Abubuwan da za su sa aurenku ya yi ƙarko

Aure

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Baya ga mutuwa da yunwa, waɗanda ɗan Adam ya kasa yi wa kansa maganinsu, akwai kuma mace-macen aure duk da ɗumbin litattafai da maƙaloli da wa'azuzzuka da ake yi da zimmar magance ta.

A kowace rana akan ɗaura dubban aure ko fiye da haka a cikin kusan kowace al'umma a duniya. Sai dai yayin da ake ɗaura dubbai kullum, haka ma dubbai ke mutuwa a kowace rana.

A jihar Kano kaɗai, aure 999 ne suka mutu cikin wata tara na farkon 2023, a cewar wani rahoto da reshen ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta duniya na Kano ya fitar a wannan makon.

Ta samu waɗannan alƙaluma ne bayan ta karɓi ƙorafi 1,080 daga ma'aurata, wanda ya ninninka na 2022 da ta karɓa (288).

A 2020, hukumar Hisbah ta Kanon ta ce aure 631 ne suka mutu, yayin da wani bincike na Mujallar International Journal of Social Science and Humanity da aka yi a 2009 ya ce akwai sama da zawarawa miliyan daya da aurensu ya mutu a jihar.

Idan muka duba matsalar a Najeriya, abu ne mawuyaci a iya samun alƙaluman da ke nuna yawan rabuwa ko kuma sakin aure, ko kuma yawan zawarawa maza da mata.

Amma dai a alƙaluman hukuma, wani rahoto na hukumar ƙididdiga ta ƙasa wato National Bureau of Statistics (NBS) ta wallafa a 2016 ya ce kashi 0.2 cikin 100 na maza da kuma 0.3 na matan Najeriya ne suka raba aurensu a kotu.

Sai dai kuma, bayan kasancewar rahoton tsoho, shakka babu adadin auren da ke mutuwa sun ninninka haka kasancewar har yanzu aure-auren da ake ɗaurawa a wajen kotu sun ninninka na kotun, haka ma waɗanda ke mutuwa.

Ganin cewa matsalar na neman ta gagari Kundila, ko me ya kamata ma'auratan su din ga yi don yauƙaƙawa da kuma guje wa lalacewar auren nasu?

Mun tuntuɓi Sheikh Ibrahim Khalil, malamin addini a Kano, da kuma Maijidda Labo Mahuta, wata mai koyarwa da bayar da shawarwari kan zaman aure da soyayya a Abuja, don jin amsar wannan tambaya.

Abubuwa biyar daga Sheikh Ibrahim Khalil

Sheikh Ibrahim Khalil

Asalin hoton, Nasara Radio

Bayanan hoto, Sheikh Ibrahim Khalil shahrarren malami ne a Kano da ke gabatar da shirye-shirye da dama kan zamantakewa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shahararren malamin addini a Kano - wanda kuma yake gabatar da shirye-shirye da dama a gidajen rediyo game da zamantakewa -ya zayyana abubuwa biyar da yake ganin su ne kan gaba wajen magance matsalar rabuwar aure.

Haƙuri: "Haƙuri ne ke riƙe aure. Miji da mata su zama masu haƙuri. Miji ya daina garaje wajen yin saki, ita kuma mace ta daina hasala."

Kalmomi masu kyau: "Lallai ne miji ya sani cewa kalmomi masu daɗi ne ke zaunar da aure lafiya. Ya dinga yabonta, yana ziga ta, yana koɗa ta, yana tausasa mata.

"Musamman a yanzu da ake cikin wani hali, ya dinga ba ta haƙuri, yana kwantar mata da hankali."

Daina kai wa iyaye ƙara: "Lallai ne su daina kai wa magabatansu ƙara, su daina saka wani mutum na uku a tsakaninsu a harkar aure."

Fahimtar juna: "Abin da ke zaunar da aure lafiya shi ne fahimtar juna. Mace ta gane abin da mijinta ba ya so ta bari, shi kuma ya yi ƙoƙarin yaba mata a kan kowane abu."

Kar a yi hukunci lokacin fushi: "Idan suna cikin fushi kar wani daga cikinsu ya yi wani hukunci. Idan namijin ne ya yi fushi ta ƙyale shi ya huce sannan su yi magana.

"Idan ita ce ta yi fushin ya bari ta huce sannan su yi magana. Amma a daina garajen saki, ko garajen kai ƙara wajen iyaye, ko kai ƙara kotu, ko wani wuri."

Abin da mutane ba su sani ba game da aure - Maijidda

Maijidda Labo Mahuta

Asalin hoton, Instagram/jyda Labo Mahuta

Bayanan hoto, Maijidda - wada aka fi sani da jyda Labo Mahuta a shafukan zumunta -na koyar a zaman aure a Abuja

"Kamar yadda muke ɗan'adam daban-daban haka ma aure yake daban-daban," a cewar Maijidda, tana mai ƙarawa da cewa "gidan iyaye daban, gidan miji ma daban".

Malamar ta ce wannan na nufin saurayi da budurwa za su iya fuskantar yanayi na zaman aure nau'i daban ba irin wanda suka saba gani ba a gidan iyayensu ba.

"Abin da nake so a gane shi ne, tarbiyyarmu ta sha bamban da juna. Ɗabi'unmu ba ɗaya ba ne. Wasu na da lalurar fushi, ko ta ƙwaƙwalwa da suka samu tun daga yarintarsu saboda wani dalili."

Haka nan, ta buƙaci ma'aurata su rage burin abin da suke tsammanin tararwa a gidan aure kafin su shiga daga ciki.

"Bai kamata mutum ya ce yadda mahaifiyarsa take haka yake so matarsa ta zama . Ya kamata a shiga gidan aure tsakani da Allah kuma da niyyar cewa su ne za su tsara nasu nau'in zaman auren, ba wai irin wanda ƙawarta ko abokinsa suke yi ba.

"Dole ne sai miji da mata sun gane cewa su ɗin mutane ne daban-daban tun daga farko, masu ɗabi'u daban."

Emotioanal intelligence (EI) - 'Mutane da yawa ba su da kissa mai amfani'

Wani abu da Maijidda ta assara da kissa ko kuma kaifin hankali shi ne Emotioanal intelligence (EI), wanda ta ce da yawan ma'aurata ba su da shi kuma ba su yin wani ƙoƙari don samun sa.

"EI yana koya mana yadda za mu san kanmu, mu san abin da ke ɓata mana rai, mu san lokacin da muke yin fushi, mu san lokacin da muke kishi, sannan kuma mu san yadda abokan zamanmu suke yin tunani.

"Wani abu ne idan miji ya faɗa wa matarsa ko mata ta faɗa wa mijinta zai jawo rigima? Wace hanya ya dace mata ta bi wajen neman wani abu da take so mijinta ya yi mata, kuma wane irin kalamai za ta yi amfani da su?"

Ta jaddada cewa wajibi ne tun kafin a yi aure masoya su je makarantar aure irin tasu.

"Shi ya sa muke shirya azuzuwa masu sauƙin kuɗi domin wayar da kan mutane a kan aure. Akwai ajin emotional intelligence (kissa), da na masu shirin aure, da kuma na ma'aurata."

'Abin da Hausawa ke ƙaranci a zaman aure'

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Cibiyar faɗakar da ma'aurata yadda ake zaman aure a Kano

A al'ummar Hausawa, an fi mayar da hankali kan shirye-shiryen aure fiye da koya wa ma'auratan yadda za su zauna lafiya da juna.

A wannan zamanin ma ana ganin yadda kashe makuɗan kuɗaɗe ya zama abin gadara da alfahari a aure, kama daga shirya liyafa, da kayan lefe, da kayan ɗaki, da kayan gara, da dai sauransu.

Sai dai za a iya cewa babu laifi a baya-bayan nan ana samun ƙaruwar buɗe cibiyoyin gyara zamantakewar aure a sassan yankin.

BBC Hausa ta ga yadda wasu da ke shirin angwancewa suke zuwa cibiyar gyara zamantakear aure ta Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a Kano a 2020.

"Kamar sumbata (kiss), mutane da yawa na ganin ba Musulunci ba ne, ba na Hausawa ba ne. Amma mun fahimta cewa Annabi Muhammdu SAW yakan yi hakan da iyalansa," a cewar Dr Sadiha Sulaiman, wata da ke shirin amarcewa a lokacin.

"Wasu daga cikin Hausawanmu kuma za ka ga ba su son su fita unguwa da matansu, sai dai direba ya kai su. Wasu kuma ba su son su yi wanka tare da matan nasu," in ji Amir Tijjani Bawa mai shirin angwancewa a 2020.

"Amma ka ga waɗannan abubuwan na ƙara danƙon soyayya."

Duka waɗannan na cikin abubuwan da masu shirin yin aure ke koya a cibiyar, wadda shahararren malamin addinin Musuluncin ke gudanarwa.