Rufewa
A nan za mu tsaya, tare da rufe wannan shafin na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe Asabar idan Allah ya nuna mana.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Juma'a 08/05/2026
Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Nabeela Mukhtar Uba
A nan za mu tsaya, tare da rufe wannan shafin na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe Asabar idan Allah ya nuna mana.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Ukraine da Rasha sun amince su yi musayar fursunonin yaƙi guda dubu daya daga kowanne ɓangare, a wani bangare na yarjejeniyarda ta ƙunshi tsagaita buɗe wuta na kwanaki uku tsakanin kasashen biyu.
Rasha ce ta bukaci tsagaita wutar na wucin gadi domin bikin tunawa da cika shekaru da kawo karshen yaƙin duniya na biyu.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce ya umarci dakarun kasarsa da kada su kai wani hari dandalin Red Square da ke Moscow da za a gudanar bikin.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an cimma yarjejeniyar ne bisa bukatarsa, yayin tattaunawar da ake yi domin kawo ƙarshen rikicin.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ci tarar wasu fitattun ‘yan wasanta biyu Euro dubu dari biyar-biyar, bayan wata hatsaniya da ta ɓarke a filin atisaye, wadda ta kai ga kai ɗaya daga cikinsu asibiti domin jinya, sakamakon raunin da ya samu a kai.
Dan wasan tsakiya na Uruguay, Federico Valverde ya samu rauni a Ƙansa, bayan cacar baki da dan wasan kasar Faransa, Aurelien Tchouameni wanda zai hana shi buga wasa na akalla kwanaki goma.
Real Madrid za ta kara da babbar abokiyar hamayyarta FC Barcelona gidan bankashi a ranar Lahadi, inda idan tayi rashin nasara zai bai wa Barcelona damar lashe kofin gasar Laliga karo na biyu a jere.

Asalin hoton, X/Nasir El-Rufa'i
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage zaman sauraron shari'ar da Nafi'u Bala Gombe ya shigar yana ƙalubalantar sabon shugabancin jam'iyyar ƙarƙashin Sanata David Mark, har illa masha Allahu.
Mai Shari'a Emeka Nwite shi ne ya sanar da ɗage zaman bayan da mai ƙarar ya sanar da kotun cewa ya nemi alƙalain alƙalai na babbar kotun tarayya da ya mayar da shari'ar zuwa ga wani alƙalin daban.
Shi dai Nafi'u Gombe yana ƙalubalantar kasancewar Sanata David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam'iyyar ADC, inda ya ce kasancewarsu a jagoranci ya saɓa dokokin jam'iyyar da dokokin zaɓe na Najeriya.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Aragchi, ya zargi Amurka da sadaukar da diflomasiyya saboda abin da ya kira tsantsar kasada da ɗanyen kai.
A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya ce duk lokacin da aka samu damar warware rikicin ta hanyar diflomasiyya, Washington kan zabi yin kasadar amfani da soji ba tare da tunani ba.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan da bangarorin biyu suka dora wa juna alhakin rikicin soja da ya auku a mashigar Hormuz, duk da tsagaita wutar yaƙi da Shugaba Donald Trump ke cewa har yanzu ta na nan daram.
MistaAragchi ya ce ko wane hali akai a rikicin, Iran ba za ta taɓa mika kai ga bori ya hau ba.
Wakilin BBC ya ce yana tunanin dukkanin ɓangarorin biyu na son cimma yarjejeniya, amma ba sa son yin na'am da daftarin da kowanne daga cikin su ke gabatarwa.

Asalin hoton, Getty Images
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce Washington na sa ran samun martanin Iran a yau Juma'ah kan ƙudurin zaman lafiya da ta aika mata.
Ya ce yana sa ran buƙatun Iran za su kasance na dattaku.
Ana ta hasashen tattaunawar na iya rugujewa a yayin da ɓangarorin biyu ke musayar wuta a Mashigar Hormuz.
Amurka ta ce ta buɗe wuta kan jiragen ruwan Iran biyu da ke ƙoƙarin tsallake shingen da ta sanya a tashoshin jiragen ruwan ƙasar a yau juma'a.

Asalin hoton, Getty Images
Maimakon makon nan ya karkata gaba ɗaya kan wasan da ke da matuƙar muhimmanci na El Clásico tsakanin Real Madrid da Barcelona, rahotanni sun mamaye shi da labaran rikici da rashin kwanciyar hankali a ɗakin canja kaya a Real Madrid.
Idan Real Madrid ta sha kashi a ranar Lahadi a wasan hamayya a La Liga, hakan zai bai wa Barcelona damar lashe kofin bana karo na biyu a jere, ita kuwa Real Madrid za ta kare kaka biyu a jere ba tare da ɗaukar kofin ba.
Sai dai yayin da Barcelona — wadda ita ma ta taɓa shiga rikici ba da dadewa ba — ke ci gaba da samun nasarori, Real Madrid na fuskantar ruɗani sakamakon rashin jin daɗi daga magoya baya da rashin tabbas kan makomar koci da kuma zarge-zargen rikici tsakanin ƴan wasa.
Rahoton BBC Sport ya duba abubuwan da suka faru a makon da ya gabata da kuma dalilin da ya sa suka ƙara tayar da hayaniya kan kakar da ta fara rushewa a fili da kuma cikin gida.

Asalin hoton, Lere Olayinka
Ministan Abuja Nyesom Wike ya kare gina gidajen da gwamnati ta yi wa alƙalai da sauran ma'aikatan ɓangaren shari'a a Abuja, inda ya yi watsi da damuwar da ƙungiyoyin lauyoyi ta nuna cewa hakan zai iya shafar ƴancin ɓangaren shari'a.
Wike ya bayyana haka ne a lokacin da yake zagayen duba ayyukan da ake yi na gina gidajen alƙalai da gyara da sauran ababen more rayuwa domin amfanin ma'aikatan ɓangaren na shari'a a Abuja.
Jawabin na minista na zuwa ne bayan ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya, NBA ta soki abin da ta kira yunƙurin katsalandan daga ɓangaren zarwasta na samar da ababen more rayuwa ga ɓangaren shari'a.
Wike ya ce tallafin gwamnati wajen samar da ababen more rayuwa ga alƙalai da sauran ma'aikatan shari'a ba sabon ba ne, kuma ba zai taɓa martabar ƴancin shari'a ba.
"Domin gwamnati ta yi gine-gine, hakan ba ya nufin za ta riƙa katsalanda a kan harkokin shari'a," in ji shi.
"A baya gwamnati ta gina gidaje ga majalisun tarayya da ma'aikatan shari'a. Ita kanta Kotun Ƙolin ai gwamnati ce ta gina. Don haka wannan ba sabon abu ba ne."

Asalin hoton, X/ADC
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage shari'ar da Nafi'u Bala Gombe ya shigar inda yake ƙalubalantar shugabancin jam'iyyar ADC tsagin tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark, har illa masha Allah.
Mai shari'a Emeka Nwite ne ya ɗage shari'ar bayan wanda ya shigar da ƙarar ya buƙaci a canza masa alƙalin da ke sauraron shari'ar.
Ɗaya daga cikin lauyoyin jam'iyar ADC DR Sulaiman Usman ya ce lamarin ya zo musu da bazata ganin cewa ɓangaren Nafi’u Bala ne suka shigar a ƙarar, sai kuma yanzu gashi su ke da ƙasa a gwiwa har suke nema a tura ta wata kotu, wanda kuma yin hakan zai sa shari’ar ta koma ƙasa.
A cewar sa kawai suna neman a kai su kotun da za ta yi musu abinda suke so ne ko abin da zai musu dadi, kuma a cewar sa ‘hakan bai dace ba a shari’a’.
Lauyan ya kuma ce za su mayar da martani ta hanyar rubutu ga babban alkali kan cewa babu hujjar da za ta sa a ɗauke shari’ar.
“ Babu wani abu da ya faru a shari’ar da wani zai kawo koke, sannan har kotun koli ta yabi alkalin saboda babu wani abu da ya taɓa yi na tauye wa wani haƙƙi ko nuna ɓangaranci ko rashin adalci’’. In ji lauyan.
Aƙalla mutum shida ne suka mutu a jihar Zamfara bayan da wabi abin fashewa ya tashi kan babbar hanyar Anka zuwa Bagega.
Wannan ne al'amari na baya-bayan nan a abin da hukumomi suka alaƙanta da ƙaruwar tashin hankali a yankin.
Ƴansanda a jihar Zamfara sun ce mutanen na kan hanyarsu ta tafiya lokacin da abin fashewar ya tashi har ma wasu guda shida suka ji rauni.
Harin na bayyana wani sabon salo da ƴanbindiga suka ɗauka na kai hari ta hanyar amfani da abin fashewa kan tituna.
Mazauna yankunan dai a yanzu na cikin zullumi a duk lokacin da suka kasance a hali na tafiya ko zuwa gonaki ko ma wasu ƙauyukan a sassan jihar ta Zamfara.
Jihar na ɗaya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da matsalar ƴanbindiga ta yi ƙamari.

Asalin hoton, @HQNigerianArmy
Sojojin da ke aiki ƙarƙashin rundunar Quick Response Force sun bankaɗo wasu masana'antun ƙera makamai ta haramtacciyar hanya guda biyu a yankin Vom da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau.
Jami'in yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Chinonso Polycrap Oteh ne ya sanar da haka cikin sanarwar da ya fitar inda ya ce samamen da aka tsara wani ɓangare ne na ƙoƙarin da rundunar Enduring Peace ke yi na daƙile hanyoyin da ake samun makamai ta haramtacciyar hanya da kuma yunƙurin kare al'ummar da ke yankin.
Samamen wanda ya faru bayan nazari da kuma tattara bayanan sirri ya taimaka wajen gano masana'antun ƙera makamai ba bisa ƙa'ida ba.
Yayin samamen, sojojin sun kama mutum biyar da ake zargi da ƙera miyagun makamai sannan kuma binciken da aka yi ya sa an gano tarin makamai da suka haɗa da bindiga ƙirar AK47 da alburusai.

Asalin hoton, Reuters
Kotun Kundin Tsarin Mulki a Afirka ta Kudu ta umarci majalisar dokoki da ta kafa kwamiti da zai yi bincike kan Shugaba Cyril Ramaphosa kan sama da faɗi da fiye da dala 500,000 daga gidansa da ke ƙauye shekaru shida da suka gabata.
Lamarin ya janyo zarge-zarge cewa shugaban ya gaza bayyana ta inda kuɗin ya fito.
Kotun ta yanke cewa majalisar ta ɗauki matakin da ya saɓa doka ta hanyar toshe yunƙurin tsige shugaban a 2022. A lokacin ƴanmajalisa sun kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa da wani rahoton kwamiti mai zaman kansa da ya gano cewa akwai dalilan da za su saka Mista Ramaphosa ya amsa tambayoyi game da satar.
A lokacin jam'iyyar Mista Ramaphosa ta ANC ce take da rinjaye, matsayin da ta rasa a zaɓen da ya gabata.
Matakin Kotun Tsarin Mulkin ta sa jagoran adawa a ƙasar, Julius Malema kira ga Shugaba Ramaphosa da ya sauka daga kan mulki.
Malema ya yi maraba da hukuncin kotun yana mai cewa ya kamata Ramaphosa ya yi murabus sannan ya mayar da hankali kan shirye-shiryen tsige shi saboda hakan na da mummunan tasiri a kansa.

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya Nimet ta yi gargaɗi cewa akwai yiwuwar jihohi 18 a ƙasar su fuskanci ambaliya cikin kwanaki masu zuwa sakamakon ruwa kamar da bakin ƙwarya da ake tsammanin yi.
A wata sanarwar gargaɗi da ta wallafa a shafinta na X jiya Alhamis, Nimet ta ce jihohin da ka iya fuskantar ambaliyar sun haɗa da Zamfara da Nassarawa da Kwara da Oyo da Legas da Ogun da Ekiti da Delta da Imo da Anambra da Enugu da Ebonyi da Akwa Ibom da Cross River da Rivers da Edo da Ondo da Bayelsa.
A cewar hukumar, ambaliyar na iya janyo tsaiko wajen wucewar motoci da yin ɓarna ga wasu gidaje da gonaki da gine-gine sai toshewar magudanan ruwa da rashin lantarki da matsalar sadarwa da kuma haɗurran yaɗuwar cututtuka.
Nimet ta kuma shawarci jama'a da ke jihohin da su ɗauki matakan da suka dace ta hanyar tsaftace magudanan ruwan da ke gidajensu sannan kuma su riƙa duba hasashen yanayi a kai a kai.
Hukumar ta gargaɗi masu ababen hawa da masu tafiya a ƙafa da su kaucewa yin tuƙi ko ma bi ta wuraren da ambaliya ta mamaye.
Gargaɗin na zuwa ne bayan da gwamnatin ƙasar ta yi gargaɗi cewa wasu jihohi 33 har da birnin tarayya Abuja na cikin haɗarin fuskantar ambaliya a 2026.

Asalin hoton, Getty Images
Mayaƙan ISWAP sun halaka sojojin Najeriya biyu da ke aiki ƙarƙashin rundunar Haɗin Kai a Magumeri da ke jihar Borno.
Lamarin ya faru ne yayin da dakarun da ke aiki ƙarƙashin rundunar suka daƙile wani harin ISWAP, abin da ya yi sanadin mutuwar ƴan ta'adda da dama har ma ta kai ga ƙwato makamai daga hannunsu.
Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Leftanar Kanar Sani Uba ya fitar wanda shi ne jami'in yaɗa labarai na rundunar Operation Haɗin Kai.
Samamen dai ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis lokacin da ƴan ta'adda suka yi yunƙurin mamaye wani sansani na rundunar.
Rundunar soji ta ce sojoji sun kai martani cikin sauri lamarin da ya sa suka daƙile harin tare da kashe mayaƙan da dama.
Daga cikin makaman da sojojin suka ƙwato a hannun mayaƙan akwai bindigoyi ƙirar PKT da AK47 da kuma tarin alburusai.
A cewar sanarwa, soja guda da wasu da suka ji rauni na samun kulawa.

Asalin hoton, Australian Federal Police
Wasu mata biyu da aka alaƙanta da ƙungiyar IS - mai iƙirarin jihadi - waɗanda suka koma ƙasar Australiya daga Syria sun bayyana a kotu a kan tuhumarsu da aikata laifuka da suka haɗa da mallakar baiwa.
Ana zargin Kawsar Abbas mai shekara 53 da sayen wata mata 'yar Yazidi a matsayin baiwa, tare da ajiye ta a gidanta.
Ita ma 'yar Kawsar dɗin, Zeinab Ahmed - ana tuhumarta da irin waɗannan laifuka biyu.
Akwai wasu matan biyu su ma da suka koma Australiya ranar Alhamis - ɗaya ba a tuhume ta ba tukunna, yayin da aka tuhumi ɗayar da kasancewa 'yar ƙungiyar ta'addanci.

Asalin hoton, CHESNOT / GETTY IMAGES
Chadi ta ayyana kwana 21 na dokar ta ɓaci a yankin Tafkinta bayan harin da ƙungiyar Boko Haram ta kai a farkon makon nan, inda ta kashe aƙalla sojoji 26.
Tuni ƙasar ta yankin Tsakiyar Afirka ta ayyana zaman makoki, bayan da mayaƙan Boko haram suka kashe wasu janar-janar na sojinta biyu a ranar Laraba, a lokacin da suke sintiri a wasu tsibirai a yankin tafkin.
Kafin wannan, ƙungiyar ta kashe sojoji 24 a wani hari da ta kai wani sansanin sojin ƙasar.

Asalin hoton, Anna Moneymaker / Getty Images
Shugaba Donald Trump ya ce har yanzu yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta na nan daram - duk da ɗauki ba daɗi da aka yi tsakanin jiragen yaƙin ruwa na Iran da Amurka a Mashigar Hormuz.
Wakilin BBC ya ce Amurka da Iran na zargin juna da fara buɗe wuta
Sojojin Amurka sun ce Iran ce ta harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa da wasu ƙananan jiragen ruwa a kan jiragen ruwanta na yaƙi uku kan abin da Amurkar ta kira haka siddan ba takala.
Ta ce a kan haka ne ta mayar da martani da hari kan kayan sojin Iran ɗin.
Iran ta ce ta mayar da martani ne a kan barazanar sojin Amurka a kan jirgin ruwanta na dakon mai da kuma wani jirgin dakon.
A halin da ake ciki kuma Haɗaɗɗiyar daular larabawa ta ce ta tare wasu makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa da Iran ta harba mata.
Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye, muna muku barka da zuwa shafinmu na yau Juma'a.
Kamar kullum, za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a duniya, kama daga yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran, da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta - Facebook da Instagram da YouTube da kuma X domin kallon bidiyo da kuma tafka muhawara.