Matakai biyar da gwamnatin Kano ke ɗauka kan matsalar tsaro

Asalin hoton, Kano State Govt.
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ɗauki matakai daban-daban domin daƙile sabuwar matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.
A baya-bayan nan jihar - wadda ke zama a matsayin cibiyar kasuwancin arewacin ƙasar - ta fara fuskantar hare-haren ƴanbindiga masu sace mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Ƙananan hukukomin jihar da ke fama da matsalar sun haɗa da Ƙiru da Tsanyawa da Ghari da Shanono da Tudun Wada da kuma Doguwa.
Ko a makon da ya gabata ma wasu ƴanbindiga ɗauke da makamai suka auka wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Tsanyawa inda suka sace mutane kusan 20, kodayake a ƙarashen mako sojoji sun bayar da rahoton kuɓutar da bakwai daga ciki.
A wata ziyara da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya kai ƙauyukan da ke fuskantar matsalar tsaron ya ce kashi 95 cikin 100 na ƴanbindigar da ke kai hare-hare jihar ƴan asalin jihar Katsina ne.
Abba Kabir Yusuf ya ce yana taƙaicin yadda mutanen Katsina waɗanda suke da addini da asali guda suka ajiye makamai da sunan sulhu a Katsina, amma suka koma Kano da hare-hare.
A lokacin ziyarar gwamnan ya tabbatar da ɗaukar matakan da suka dace a matakin gwamnatin jiha domin magance sabuwar matsalar tsaron da ke yi wa jihar barazana.
Ga wasu matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka tun bayan fara bayyanar sabuwar matsalar tsaron jihar.
Taron majalisar tsaron ƙananan hukumomi

Asalin hoton, Kano State Govt.
A farkon watan Nuwamba ne Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya umarci duka shugabannin ƙananan hukumomin jihar su riƙa gudanar da tarukan tsaro akai-akai domin ƙarfafa zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Taron zai ƙunshi shugabannin ƙananan hukumomi da manyan jami'an tsaro a matakin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a matakin ƙaramar hukuma.
Gwamnan ya ce matakin zai karfafa hanyoyin tattara bayanan sirri da musayar su a tsakanin al'umma da jami'an tsaro domin magance matsalolin da ke addabar yankunan.
Abba Kabir ya kuma ce gwamnatin Kano za ta ci gaba da bai wa ƙananan hukumomin hadin kai da aiki tare da jami'an tsaro domin tabbatar da cewa an hana ƴanbindiga da sauran masu aikata laifi samun mafaka a cikin jihar.
Saya wa jami'an tsaro kayan aiki
A tsakiyar watan Nuwamban ne kuma gwamnatin jihar ta ce ta bai wa rundunar tsaro ta JTF a jihar motoci 10 da Babura kusan 50 domin inganta tsaro a yankunan jihar da ke fama da matsalar tsaron.
Tun a farkon watan ne gwamnan ya yi alƙawarin samar da ababen hawa ga sojojin lokacin wata ziyara da babban kwamandan runduna ta ɗaya ya kai jihar Kanon a wata ziyarar ƙarfafa gwiwa da ya kai wa dakarun da ke yaƙi da ƴanbindiga a jihar.
Gwamnan ya ce ya bai wa jami'an tsaron ababen hawan ne da nufin tallafa wa ayyukansu na kawar da ƴanbindigar da ake addabar jihar.
Haka kuma ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa jami'an tsaro wajen yaƙi da 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma satar shanu.
Kafa rundunar tsaro ta jiha
A farkon shekarar nan ne Gwamna Abba Kabir ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaron al'umma ta jihar, mai suna 'Kano State Security Neighborhood Watch.'
Hakan na zuwa ne bayan dokar samar da rundunar tsaron ta bi matakan da doka ta tanada a majalisar dokokin jihar.
A yanzu haka gwamnatin ta ce sabbin jami'an rundunar na ci gaba da karɓar horon aiki, kuma nan ba da jimawa ba za a yaye su domin kama aiki.
Ana sa ran sabuwar rundunar - wadda ta ƙunshi matasan da aka bai wa horo - za ta taimaka wajen daƙile sabuwar matsalar tsaron da ke yi wa jihar barazana.
Jaddada hana acaɓa
A baya-bayan nan ne dai gwamnatin jihar Kano ta sanar da jaddada aiwatar da dokar hana sana'ar acaɓa ta shekarar 2013, wani mataki da ta ce zai taimaka wajen kare tsaro da rage laifuka, da tabbatar da doka da oda a faɗin jihar.
Ma'aikatar Shari'ar jihar ta bayyana cewa dokar, wadda ta daɗe tana nan daram kuma za a ci gaba da aiwatar da ita sosai.
Kwamishin shari'a na jihar, kuma babban lauyan gwamnati, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya buƙaci jama'a musamman masu baburan haya wato acaɓa su yi biyayya ga tanade-tanaden dokar.
Gwamnatin jihar ta ce matakin na daga cikin matakan inganta tsaron da take ɗauka domin magance sabuwar matsalar tsaron da jihar ke fuskanta.
Neman haɗin kan al'umma

Asalin hoton, Kano State Govt
A lokacin ziyarar da gwamnan ya kai ƙauyen Kamaye da ke yankin ƙaramar hukumar Tsanyawa ya buƙaci mazauna yankunan su taimaka wajen bayar da bayanan sirri ga jami'an tsaro.
''Waɗannan jami'an tsaron da kuke gani an kawo an jibge a garinku, ya kamata ku gode musu, kuma ba za mu zuba musu ido su yi aiki su kaɗai ba, a taimaka musu yadda ya kama''.
''Duk wanda ya ji labarin ƴanbindigar nan ko ya ji sun taho a taimaka a sanar da jami'an tsaron nan'', in ji gwamnan.
Sannan ya yi kira ga al'ummar yankin su duƙufa da yin addu'o'i a masallatai domin neman kariyar ubangiji.
Ko waɗannan matakan sun wadatar?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya, mai sharhi ne kan al'amuran tsaro a Kano kuma ya ce akwai ƙarin abubuwan da gwamnan Kanon ya kamata ya yi bayan waɗannan.
- Gina ingantaccen tsarin tsaro
Masanin tsaron ya ce yana da kyau gwamnati ta samar da wata katangar tsaro da ta ƙunshi jami'an tsaro na gwamnatin tarayya da na jiha da kuma masu unguwanni da dagatai.
''Wannan katanga ta ƙunshi shugabannin Fulani makiyaya da manoma da masu sana'o'i, domin yin aiki tare'', in ji shi.
Kyaftin Bakoji ya ce hakan zai inganta hanyoyin tattara bayanan sirri tare da magance kowace matsala tun tana ƙarama.
- Ƙarfafa wa matasa da sana'o'i
Kyaftin Bakoji mai ritaya ya ce yana da kyau kuma gwamnatin ta ɓullo da wasu hanyoyin tallafa wa mtasan jihar domin inganta sana'o'in dogaro da kai.
''A wasu lokuta irin wanna matsala na farawa ne daga rashin aikin yi, ko sana'a, don haka gwamnati ta riƙa ƙirƙirar cibiyoyin koyon sana'a a irin waɗannan yankuna, sannan a bai wa matasa tallafi da jari'', in ji shi.
- Inganta sabbin dabarun tsaro na gaggawa
Masanin tsaron ya ce yana kuma da kyau a samar da ƙananan rundunoni tsaro a kusa da wuraren da matsalar ta fi ƙamari.
''Hakan zai taimaka su riƙa kai ɗauki da zarar an samu wata barazana'', in ji shi.
Tsohon jami'in sojin ya kuma ce yana da kyau jami'an tsaro su samar da lambar kiran waya ta gaggawa, inda idan an samu wata matsala za a sanar da su cikin sauri.
- Fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya
Kyaftin Bakoji mai ritaya ya ce samar da fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya na daga cikin manyan batutuwan da suka kamata a kula da su.
''A kafa kwamitin gano rikici tsakanin waɗannan ɓangarorin biyu, da wuri, idan an samu shigowar wasu baƙi da ba a yarda da su ba, wannan kwamiti zai taimaka wajen sanar da jami'an tsaro da rage tunanin ɗaukar fansa'', in ji tsohon sojan.
- Tsananta sintiri a kan iyakar Kano da Katsina
Masanin tsaron ya kuma ce yana da kyau gwamnati da jami'an tsaro su tabbatar da samar da ƙarin jami'ai da za su riƙa sintiri a kan iyakar Kano da Katsina.
Gwamnan Kanon dai ya yi zargin cewa ƴanbindigar na tsallakawa ne daga Katsina domin ƙaddamar da hare-haren a Kano.
Don haka ne Kyaftin Bakoji mai ritaya ke ganin sintirin jami'an tsaro a kan iyakokin jihohin zai taimaka wajen daƙile matsalar.











