Sirrin ma'auratan Kano da suka shekara 50 tare

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Sirrin ma'auratan Kano da suka shekara 50 tare

Wasu dattijan ma'aurata a Kano sun bayyana mana sirrin daɗewar aurensu da ya kai shekara 50.

Mahmud Kabir Yakasai ya ce addini da rashin nuna son kai da dattakon iyayen uwargidansa, Rabi'atu Tahir na cikin sirrin daɗewar aurensu da aka ɗaura tun a 1973.

Uwargidan kuma ta ce aurensu ya yi albarka, har Allah ya ba su 'ya'ya 13, cikin shaƙuwa da mutuntawa da kuma girmama juna.