Yaƙin Iran: Wace ƙasa ce ta yi nasara?

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Amir Azimi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian
- Lokacin karatu: Minti 6
Yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran ya kusa zuwa ƙarshe - kamar dai yadda Washington ke bayyanawa.
A ranar Talata, 5 ga watan Mayu, bayan tsagaita wuta na makonni, Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce shirin soji da aka yi wa laƙabi da Operation Epic Fury ya zo ƙarshe.
Don haka, abin tambaya a nan shi ne : wane ne ya yi nasara?
Amsar wannan tambaya dai ta ta'allaƙa ne ga wanda ke bayar da labarin.
A can Iran, kafar yaɗa labarai ta ƙasar na nuna yaƙin a matsayin shaida cewa Iran ta tsaya gaba da gaba da haɗakar soji mafi ƙarfi a duniya, kuma ta yi nasara kansu.
A Washington kuma, Shugaba Donald Trump da gwamnatinsa na iƙirarin cewa su suka yi nasara, kuma sun sha nanata cewa sun cimma burukansu.
Sai dai baya ga duk waɗannan kalaman, a yanzu haka yarjejeniyar da ake yi na neman ta fi yaƙin da ake gwabzawa muhimmanci wajen tabbatar da wanda zai yi nasara.

Asalin hoton, Anna Moneymaker/Getty Images
A cewar rahotanni daga kafar yaɗa labarai ta Axios da kamfannin dillancin labarai na Reuters, da kuma wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka, White House na ganin cewa tana dab da cimma yarjejeniya mai ƙunshe da sharuɗɗa 14 da Iran.
Yarjejeniyar za ta bayar da damar faɗaɗa tattaunawa kan shirin nukuliyar Iran, da batun Mashigar Hormuz da kuma sauran matsalolin da ke addabar yankin.
Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran ya ce ƙasar na sake nazari kan ƙudurin, kuma za ta mayar da martani ta hannun Pakistan da ke shiga takani. Sai dai tuni wasu manyan ƴan siyasa a Iran suka yi watsi da shi.
''Amurkawa ba za su amfana da komai ba a yaƙin da suke rashin nasara,'' in ji wani mai magana da yawun kwamitin tabbatar da tsaron ƙasa na majalisar dokokin Iran, yana mai wasti da buƙatun Amurka.
A cewar bayanan da aka wallafa zuwa yanzu, wajibi Iran ta dakatar da kaso mai yawa na shirin nukiliyarta na shekara 20, ta kuma sallama tarin sinadarinta na Yureniyum (Uranuim), sannan ta bayar da dama a yi kyakkyawan bincike kan harkokinta na nukiliya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rahotanni sun kuma ce cikin buƙatun har da wanda ke neman Iran ta bayar da tabbacin sake buɗe Mashigar Hormuz baki ɗayansa.
A nata ɓangaren kuma idan Iran ta amince, Amurka za ta ɗage takunkuman da ta sanya mata sannu a hankali, za ta kuma saki kadarorin Iran da aka ƙwace, sannan kuma za ta bar Iran ta cigaba da tara sinadarin Uranium kaɗan-kaɗan bayan wa'adin da aka cimma ya kawo ƙarshe.
Sai dai ga mutane da yawa a Iran, suna ganin hakan tamkar miƙa wuya ne.
Kuma suna da dalilin tunanin hakan.
Suna ganin Amurka ta dakatar da shirinta na soji na Operation Epic Fury ne saboda bai samar da sakamakon da take so ba, sannan shirin Operation Freedom - wanda Amurka ta ƙaddamar domin sake buɗe Mashigar Hormuz kuma ya zo ƙarshe cikin ƙanƙanin lokaci - ya na barazanar ƙara dulmiya yankin Gulf cikin rikici.
Duk da dai Iran ta kai hari kan sansanonin Amurka da cibiyoyin makamashi a ƙasashen yankin, babu wanda cikinsu ya shiga yaƙin kai tsaye.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Sai dai abu mafi muhimmanci shi ne gwamnatin musulunci ta ƙasar ba ta ruguje ba, duk da dai an hallaka jagoranta da wasu manyan kwamnadojin sojin ƙasar da manyan jami'an tsaro.
An ci gaba da gudanar da ayyuka a fannin siyasa da tsaron ƙasar, sannan an yi gagagwar maye guraben waɗanda suka mutu.
Kafin soma yaƙin, wasu jami'ai da masu sharhi na ƙasashen yamma na ganin kai hare-haren soji, haɗi da hallaka manyan shugabanni da kwamandojin ƙasar, zai ƙara jefa ƙasar cikin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati, wataƙil ma har ya kai ga kifar da gwamnatin.
Sai dai hakan bai faru ba.
Zanga-zangar da ta girgiza Iran a watannin da suka gabaci fara yaƙin ta kau.
Jami'an tsaro suka tsananta tsaro, sannan kama mutane ya ƙaru, wasu kuma aka aiwatar musu da hukuncin kisa.
Duk dai a wannan lokaci, kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta riƙa nuna masu zanga-zangar goyon bayan gwamnati.

Asalin hoton, Iranian Parliament Speaker Office/Handout/Anadolu via Getty Images
Kakakin majalisar dokokin Iran kuma babban mai shiga tsakani Mohammed Bagher Ghalibaf, ya rubuta a baya-bayan nan cewa ''Mun sani cewa Amurka ba ta jin daɗin halin da ake ciki yanzu, amma mu kuma ba mu ma fara komai ba.''
Amma kuma a ɓangaren shugabancin Iran, rashin nasara wajen kifar da gwamnatin alama ce ta yin nasara, baya ga haka kuma ga hare-haren da Tehran ta kai kan sansanonin Amurka da kayyayakin more rayuwa a yankin, da kuma Isra'ila.
Hakan ne ya sa ba a ga alamun Tehran ta matsu ta kauce wa a sake gwabza faɗa ba.
Hukumomin Iran na ganin ƙasar za ta fi iya jure wa matsin tattalin arziƙi, da harin soji da kuma kwashe tsawon lokaci tana yaƙi fiye da abokan gabar ta.

Asalin hoton, Asghar Besharati/Getty Images
Suna kuma ganin rufe Mashigar Hormuz na nuna irin tasirin da har yanzu Iran ke da shi kan tattalin arzikin duniya.
Hakan ya bayyana matuƙar muhimmancin hanyar ruwan.
Rufe mashigar ya shafi sufurin jiragen ruwa, da samar da abinci, da kasuwancin kasa da ƙasa.
A yanzu Iran na ganin sake buɗe Mahsigar Hormuz a matsayin wani abu da za ta yi amfani da shi wajen yin yarjejeniya.
Hakan kuma na iya yin tasiri a yankin.
A ƙarshen yaƙin, Iran za ta iya kasancewa ta ƙara ƙarfi, musamman kan ƙasashe makwafta da ke da sansanonin Amurka ko kuma suka goya wa Amurka da Isra'ila baya a fakaice.

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images
Sai dai duk hakan ba ya nuna cewa Iran ta cimma abin da take buƙata.
An lalata wurare da dama a ƙasar, manyan jam'ian tsaronta sun mutu, an lalata muhimman kayayyakin more rayuwa, sannan tana fuskantar matsin tattalin arziƙi wanda mai yiwuwa ya iya tayar da wata zanga-zanga.
Amurka da Isra'ila sun kuma nuna cewa za su iya kai hari cikin tsakiyar ƙasar ta hanyar amfani da manyan makamai da kuma tattara bayanan sirri.
Sai dai kuma ba a fagen daga kawai ake gane wanda ya yi nasara ba a wasu lokutan.
Idan za a yi alƙalanci kan wanda ya yi nasara, ba lallai a yi bisa yaƙin kansa ba, sai dai kan sakamakon yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.
Idan Amurka ta tilasta wa Iran haƙura da shirinta na nukiliya, Amurka za ta yi iƙirarin ita ce ta yi nasara.
Idan kuma Iran ta ci gaba da kasancewa mai tasiri a yankin, kuma ta ƙi amincewa da dakatar da shirin nukliyarta, za ta yi iƙirarin nasara.
A yanzu dai dukkaninsu na iƙirarin yin nasara.
Sai dai za a san haƙiƙanin wanda ya yi nasarar ne idan aka kawo ƙarshen yarjejeniyar da ake yi, idan har ɓangarorin biyu suka hau teburin tattaunawar kuma suka tsaya har aka kai ƙarshe.








