Yawan mutanen da ke ƙaura zuwa Birtaniya ya ragu zuwa 77,000

Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Birtaniya (ONS) ta fitar ya nuna cewa adadin mutanen da suka shiga ƙasar ya zarce waɗanda suka fice da mutum 77,000 a shekarar da ta ƙare a watan Yunin 2026.
Wannan shi ne adadi mafi ƙanƙanta cikin kusan shekaru 30, tun daga 1997, ban da lokacin annobar korona.
Adadin ƙaura da ake kira net migration shi ne bambancin yawan mutanen da suka shigo ƙasar da waɗanda suka fice zuwa wasu ƙasashe.
Rahoton ya kuma nuna cewa yawan mutanen da suka nemi mafaka a Birtaniya ya ragu da kashi ɗaya bisa uku a shekarar da ta ƙare a watan Satumban 2026.
A cikin watanni 12, mutum 74,000 ne suka nemi mafaka, wanda ke nuna raguwar kashi 33 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Sai dai wannan adadi har yanzu ya haura matakin da aka gani a tsakanin shekarun 2004 da 2021.
Ma'aikatar cikin gida ta Birtaniya ta ce raguwar ta samo asali ne musamman daga ƙarancin mutanen da suka shiga ƙasar ta hanyoyin da ba bisa ƙa'ida ba.
Duk da haka, hanyoyin shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba na ci gaba da kasancewa mafi shahara a tsakanin masu neman mafaka.














