Yadda matsalar tsaro ta hana magidanta kwana a gidajensu a Danko/Wasagu

,
Bayanan hoto, ,
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Jama'ar Wasagu da sauran wasu garuruwa kimanin bakwai na yankin karamar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi, na ci gaba da kokawa kan yadda matsalar hare-haren 'yan bindiga ke ta addabar su, al'amarin da ya hana su zaman lafiya, har ma wasu magidanta sun kwashe wata biyar ba sa iya kwana a gidajensu ba .

Matsalar tsaron ta kuma hana jama'ar garuruwan damar girbi da kwashe kayan amfanin gonarsu, bayan kwashe mutum fiye da ashirin a gonaki ranar Alhamis da ta gabata.

Sai dai rundunar 'yan sandan Najeriyar ta ce ana bin matakan shawo kan matsalar tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar ta Kebbi.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa BBC cewa matsalar tsaro ta yi wa garin Wasagu a jihar Kebbi kofar rago

''Duk hanyar da za ka fita daga Wasagu ko kuma za ka shigo, to in ka san za ka iya fita amma ba ka san za ka iya dawowa lafiya ba, saboda koina ana iya haduwa da su 'yan fashin nan''in ji shi.

Ya kuma danganta yawaitar hare haren saboda yankin nada iyaka da jihar Zamfara, inda ya ce 'yan bindigar na garkuwa da mutanen da suka je gona domin tsinkar amfanin gonarsu.

''A ranar alhamis 'yan bindiga sun kwashi mata masu tsinkar gyada su 7 sun ce kowane sai an bada miliyan 2'', in ji shi.

Wani mutumin daya daga cikin wadannan garuruwa da matsalar hare-haren ta zame wa karfen kafa a gefen garin na Wasagu, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya yiwa BBC bayani kan irin tasku da suke ciki:

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''Mun kai akalla wata biyar a yanzu ba kowani magidanci ke kwana a cikin gidanshi ba saboda matsalolin da mu ke ciki.Bayan an hana mu kwana a cikin gidaje yanzu ana bin mutane daji , ko ranar Aljamis an kwashi mutum 20 a Kangon Wasagu'' in ji shi.

BBC ta tuntubi Kwamishinan 'yan sanda a jihar ta Kebbi, Umar Hadeja kan wannan batu kuma ya ce ba a yi kwance da sirdi ba:

''Muna da folis namu na mobil, su na da motocin silke wanda suke sintiri tsakanin Wasagu zuwa kauyukan Danko''

Ya kuma ce Tudun Bichi suna da sansanin sojoji wadanda ke sintiri a wadannan kauyuka

Sai dai Kwamishinan ya ce akwai kauyuka da yawa da suke kyautata zaton sun yi sulhu da 'yan bindiga ba tare da amincewar gwamnatin ba.

'' Kuma wannan sulhun da suke yi shi ne ya ke kawo matsala kwarai da gaske domin daya daga cikin sharuddan da suka gindaya mu su shi ne za su rika basu labari kan jamian tsaro'' in ji shi.

Don magance wannan matsala ta infomanci, kwamishinan 'yan sandan na jihar Kebbin ya yi kira ga shugabannin al'ummomin garuruwan da abin ya shafa, su taimaka wajen zakulo mutane da ke tsegunta bayanai ga 'yan bindiga.