Sau nawa Taylor ya busa wasan Chelsea da Arsenal a tsakaninsu?

Anthony Taylor

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Anthony Taylor ne zai yi alkalancin wasan Premier League karawar mako na 13 tsakanin Chelsea da Arsenal a Stamford Bridge ranar Lahadi.

Kawo yanzu Taylor ya busa wasa 16 a kakar nan da ya haɗa a Premier League da gasar zakarun Turai da ta neman shiga gasar cin kofin duniya.

Wannan shi ne karo na 11 da Taylor zai yi alkalancin tamaula a Premier League a bana, wanda ya raba katin gargadi 53 da jan kati ɗaya shi ne wanda ya kori, Jonas Adjetey na Basel a karawa da Copenhagen ranar 20 ga watan Agusta da bayar da katin gargaɗi bakwai a ranar.

Haka kuma alkalin ya busa wasan da ya shafi Chelsea da kuma wanda Arsenal ta fuskanta a kakar nan, kenan ba wani sabon aiki zai gudanar ba ranar Lahadi.

Taylor ne ya yi rafli a wasan da ƙungiyoyin suka fuskanci juna a 2016-17 da kuma 2019-20 a FA Cup, kuma Gunners ce ta yi nasarar wasan biyu da cin 2-1.

Kuma Chelsea ta karasa kowanne wasan da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili a fafatawar da ta jawo cece-kuce.

Taylor ya bai wa Mateo Kovacic katin gargaɗi na biyu da jan kati a 2019/20, saboda keta da ya yi wa Granit Xhaka, amma da aka sake duba lamarin sai aka gane cewar ɗan kasar Croatia aka yi wa ketar.

An kuma bai wa Victor Moses na Chelsea jan kati a zagaye na biyu a 2016/17

A kakar 2016/17, Alexis Sanchez ya fara ci wa Arsenal ƙwallo, duk da cewa an yi ta korafin ya taɓa da hannu.

Sau nawa Taylor ya yi rafli a wasan Chelsea

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Taylor ya yi alkalancin wasa 56 da ya shafi karawa da Chelsea kawo yanzu, wasan da ya fi yawan rafli shi ne da ya kunshi karawa da Liverpool, wanda ya yi 68.

Magoya bayan Chelsea ba sa jin daɗin busan da Taylor ke musu a wasanninsu, inda suke zarginsa da baya yi musu adalci.

Taylor ya bayar da katin gargaɗi ga ƴan wasa Chelsea sau 128, fiye da sauran ƙungiyoyin da ya yi wa alkalanci.

Ya kuma bai wa ƴan wasan Chelsea jan kati uku har da biyu a wasan karshe a FA Cup da ya haɗa da ɗaya a 2016/17 da kuma ɗaya a 2019/20

Taylor ya kafa tarihin bayar da katin gargaɗi 14 da ya shafi wasa da Chelsea a bara.

Chelsea ta yi nasara biyar baya a karawar da Taylor ya yi mata alkalanci.

Wasannin da Taylor ya busa wa Chelsea a tarihi:

Ya busa wasa: 56

Ta yi nasara: 29

Ta yi canjaras: 14

An doke ta: 13

Ta haɗa maki 86 a lik

Taylor ne ya yi alkalancin wasan da Chelsea ta doke Liverpool 2-1 a Premier League a kakar nan.

An kuma yi mamaka da katin gargaɗi biyu ya bayar, kuma dukka ƴan wasan Liverpool ya nuna wa.

Sai dai bai bayar da fenariti ba a lokacin da aka yi wa Alejandro Garnacho keta a da'ira ta 18, bayan da Chelsea ta yi korafi, to sai dai VAR ta tabbatar da hukuncin da Taylor ya yi.

Sau nawa Taylor ya yi alkalancin wasannin Arsenal?

Taylor

Asalin hoton, Getty Images

Haka dai Taylor ya yi alkalancin wasa 56 da ya shafi fafatawa da Arsenal, inda Gunners ta yi nasara 32 daga ciki.

Wasa takwas ta yi rashin nasara da kuma canjaras 16 a wasannin.

Haka kuma akwai hukunce-hukuncen da Taylor ya yi a wasan Arsenal da magoya baya ke jinhaushinsa.

Domin ya bai wa ƴan wasa Arsenal jan kati bakwai, ita ce ƙungiya kan gaba da Taylor ya korar mata ƴan wasa a alkalancin da ya yi mata.

Ba a doke Arsenal a wasa tara a bayan nan da Taylor ya busa mata.

Wasannin da Taylor ya busa wa Arsenal a Tarihi:

Ya busa mata wasa: 56

Ta ci: 32

Ta yi canjaras: 16

Aka doke ta 8:

Ta samu maki 94 a lik

Taylor ne ya busa wasan hamayya na ƴan birnin Landan da Arsenal ta yi nasara a kan Fulham a Craven Cottage.

An dai samu takaddama lokacin da Taylor ya bai wa Arsenal fenariti, sakamakon ketar da Kevin ya yi wa Bukayo Saka.

Daga baya VAR ta soke hukuncin, amma magoya baya sun ji kamar ba a ƙyauta musu ba a hukuncin.

Haka kuma ba a bayar da kati ko ɗaya ba, duk da keta 15 da aka yi a wasan, inda Fulham ta yi 11 daga ciki.

Ko mai zai faru a busan da Taylor zai yi a wasan Chelsea da Arsenal

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Wasa biyar da Taylor ya yi rafli a kece raini tsakanin Chelsea da Arsenal, ya bayar da katin gargaɗi 19 da jan kati biyu.

Ya kuma bayar da bugun fenariti biyu, kowacce ta buga ɗaya.