Man Utd na son Tavernier, Klopp ya musanta tattaunawa da Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta sanya dan wasan tsakiya na Bournemouth, Marcus Tavernier, dan Ingila mai shekara 26, cikin jerin wadanda take son saye. (Mail Plus)
Bisa ga dukkan alamu Unai Emery na shirin barin Aston Villa a bazaran nan, saboda damuwar da yake nunawa ta rashin sakin kudi da kungiyar ke yi. (Football Insider)
Kociyan Newcastle Eddie Howe zai mayar da hankali sosai wajen neman sabon mai tsaron raga ganin yadda tauraron golan kungiyar, Nick Pope, ke dusashewa, kuma kungiyar ba ta son ta sayi Aaron Ramsdale, wanda ta karba aro, dindindin. (The Athletic)
Wakilin tsohon kociyan Liverpool Jurgen Klopp, ya ce maganar da ake yi ta cewa suna tattaunawa kan karbar aikin horad da Real Madrid, jita-jita ce kawai, domin ba wanda ya tuntube su zuwa yanzu. (Goal)
Kociyan Manchester City Pep Guardiola, ya bayar da tabbacin cewa kungiyar za ta fi yadda take a yanzu a kaka mai zuwa, wanda hakan ya nuna alamun cewa zai ci gaba da zama har zuwa shekarar karshe ta kwantiraginsa a Cityn, bayan da ake ta rade-radin cewa a bana zai ajiye aiki. (Sky Sports)
Fabian Schar da Kieran Trippier, na daga cikin karin 'yan wasan Newcastle, da babu tabbacin ci gaba da zamansu a kungiyar, saboda kungiyar na fuskantar matsalar rasa damar shiga gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa. (ChronicleLive)
Bisa ga dukkan alamu Bernardo Silva, zai bar Manchester City, a watan Yuni, a matsayin wanda ba shi kungiya, domin babu wata tattaunawa da Cityn ke yi da dan wasan na tsakiya na Portugal mai shekara 31 a yanzu kan sabunta kwantiraginsa. (Matteo Moretto)
Manchester Cityn na sha'awar sake sayen Felix Nmecha a matsayin wanda zai rika maye gurbin Elliot Anderson. Dan wasan na tsakiya na Jamus mai shekara 25, ya taka rawar gani sosai a Borussia Dortmund a bana. (Football Insider)
Liverpool na kara nuna sha'awarta a kan dan bayan Nottingham Forest, Murillo, kuma kungiyar ta Anfield na ganin fam miliyan 70 za ta iya sa su samu dan wasan na Brazil mai shekara 23. (Fichajes)
Arsenal na shirin zawarcin dan wasan tsakiya na Newcastle United, Sandro Tonali, a bazara, yayin da Manchester City da Manchester United su ma suke son dan wasan na tawagar Italiya mai shekara 25. (Tuttosport)











