Abin da ya sa Haaland ya ci ƙwallo 100 a wasanni ƙalilan na Premier

Erling Haaland celebrates scoring against Fulham

Asalin hoton, AFP via Getty Images

    • Marubuci, Shamoon Hafez
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Manchester City reporter
    • Marubuci, Gary Rose
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • Lokacin karatu: Minti 4

Erling Haaland ya doke tarihin Alan Shearer na zura ƙwallo 100 a raga a gasar Premier League da mafi ƙarancin wasanni - ya kuma yi wanan bajintar a wasan da Manchester City ta doke Fulham ranar Talata a Craven Cottage.

Ɗan kasar Norway, mai shekara 25, yana taka rawar gani a kakar bana ta 2025/26, wanda ya zura ƙwallo 20 a wasa 19 a dukkan karawa kawo yanzu.

Haaland ya fuskanci Fulham da cewar wasa uku baya a jere bai samu cin ƙwallo ba, wato a karawa da Newcastle United a Premier League da Bayern Leverkusen a Champions League da kuma Leeds United a babbar gasar tamaula a makon jiya.

Amma ƙwazon da ya nuna ya sanya ya zama na farko da ya zura ƙwallo ta farko a raga a wasan mako na 14 a Premier League da City ta yi nasara 5-4 a gidan Fulham

Guardiola ya yi mamaki da Haaland ya yi wannan bajintar

Yanzu dai Haaland ya zura ƙwallo ta 100 a gasar Premier ranar Talata a Craven Cottage, amma za a ci gaba da lissafin ya zura na 101 da na 102 tunda har yanzu zai ci gaba da yin gasar.

Ya kuma buga ƙwallo ta bugi turke har karo biyu a wasan da Fulham, sannan ya bayar da biyu aka zura a raga, duk a wasan na ranar Talata.

Haaland ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a gasar Premier, inda yake da ƙwallo 15 a raga a kakar nan, yayin da ɗan wasan Brentford, Igor Thiago ke biye da shi, mai 11 a raga.

Tun bayan da ya koma Manchester City daga Borussia Dortmund a 2022, ya kafa tarihin bajinta da yawa a Ingila, ciki har da doke ƙwazon Shearer na cin ƙwallo 100 a wasa 111.

Sai da Shearer ya buga karawa 124, sannan ya zura ƙwallo ta 100 a gasar, sannan tsohon kyaftin ɗin tawagar Ingila ya ci 260 a matakin shi ne kan gaba a cin ƙwallaye a babbar gasar tamaula ta Ingila, wadda daga 1992/93 aka sauya mata fasali.

Ƙoshin lafiyar Haaland da rawar da yake takawa ce ta kai da ya zura ƙwallo 11 a bana, bayan da City take da 32 jimilla a raga a kakar nan.

''Ina taya ka murna'', Kamar yadda kociyan City, Pep Guardiola ya bayyana sanadiyyar bajintar da ɗan wasan ke yi a ƙungiyar.

"Me zan ce? Yau ya yi fice ƙwarai. Ya yi abin ban mamaki kuma ya zura ƙwallo mai ban sha'awa."

"Ina jin daɗin yadda yake taka leda, ina fatan zai ci gaba da sa ƙwazo da ci gaba da zura mana ƙwallaye a wannan ƙungiya."

Dan wasan City, Bernardo Silva, ya ce: "Erling har yanzu matashi ne kuma zai iya zama fitaccen ɗan wasan da ba za a taɓa yin irin sa ba a Premier League idan ya ci gaba da yin abin da yake yi yanzu."

Bajintar da Haaland ke yi a gasar

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Matthew Hobbs, ɗan jaridar wasanni a BBC

Yadda Erling Haaland ya zama ɗan wasan da ya zura ƙwallo 100 cikin wasanni ƙalilan a tarihin gasar Premier, ya kasance tamkar abun da aka yi hasashe tun daga kakarsa ta farko a Ingila.

Tun daga lokacin da ya ci ƙwallo 36 a kakar 2022/23 - tarihin cin ƙwallaye mafi yawa a tarihi a kaka a kuma fafatawa 33.

Kawo yanzu Haaland ya ci ƙwallo 100 a Premier League a wasa 111, ya bai wa Shearer tazarar wasa 13 kenan.

Haaland ya koma Manchester City kan fam miliyan 51 a kakar 2022, bayan kaka biyu da rabi a Borussia Dortmund mai buga Bundesliga, inda ya ci ƙwallo 62 a wasa 67 a lik.

Ƙwazon ɗan wasan mai shekara 25 tun bayan da ya koma taka leda a Premier League ya ɗara duk wani mai buga gurbin cin ƙwallaye a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Haka kuma shi da kansa ya tashi tuƙuru da ya samu damar yin wannan bajintar ta cin ƙwallo 100 a gasar Premier a kaka uku da yake buga wasannin.

Samun cin ƙwallo 100 da ya yi a Gasar Premier League ya zo a wani muhimmin lokaci a cikin sana'arsa ta ƙwallon ƙafa – fiye da shekara guda da ta gabata, wasu sun ce dan wasan City ƙwazonsa na yin baya.

Lokacin da Liverpool ta doke City 2-0 a Gasar Premier, ranar 1 ga Disamba 2024, inda Haaland ya kasa yin kataɓus a wasan, sannan ya kasa yin kokari, wanda ya zura ƙwallo daya a raga a wasa bakwai a dukkan gasa - karon farko a kakar da bai yi abin a-zo-gani ba.

Ɗan kasar Norway ɗin ya ci gaba da kammala kaka da mafi ƙarancin ƙwallaye tun bayan zuwan sa Ingila daga Bundesliga – amma abin lura shi ne kakarsa "mafi rauni" har yanzu ya haɗa da cin ƙwallo 34 a dukkan fafatawa, ciki har da 22 a cikin wasa 31 a Premier League.

Kawo yanzu a kakar tamaula ta 2025-26, Haaland ya zura ƙwallo 15 a raga a wasa 14 a Premier League, kuma 20 jimilla a dukkan fafatawa daga karawa 19.

Da yake kwantiragin tsohon ɗan wasan Molda da Salzburd zai kare a Etihad a karshen kakar 2034, watakila ya doke tarihin Alan Shearer a karo na biyu, wanda shi ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a Premier League mai 260 jimilla.