Man Utd ta ware mutum biyar don maye gurbin Carrick, Arsenal na son Goretzka

Michael Carrick sanye da bakar riga ya sa hannunsa a habarsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun bayan da United ta bai wa Carrick rikon-kwarya ta farfado a wasanninta
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United, ta ware wasu kociyoyi biyar da za ta iya zabar wanda zai maye gurbin Michael Carrick, da ke rikon-kwarya, a bazara - masu horarwar su ne - kociyan Crystal Palace, Oliver Glasner, da na Aston Villa Unai Emery, da Andoni Iraola na Bournemouth, da tsohon kociyan Brighton Roberto de Zerbi da kuma kociyan Jamus Julian Nagelsmann. (Sun)

Marcus Rashford, ka iya komawa Manchester United, bayan zaman aron da ya yi a Barcelona, wadda take sha'awar dan wasan gaba na gefe na Chelsea da Portugal Pedro Neto, mai shekara 26, a matsayin sauyinsa. (Mundo Deportivo)

Shi dai Rashford mai shekara 28, yana son zama a Barca, to amma tattaunawa a kan zaman nasa ta ci tura, abin da ya sa darektan wasanni na kungiyar ta Sifaniya, Deco ya bayar da shawarar, sake karbarshi aro a kaka ta biyu domin Barca ta samu damar cika ka'idar zabin sayensa kamar yadda yarjejeniya ta tanada. (Talksport)

Arsenal na shirin gabatar da tayin sayen dan wasan tsakiya na Bayern Munich da Jamus Leon Goretzka, mai shekara 31, a matsayin wanda ba shi da kungiya a bazara. (Teamtalk)

To amma kuma AC Milan ma na sha'awar Goretzka, wanda Bayern Munich, ta tabbatar cewa zai bar kungiyar a karshen kaka. (Goal)

Tottenham na duba zabin da take da shi na kociyan da zai maye gurbin Igor Tudor, idan har buatar hakan ta taso. (Athletic)

Yayin da kociyan na Tottenham, zai ci gaba da zama na dan wani lokaci, tuni ya ware wasu 'yan wasa ba ya sa su a wasa. (Talksport)

Napoli za ta fitar da yuro miliyan 44, kamar yadda yarjejeniya ta tanada domin sayen dan gaban Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 23, wanda ta karba aro, daga Manchester United, domin ya zama nata dindindin. (Fabrizio Romano)

Liverpool za ta gamu da gogayya da Barcelona idan ta nuna sha'awarta ta sayen dan bayan Inter Milan da Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 26. (Sport)

Manchester United ce kan gaba a masu son sayen dan wasan tsakiya na Bournemouth da Amurka Tyler Adams a bazara, inda Chelsea da Liverpool ma ke son dan wasan mai shekara 27. (Teamtalk)

Arsenal za ta iya samun kusan fam miliyan 1.7, idan bukatar Juventus ta sayen tsohon dan bayan Gunners din da Poland Jakub Kiwior, mai shekara 26, wanda ya tafi zaman aro Porto a watan Satumba tare da sharadin sayensa a kan kusan fam miliyan 23, ta tabbata. (Sun)