Bayanin likitan ƙashi kan muhimmancin cin nama ga mace
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A makon da ya gabata ne BBC Hausa ta wallafa wani labari da ke bayani kan wani binciken likitoci da ya ce matan da ba sa cin nama za su iya fuskantar yiwuwar karyewa a kwankwaso nan gaba a rayuwa.
Masu binciken sun rika bin rayuwar mata 26,000 na tsawon shekaru 20 kuma sun gano cewa kashi daya bisa uku na matan da ke cikin rukuni da ba sa cin nama sai kayan lambu ko kayan itace za su iya samun karaya ko targade fiye da masu cin nama.
Labarin ya yi matuƙar jan hankali mutane a Najeriya musamman ma mata, bayan da BBC ta wallafa shi a shafukanta na intanet.
Hakan ne ya sa BBC Hausa ta sake tuntuɓar wani likitan ƙashi a asibitin ƙashi na ƙasa da ke jihar Kano a Najeriya, don ƙrin bayani kan binciken wanda aka yi a Turai.
Dr Aliyu Muhammad ya feɗe biri har bindi a cikin wannan hirar da muka yi da shi a bidiyo.






