Barca na son Haaland, Man Utd na zawarcin Fernandes

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta tattauna da Manchester City a kan Erling Haaland mai shekara 25, ko da kungiyar ta Firemiya za ta sa dan wasan na gaba dan Norway a kasuwa. (Sport)
Sai dai kuma wakilin Haaland din, Rafaela Pimenta, ya shiririntar da maganar ta Barcelona a wata hira ada aka yi da shi a wani gidan talabijin na Sifaniya. (Times)
Dan wasan tsakiya na Newcastle United Sandro Tonali, dan Italiya mai shekara 25, na cikin jerin 'yan wasan da Manchester United, ke son nema. (Sun)
Haka kuma Manchester United din na zawarcin dan wasan tsakiya na West Ham, Mateus Fernandes, na Portugal, mai shekara 21, wanda zai nemi barin kungiyar tasa idan ta fadi daga gasar Firemiya. (Talksport)
Watakila tsohon kociyan Liverpool Jurgen Klopp, zai bar aikinsa na matsayin shugaban harkar kwallon kafa na duniya na kamfanin Red Bull, domin ya koma aikinsa na kociya a matsayin mai horad da tawagar kasarsa Jamus bayan gasar Kofin Duniya. (Bild)
Newcastle na neman sabon mai kai hari a bazaran nan, duk da cewa ta kashe fam miliyan 124 a wannan bangare a bara, kuma matashin dan wasan Cologne da tawagar Jamus ta 'yan kasa da shekara 21, Said El Mala, mai shekara 19, na daga cikin wadanda kungiyar ta Firemiya ke hari. (Mail+)
Haka kuma kungiyar ta Newcastle ta kara bayyana sha'awarta a kan tauraron dan wasan tsakiya na Monaco, Lamine Camara, dan Senegal mai shekara 22. (The I)
Shi kuwa dan bayan Newcastle din Kieran Trippier, mai shekara 35, watakila kungiyar ta kulla sabon kwantiragi da shi yayin da Arsenal ke ci gaba da zawarcin Tino Livramento shi ma dan Ingila mai shekara 23. (Football Insider)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Juventus na daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin Robert Lewandowski, dan Poland mai shekara 37, wanda ake sa ran kwanriginsa da Barcelona zai kare a bazara. (Tuttosport)
wasu majiyoyi daga Liverpool sun yi watsi da jita-jitar da ake yi cewa kungiyar za ta sakar wa Real Madrid dan wasan tsakiya na Jamus, Florian Wirtz, mai shekara 22, bayan kaka daya kawai a Anfield. (Teamtalk)
Ana duba yuwuwar nada tsohon kociyan Everton da Burnley, Sean Dyche a matsayin wanda zai maye gurbin kociyan rikon-kwarya na Tottenham, Igor Tudor. (Independent)
Amma kuma ba lalle ba ne Dyche, ya amince da hakan, domin zai so rike matsayin har bayan kaka, aikin da kuma kungiyar ke duba yuwuwar nada wani daga cikin tsofaffin 'yan wasanta Robbie Keane ko kuma Ryan Mason. (Talksport)
A shirye Atletico Madrid take ta sayar da dan gaban ta na Argentina, Julian Alvarez, mai shekara 26, ga wata kungiyar Firimiya in dai za a biya ta fam miliyan 85, amma kuma ba za ta sayar wa da Barcelona ba. (Sport)
ita ma Inter Milan, za ta iya sayar da dan bayanta Alessandro Bastoni, mai shekara 26, da kuma dan wasanta na tsakiya Nicolo Barella, mai shekara 29, a bazara, idan har ta samu tayi mai kyau a kan 'yan wasan biyu na Italiya. (Gazzetta dello Sport)











