Me ya sa Real Madrid ke fuskantar matsaloli a bana?

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 7

Real Madrid ta yi wasa uku a jere a La Liga ba tare da nasara ba, hakan ya sa ta koma ta biyun teburi da tazarar maki ɗaya tsakani da Barcelona ta ɗaya.

Kawo yanzu Real ta buga wasa 14, daga ciki ta yi nasara 10 da canjaras uku aka doke ta wasa ɗaya shi ne wanda Atletico Madrid ta ci 5-2 a cikin watan Satumba.

Bari mu fara da lissafin yadda Real Madrid ta fara kakar tamaula ta 2025/26, wadda ta yi nasara bakwai a jere da cin ƙwallo 16 aka zura mata huɗu a raga.

Daga nan kuma sai ta sha kashi a gidan abokiyar hamayya Atletico Madrid a babbar gasar tamaula ta Sifaniya a makon ƙarshe na Satumba.

Rashin nasarar bai hana Real taka rawar gani ba, wadda daga lokacin ta ci wasa shida a jere har da doke Barcelona 2-1 a El Clasico.

Jimilla ƙungiyar ta Santiago Bernabeu ta ci wasa 13 daga 14 a dukkan fafatawa a kakar nan.

Bayan da Real ta ɗura 4-0 a ragar Valencia, sai ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Liverpool a Champions League a karawar da mai tsaron raga, Thibaut Courtois ya taka rawar da ba a ci Real ƙwallaye da yawa ba.

Daga nan sai Real ta tashi 0-0 a gidan Rayo Vallecano ranar 9 ga watan Satumba a La Liga, mai masaukin baƙi ta samu damarmaki da yawa, amma Coutois ya hana ƙwallaye su shiga ragarsa.

Daga nan aka samu hutun buga wasan kasa da kasa da ya kamata Real Madrid ta samu ta koma ganiya, amma sai ta kara ɓarar da maki a hannun Elche, wadda sabuwa ce a gasar ta La Liga a bana.

Real ɗin ta je ta tashi 2-2 a wasan ranar 23 ga watan Nuwamba.

Real Madrid ta buga gasar Champions League a gidan Olympiacos a Girka, inda ta yi nasarar cin 4-3, sai dai kuma Real ba ta taka rawar gani ba da ta kai an zura mata ƙwallo uku, kuma Kylian Mbappe ne ya ci mata huɗun.

An sa ran Real Madrid za ta huce a kan Girona ranar Lahadi a wasan mako na huɗu, sai aka fara zura mata ƙwallo, daga baya ta farke a bugun fenariti, kuma Mbappe ne ya ci.

Ranar Laraba 3 ga watan Disamba Real Madrid za ta je gidan Bilbao, domin buga wasan mako na 15 a La Liga.

Ta ina aka samu matsala daga Real Madrid?

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Har yanzu Real Madrid ba ta daidaita gurbin masu buga wasan gaba ba a matakin masu zura ƙwallaye a raga ba.

Kowa ya kwan da sanin cewar Jude Bellingham gwani ne kuma ƙwararre, amma an kasa samun daidaito tsakaninsa da Mbappe kan yadda za riƙa buga wa ƙungiyar tamaula.

Wani lokaci za ka ga cewar zalamar Mbappe ta sa ya koma gurbin ɗan wasan tawagar Ingila, shi ma yana haka, wasu lokutan sai su daburce a gurbi ɗaya.

Shi dai Bellingham bai fara buga wa Real wasannin ba a kakar nan, sakamakon jinya, amma ya fara taka mata leda a karawar hamayya da Atletico ta doke Real Madrid 5-2, wanda ba yadda za ka ɗora alhakin rashin nasarar a kan ɗan ƙwallon.

Tsakanin Oktoba zuwa Nuwamba da aka yi hutu, domin buga wasannin kasa da kasa, Bellingham mai shekara 22 ya koma kan ganiya, wanda ya ci ƙwallo ya kuma bayar da ɗaya aka zura a ragar Barcelona a wasan hamayya.

A wasan Barcelona da wanda Real Madrid ta sharara 4-0 a ragar Valencia ya nuna cewar Bellingham da Mbappe za su iya fitar da Real Madrid kunya idan har kowanne yana kan ganiya.

To sai dai a wasan Elche, Bellingham ne gwarzo, a karawa da Olympiacos a Champions League Mbappe ne ya taka rawar gani, amma a wasan Girona ba wanda ya yi fice a fafatawar ta ranar Lahadi a La Liga.

Kylian Mbappe da Jude Bellingham

.

Asalin hoton, Getty Images

Haka kuma a kakar 2023/24 Jude Bellingham da Vinicius Junior sun taka rawar gani, waɗanda ke kan ganiya har karshen kakar da ta wuce.

To amma tun daga lokacin ƴan wasan ba sa taka rawar gani kamar yadda suka yi a kakar da ta wuce, amma suna iya kokarin ganin sun fitar da kungiyar ƙunya.

Duk da cewar Mbappe yana cin ƙwallaye tun bayan da ya koma Real Madrid daga Paris St Germain, wasu kan ce yana nuna zalama.

Wasu lokutan a wasan Real Madrid sai ka neme shi ka rasa a gurbin mai cin ƙwallaye, sai kaga an bugo ƙwallon cikin da'ira, amma ɗan kasar Faransa na can gefen kusurwa.

A kakar tamaula ta 2023/24, kociya Carlo Ancelotti ya yi amfani da Rodyrgo domin taimaka wa Vinicius da kuma Bellingham.

Rodyrgo ɗan ƙwallo ne mai hazaka tukuru, wanda ke aiki sosai da ba kowa yake gane gudunmuwar da yake bayarwa ba a Real Madrid.

Wane salon wasa Alonso ke amfani da shi a Real?

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Ya kamata Xabi Alonso ya tantance salon da zai riƙa amfani da Jude Bellingham da Kyalian Mbappe da kuma Vinicius Junior a kowane wasa da zai yi amfani da su, domin su kasance kan ganiya da ƙwazo.

Hakan zai sa duk ƙungiyar da Real Madrid ta fuskanta ta ɗanɗana ƙudarta a hannun waɗannan ƴan gaba, saboda kowanne gwarzo ne da ƙwarewa da gogewa.

To amma hakan zai yi wuya a bana a ƙungiyar, kasancewar matasa irin su Arda Guler da Franco Mastantuono suna kokarin da ya kamata a riƙa fara wasannin da su a kakar nan.

Real Madrid na fuskantar ɗan karen ƙalubale a wasannin da take bugawa a waje, haka kuma canje-canjen da Alonso ke yi bayan kawo gagarumin sauyi, sai kaga ƙungiyar ta samu koma-baya kuma.

A karawar Girona, Alonso ya saka Gonzalo Garcia daf da za a tashi wasan, inda ya maye gurbin Trent Alexander-Arnold, wanda shi ke kai ƙwallaye ga ƴan gaba da Carerras shi ma daf da za a tashi daga karawar.

Ya kuma sa Rodrygo ya maye gurbin Aurelien Tchouameni, ba laifi ba ne ka saka dukkan masu buga maka gurbin cin ƙwallaye, amma dai an kasa samun daidaito a ƙungiyar a wasa da Girona.

Haka kuma ya saka Eduardo Camavinga ya maye gurbin Arda Guler bayan zagaye na biyu, amma duk da haka Real Madrid ba ta samu damar amfana da maki uku ba, wadda ta kare da samun ɗaya a gidan Girona.

Wace rawa Mbappe zai taka?

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

A kaka ta biyu, wato ta 2025–26, Kylian Mbappe ya karɓi riga mai lamba 10 daga Luca Modric, wanda ya bar Real Madrid a kakar da ta wuce, yayin da aka bai wa Endrick lamba tara.

A kakar nan kyaftin ɗin tawagar Faransa ya ci ƙwallo 14 ya kuma bayar da uku aka zura a raga a wasa 14 da fara La Liga.

Ranar 16 ga watan Satumba ɗan kasar Faransa ya ci wa Real Madrid ƙwallonsa ta 49 da ta 50 a wasan da ya ci Merseille 2-1 a Champions League.

Hakan ya sa ya zama na farko da ya ci ƙwallo 50 a Real Madrid a wasanni mafiya ƙaranci tun bayan bajintar da Cristiano Ronaldo ya nuna.

Ranar 30 ga watan Satumba, Mbappe ya zura ƙwallo ta 60 a Champions League har da cin uku rigis a wasa da Kairat, hakan ya sa ya haura Thomas Muller, ya zama na shida a jerin masu rike da wannan tarihin a gasar ta zakarun Turai.

Ranar 26 ga watan Nuwamba ɗan kasar Faransa ya ci Olympiaocos ƙwallo huɗu rigis.

Wane gyara ya kamata Real Madrid ta yi?

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Idan har Real Madrid tana fatan komawa kan ganiya tana bukatar gyare-gyaren da za su sa ta kara rike kambinta.

Na farko tana bukatar mai tsare baya daga tsakiya da wani mai tsare bayan amma daga tsakiyar fili da fitatcen mai cin ƙwallaye da kuma ɗan wasan tsakiya ɗaya.

Ya zama wajibi Real ta yi duba na tsanaki kan ƴan wasan da ke buga mata ɓangaren gefe da tsarinsu bai yi iri ɗaya da na ƙungiyar ba, kuma ta yi waje da masu yawan jin rauni da suke daɗewa suna jinya da waɗanda ke wasan gurbin tsakiya marasa tasiri.

Haka kuma ya kamata ta riƙe tsarin salon wasa na 4-3-3, sannan ta fitar da waɗanda take ganin za su iya yin abinda ake bukata, domin kai hare-hare a koda yaushe.

Haka kuma ya kamata kawo yanzu Real Madrid tana da ƴan wasa 11 fitattu da za ta iya fuskantar kowacce ƙungiya, a maimakon yawan sauye-sauye, wanda a wani lokacin hakan ba ya fitar da ita kunya.

Sannan ya kamata Real ta samar da fitatcen mai cin ƙwallaye, za kuma ta iya sa Endrick, kafin ta je kasuwa.

Ya kamata a fayyace jagora a Real Madrid ƙarara tsakanin Vinicius ko kuma Mbappe.

Haka kuma ta yaya za ta amfana daga wajen masu buga mata gurbin tsakiya tsakanin Valverde da Camavinga da kuma Bellingham.

Haka kuma daga ɓangaren masu tsaron baya ta dogara da Militao, sannan ta sayo wani mai tsare baya daga tsakiya da zarar an buɗe kasuwa.

Sai kuma ƙungiyar ta dawo da tasirinta a gasar zakarun Turai ta Champions League, ta hanyar tsare baya yadda ya kamata tunda tana da fitatcen mai tsare raga.

Daga karshe Real Madrid na bukatar samar da tsarin salon taka leda na ƙungiyar ba wai dogaro da gogewar ƴan ƙwallonta ba, hakan akwai rauni matuka.