Daga Bakin Mai Ita tare da Al-amin Buhari
Daga Bakin Mai Ita tare da Al-amin Buhari
Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya karɓi baƙuncin Al-amin Buhari, shahararren ɗanwasan kwaikwayo a Kannywood.
Al-amin ya ce harkar fim ta sauya shi da kusan kashi 80 cikin 100 idan aka kwatanta da lokacin da ya fara.
Ya faɗa wa BBC cewa yana ganin ƙirƙirar sabuwar kasuwa ta zamani ta yadda masu shirya finafinai za su daina dogara da kafa ɗaya, shi ne abin da zai ciyar da masana'antar gaba.
Tace hoto: Abba Auwalu




