da Malumfashi da Kankara da Faskari da Sabuwa da Dan ja da Dandume da dai sauransu." In ji shi.
Mutumin ya ce," A yankin Funtua, 'yan bindiga sun shiga garuruwa kamar Bagaji Wando inda suka kashe mutum tara tare da awon gaba da wasu 37, sannan sun kona motoci biyu, sannan sun je wani gari da ake cewa Ilallah inda suka kashe mutum biyar da tafiya da wasu hudu, ga harin da suka kai Mai Gamji, inda anan ma suka kashe wani makeri, kai hatta cikin garin Funtua ma ba a tsira ba."
Ya ce," A cikin garin Funtua ma akwai unguwannin da suka je suka kwashi mutane, ga harin da suka kai Nasarawar Dan Kurmi da Dandume, kai a takaice dai a cikin kwanaki bakwai 'yan bindigar sun sace mana mutane sun kai 200 kuma suna hannunsu."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsanantar matsalar tsaron dai ta kai intaha, a cewar mutumin na shiyyar Funtuwa, wanda ya bukaci a sakaya sunansa.
Fatan jama'ar shiyyar ta Funtuwa a jihar Katsina dai, shi ne a kara tashi tsaye, wajen hanzarta kawo karshen wannan matsala ta tsaro da ta zama wani babban jidali.
Ko da BBC ta tuntubi kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ta Katsina, Dokta Nasiru Mu'azu, ya danganta karuwar hare-haren 'yan bindigan ne da lokacin damina da ake ciki, amma kuma ya ce gwamnatin na iyakar bakin kokarinta wajen ganin na shawo kanta.
Ya ce," Gwamnatin jihar Katsina kowa ya san ba tayi kasa a gwiwa ba kullum cikin fada ta ke da barayin dajin nan, haka sojoji ma na iyakar bakin kokarinsu kai har ma daga Maiduguri mai dauko wadanda ake cewa (Civilian Hunters) suna nan a Faskari da Malumfashi da kuma Kankara, duk suna nan suna ta dauki ba dadi da 'yan bindiga."
A baya bayan nan dai gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda,inda ya jagoranci wasu dattawan jihar suka ziyarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, domin neman daukinsa game da wannan matsala ta tsaro da ta addabi jihar.
Ya kuma yi alkawarin hanzarta daukar matakan duk da suka kamata don magance ta.
Kazalika su ma wakilan jihar ta Katsina da ke majalisar dokokin kasar sun koka wa shugabannin hukumomin tsaro, game da wannan matsala inda suka ba su tabbacin za a yi abin da ya dace kan lamarin.











