KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 16/05/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 16/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya da na Amurka kan kisan Al-Manuki

    Shugaba Tinubu

    Asalin hoton, Bola Tinubu/X

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yaba wa abin da ya kira nasarar hare-haren haɗin gwiwa tsakanin dakarun ƙasarsa da na Amurka wajen kisan mataimakin shugaban ISIS na duniya.

    Cikin wata sanarwa da Shugaba Tinubu ya fitar ranar Asabar ya ce harin da sojojin suka kai ranar Juma'a kan mayaƙan IS ya haifar da kisan Abu-Bilal Al-Manuki tare da wasu mayaƙansa.

    A cewar Tinubu, harin ya faɗa kan gidan Abu-Bilal Al-Manuki da ke yankin tafkin Chadi.

    “Ƙoƙarin sojojin Najeriya sun yi aiki tare da dakarun Amurka, wajen shirya harin haɗin gwiwa da ya haifar da mummunan ɓarna kan manyan jiga-jigan ƙungiyar ISIS.''

    Shugaba Tinubu ya gode wa Amurka kan goyon bayan da suke bayarwa a lamarin.

  2. Sojojin Najeriya sun tabbatar da kisan Abu-Bilal al-Minuki

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Rudunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kisan Abu-Bilal al-Minuki, a wani harin haɗin gwiwa tsakanin dakarun ƙasar da na Amurka.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rudunar sojin ta Najeriya Samali Uba ya fitar a yau Asabar, ya ce sun samu nasarar kai wani tsararren hari da muka shirya ƙarƙashin shirinta na yaƙi da ta'adanci da ya yi sanadiyar kisan Abu-Bilal al-Minuki, ɗaya daga cikin manyan mayaƙan ISIS kuma ɗaya daga cikin ƴan ta'addan da ake da su a duniya."

    Ta ce an samu nasarar harin ne da taimakon haɗin gwiwa da tallafin haɗin gwiwar Amurka wajen musayar bayana shirri.

    "Tare da Amurka mun yi nasarar rusa gungun muggan yan ta'adda, da ke barazana ga rayukan ƴan Najeriya, da sauran ƙasashen da ke Afirka ta yamma."

    Sai dai rundunar sojin ta Najeriya ba ta sanar da inda aka kai harin ba.

    Rudunar sojin ta Najeriya ta danganta Abu-Bilal al-Minuki da hannu a sace ɗaliban makarantar ƴam mata da ke Dapchi, 2018, inda aka sace dalibai 100 a makarantar kwanan ta ƴanmata, da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, wanda hakan ya jefa damuwa a faɗin ƙasar.

  3. Trump ya ce sojojin Amurka da na Najeriya sun kashe mataimakin shugaban IS na duniya

    sojojin Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump na Amurka ya ce dakarun ƙasarsa da na Najeriya sun kashe - mataimakin babban kwamandan ƙungiyar ISIS na duniya a wani hari na haɗin guiwa.

    A wani sako da ya sanya a shafinsa na sada zumunta, shugaban na Amurka, ya ce, Abu-Bilal al-Minuki - wanda shi ne mutum na biyu mafi girman muƙami a ISIS - na ɓuya ne a Afirka.

    ''Daga yanzu ba zai ƙara zama wata barana ga sojojin Amurka da ƙasashen Afirka, ba kuma zai ƙara shirywa hari kan Amurkawa ba'', in ji shugaba Trump.

    Trump ya bayyana al-Minuki - a matsayin ɗan ta'adda lamba ɗaya, da mafi tasiri a duniya, kuma ya ce kawar da shi da aka yi, ayyukan ƙungiyar ISIS, na duniya za su ragu matuƙa gaya.

    ''Duk da cewa yana ɓoye a Afirka, bai san muna samun bayanan sirri game da shi ba'', in ji shi.

    Shugaban na Amurka ya kuma godewa gwamnatin ta Najeriya kan haɗin gwiwar da suka yi wajen wannan aiki, sai dai bai bayar da wani ƙarin bayani ba baya ga haka ba.

  4. Marabanku

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkan mu da safiyar wanna rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu a sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa