Abin da ya sa gwamnati ta ce Misirawa su koma cin ƙafar kaza

kafafun kaji

Asalin hoton, Getty Images

"Ya Allah, Kada Ka bari mu shiga tsananin da zai kai mu ga cin ƙafar kaza," in ji wani mai bara a gefen masu sayar da kaji cikin kasuwar Giza.

Ƙasar Masar na fuskantar wani matsanancin yanayin tattalin arziƙi, wani lamari da ya sa da ƙyar Misirawa ke iya ciyar da iyalansu.

Shawara ta baya-bayan nan kan abinci mai gina jiki da gwamnati ta bai wa 'yan ƙasar ita ce cin ƙafar kaza - wani sashen jikin tsuntsaye mai yawan sinadaran gina jiki, ko da yake, galibi ana zubarwa ne don karnuka da maguna su samu abin kalaci.

Wannan shawara ta fusata 'yan ƙasar har ta kai ana kakkausar suka ga gwamnati.

Ƙasashe da yawa na fama da gagarumar hauhawar farashi, sai dai duk da kaɗan hauhawar farashin ta zarta kashi 30 cikin ɗari a wannan wata na Maris, Masar na cikin ƙasashen da suka fi jin jiki.

Ga mafi yawan mutane, kayan abincin da a baya kusan kowa yana iya saye, kamar man girki da cukwi amma sun fi ƙarfin mutane da yawa.

Farashin irin waɗannan kayan abinci ya ninka sau biyu ko sau uku a 'yan watanni.

"Sau ɗaya nake cin nama a wata, ko kuma ba saye nake ba kwata-kwata.

Nakan sayi kaza sau ɗaya a duk mako," in ji Wedad, wata mahaifiya mai 'ya'ya uku da ke cikin shekarunta na sittin, a lokacin da take tafiya a tsakanin rumfunan kasuwa.

"A 'yan kwanakin nan, ko ƙwai yana kai wa senti 16."

Wani ɓangare na dalilin da ya sa Masar take fama shi ne ta dogara ne kacokan kan abincin da ake shiga da shi ƙasar daga ƙetare.

Maimakon noman da ake yi a cikin gida don ciyar da ɗumbin al'ummarta sama da miliyan 100.

Kai hatta hatsin da ake ciyar da kajin ƙasar shigar da shi ake yi daga waje.

Fiye da wata 12 da suka wuce, darajar kuɗin Masar wato fam ta faɗi da rabi idan an kwatanta da dalar Amurka.

A watan Janairu, lokacin da gwamnati ta sake rage darajar kuɗin, sai abin ya ƙara haddasa tsadar kayan da ake shigarwa kamar hatsi.

dd
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A shekarar da ta wuce, Wedad na rayuwa ne cikin jin daɗi da kuɗin fanshon da take karɓa duk wata kimanin fam 5,000.

A lokacin tana bayyana kanta a matsayin mai matsakaicin samu.

Amma yanzu, kamar sauran Misirawa da yawa, sai ta yi faɗi-tashi kafin ta samu abin da za ta ciyar da 'ya'yanta.

A yau, ta ɗan yi ƙoƙari ta harhaɗa 'yan kuɗaɗenta da za ta sayi kaji.

Wani mai sayar da kaza ya ce yana sayar da kilo ɗaya na kaza a kan fam 160.

''Wasu kuma suna sayarwa ne a kan fam 175, akwai ma na 190, kai har da na fam 200," cewar Wedad, a lokacin da take cefane.

"Ana sayar da cinyoyin kaza a kan fam 90, har ƙashin kaza ma sayarwa ake yi yanzu - ita kuma ƙafar kaza fam 20," ta faɗa tana dariya cikin shaguɓe.

A lokuta da dama shugaban ƙasar Abdul Fattah al-Sisi kan ɗora alhakin tabarɓarewar tattalin arzikin ƙasar kan guguwar siyasar da ta shafi ƙasashen Larabawa da kuma yadda yawan al'ummar ƙasar ci ƙaruwa cikin sauri.

Ya kuma bayyana annobar Korona da yaƙin Ukraine da ya biyo baya.

Mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a shekarar da ta gabata ta haifar da cikas ga tattalin arzikin ƙasar.

Masar ita ce ƙasa ta biyu a duniya da tafi saye Alkama daga ƙasashen Ukraine da Rasha.

Farashin kayayakin da ake yi da alkama kamar su biredi ya yi tashin gwauron zabi sakamakon daina shigar da alkamar da aka yi zuwa ƙasar.

Haka kuma fannin yaƙin shaƙatawa na ƙasar - wanda ke kawo wa ƙasar kashi 5 na kudin shiga - ya gamu da koma-baya sanadiyyar cutar Korona.

d

Asalin hoton, Getty Images

Masu sharhi na ganin cewa rashin ɗaukar matakan da suka dace daga ɓangaren gwamnati ne ke ƙara dagula lamuran tattalin arzikin ƙasar.

Ƙarfin iko da faɗa-a-ajin fadar shugaban ƙasa da sojoji da jami'an tsaron bayanan sirri sun ƙaru, a lokacin mulkin shugaba Sisi, kamar yadda Timothy Kaldas, mai sharhi kan tattalin arzikin yankin gabas ta tsakiya ya bayyana.

Mista Kaldas hakan na faruwa ne sakamakon gwamnatin ke bai wa jami'anta manyan kwangiloli, ya bayar da misali kan manyan kwagilolin ayyuka da gwamnatin ke bai wa manyan jami'an sojin ƙasar.

Kamfanoni masu zaman kansu na durƙushewa sannu a hankali sakamakon gaza gogayya da kamfanonin gwamnati.

Lamarin da ya janyo kamfanonin ƙasashen waje suka fice daga ƙasar.

Har kusan sau huɗu cikin shekara shida, ƙasar na zuwa Asusun bayar da Lamuni na Duniya (IMF)domin karɓar bashi.

g

Asalin hoton, Getty Images

Ƙasashen yankin Gulf kamar su Haɗaɗdiyar Daular Larabawa da Saudiyya sun sayi kadarorin ƙasar da dama da nufin taimaka wa ƙasar ficewa daga halin matsin tattalin arziki da take ciki.

To sai dai ƙasar ta tsananta musu sharuɗan zuba jari a ƙasar.

Ƙasashen yamma da na yankin Gulf na fargabar ficewa daga ƙasar- wadda ta fi kowacce yawan jama'a a yankin gabas ta tsakiya - idan tattalin arzikinta ya durƙushe.