Arsenal na zawarcin Goretzka, Real Madrid na bibiyar Schlotterbeck

Asalin hoton, Getty Images
Inter Milan na sha'awar mai tsaron ragar Liverpool na Brazil Alisson, mai shekaru 33, wanda itama Juventus ma ke sha'awar. (La Repubblica)
Manchester United na son kyaftin ɗin Newcastle Bruno Guimaraes, mai shekaru 28, don ya maye gurbin Casemiro dan wasar tsakiyarta da ke shirin tashi a wannan bazarar. (AS)
'Yan wasan Tottenham na fuskantar barazanar rage albashinsu idan ƙungiyar ta nutse daga gasar Premier zuwa gasar Championship. (The Athletic)
Dan wasan baya na Spurs Micky van de Ven ba shi da sha'awar tsawaita zamansa a ƙungiyar, inda Barcelona da Real Madrid ke sa ido kan ɗan wasan na Netherlands, mai shekaru 24. (Give Me Sport)
Bayern Munich za ta mayar da hankalinta wajen kulla sabuwar yarjejeniya da dan wasan gaban Ingila mai shekaru 32 Harry Kane bayan da dan wasan bayan Faransa Dayot Upamecano, mai shekaru 27, ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya a watan da ya gabata. (Fabrizio Romano)
Liverpool, da Arsenal da Barcelona duk suna sa ido kan dan wasan baya na Inter Milan mai shekaru 26, Alessandro Bastoni na Italiya. (Caughtoffside)
Arsenal ce ke kan gaba wajen neman sayen Leon Goretzka na Bayern Munich lokacin da kwantiraginsa zai kare a wannan bazarar, inda dan wasan tsakiyar na Jamus mai shekaru 31 ke sha'awar buga wasa a gasar Premier duk da sha'awarsa da Inter Milan, da Juventus da AC Milan ke yi. (Christian Falk)
A shirye Barcelona take ta biya Manchester United kudin da take so, don rike dan wasan gabanta na Ingila mai shekaru 28, Marcus Rashford, a matsayin din-din-din. (Mirror)
Manchester City na sha'awar sake sayen Lukas Nmecha daga Borussia Dortmund. City ta saki ɗan wasan mai shekaru 25 shekaru biyar da suka gabata ba tare da ya buga wasa a gasar Premier ba amma Pep Guardiola yana son ya dawo da shi. (Goal)
Manchester United ta ƙara sunan kocin Borussia Dortmund Niko Kovac, mai shekaru 54, cikin jerin sunayen masu horarwar da za su iya dauka nan gaba. (Football Insider)
Real Madrid ce a kan gaba cikin jerin kungiyoyin da suka fi damar daukar mai tsaron baya na Jamus Nico Schlotterbeck, mai shekaru 26, daga Borussia Dortmund saboda dangantakar kawance da ke tsakaninsu da ƙungiyar ta Bundesliga. (AS Spanish)
Mai horar da 'yan wasan Arsenal kan bugun tazara na samun wasu kudaden garabasa a duk lokacin da ƙungiyar ta ci kwallo ta hanyar bugun tazara (Times)










