Fitattun ƴan wasan gaba huɗu da ke tashe a nahiyar Turai

Haaland da Mbappe da Osimhen da kuma Kane

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Har yanzu ana ci gaba da muhawara kan irin rawar da ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen ya taka a wasan da ƙungiyar ta Galatasaray da doke Ajax da ci 3-0, a gasar Zakarun Turai da suka buga a daren da ya gabata, inda ya ci ƙwallo uku rigis.

Shi ne ɗan wasan Najeriya na biyu da ya taɓa cin ƙwallo uku rigis a gasar Zakarun Turai.

A yanzu haka shi ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a Gasar Zakarun Turai ta bana, inda yake da shida.

Baya ga Victom Osimhen akwai kuma wasu fitattun ƴanwasan gaba uku a Turai da ke kokawar lashe takalmin zinare a bana saboda irin ƙoƙarin da suke yi wajen zura ƙwalaye.

Masana ƙwallon ƙafa na alaƙanta ƙoƙarin ƴan wasan da burinsu na lashe babbar kyautar ƙwallon ƙafa ta duniya wato Ballon d'or.

A wannan muƙala mun duba wasu ƴanwasan gaba huɗu da a yanzu ke ƙoƙari a gasanni daban-daban da ƙungiyoyinsu ke bugawa a Turai.

Kylian Mbappe

Klian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Ɗan wasan gaban na Real Madrid na daga cikin ƴan wasan gaban da suke haskakawa a wannan shekara.

A kakar wasa da ta gabata ne ɗan wasan na Faransa ya koma Real daga PSG, sai dai ya fuskanci koma-baya sakamakon wasu matsaloli da Jantile ya alaƙanta da na tunani.

Jantile ya ce dama Real Madrid ta kawo Mbappe ne domin samun nasarori kasancewarsa dodon raga.

A yanzu haka ɗan wasan ya ci ƙwallo 21 a duka gasannin da ya buga kawo yanzu.

Harry Kane

Harry kane

Asalin hoton, Getty Images

Ɗan wasan gaban na Ingila ya kasance ɗaya daga cikin ƴanwasan da a yanzu ake kwatance da su.

Kane ya koma Bayern Munich daga Tottenham inda ya kwashe shekaru yana buga gasar Premier.

Jantile ya ce ba ƙaramar dabara Kane ya yi wa kansa ba da ya koma Bayern Munich.

Masanin ƙwallon ƙafar ya ce Kane bai samu wata tasgaro bayan komawa Jamus ba, kasancewar salon ƙwallon Ingila ta yi kama da ta Jamus da Italiya.

''Kuma wani abu da ɗan wasan ya yi zarra shi ne yadda ya ƙware wajen sanin wurin da zai tsaya idan za a ba shi ƙwallo (positioning), ya san yadda zai ware kansa domin karɓar ƙwallo'', in ji shi.

Ya ce wannan ne dalilin da ya sa ɗan wasan ke yawan cin ƙwallaye a wasanni.

Ya zuwa yanzu ɗan wasan gaban ya zura ƙwallo 28 a wasa 22 da ya buga a duka fafatawar da yi a wannan kaka.

Erling Haaland

Erlin Haaland

Asalin hoton, Getty Images

Tun bayan zuwansa gasar Premier League ta Ingila a shekarar 2022, ya nuna kansa a matsayin ƙwararren ɗan wasan gaba.

Bashir Jantile na ganin cewa nan ba da jimawa ba ɗan wasan na Norway ka iya zama ɗan wasa mafi tsada a duniya.

''Dalili ne shi ne har yanzu ɗan wasan na da ƙarancin shekaru, sannan yana da ƙarfi ga kuma ƙwarewar da yake da ita'', in ji shi.

''Ina mai tabbatar maka cewa sai an wayi gari manyan ƙungiyoyin duniya sun saka maƙudan kuɗi domin ɗaukar ɗan wasan''.

Yanzu haka ɗan wasan na zura ƙwallo a kusan duka wasan da ya buga a dukkan gasanni.

Victor Osimhen

Victor Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

Ɗan wasana gaban na Najeriya ya koma ƙungiyar Galatassary mai buga gasar Turkiyya daga Napoli, bayan da ya taimaka wa ƙungiyar lashe kofin Serie A a kakar wasa ta 2022/2023 karon farko cikin shekara 33.

Osimhen ya taimaka wa Galatasaray a gasar Turkiyya ta hanyar zura ƙwallayen da suka taimaka wa ƙungiyar ɗare wa kan teburin gasar.

Bashir Jantile ya ce abin da ɗan wasanb yake yi yanzu ba abin mamaki ba ne, inda ka yi la'akari da ƙoƙarin da ya yi a gasar Italiya da ya baro.

''Ya samu gogewa ta hanyar fafatawa da manyan ƙungiyoyin Italiya irin su Inter Milan da AC Millan da Juventus, don haka yanzu da yake Turkiya tamkar ɓagas ya samu na nuna kansa'', in ji shi.

Masanin wasannin ya ce komawa Turkiyya da ɗan wasan ya yi, dabara ce da ba kowa ne ya fahimceta ba, saboda zai ƙara inganta kansa.

''Kasancewarsa matashi da bai rufa shekara 30 ba, yana da makoma mai kyau idan har ya tafi da irin wannan ƙwazo'', in ji Jantile.

Mene ne sirrin ƴanwasan?

Bashir Jantile ya ce babban abin da ke taimaka wa waɗannan gwarazan ƴanwasa nuna kansu shi ne morewa da suka yi da fitattun ƴan wasan tsakiya.

Masanin wasanin ya ce duk inda ka samu ɗan wasan gaba abin da kawai yake buƙata wajen zura ƙwallo shi ne gogaggun ƴanwasan tsakiya.

''Galibi a duka ƙungiyoyin da waɗannan ƴanwasa ke bugawa ko ƙasashen da suke za ka taras akwai ƙwararrun ƴan wasan tsakiya da ke taimaka musu''.

Wane ne zai lashe takalmin zinare a Turai?

Kyautar takalmin zinare

Asalin hoton, BBC Sport

Kyautar takalmin zinare wata kyauta ce da ake bai wa ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a tsakanin manyan gasannin Turai biyar a ƙarshen kowace kaka.

To amma Bashir Jantile ya ce yana sa rana Haaland ne zai samu wannan kyauta a bana, kasancewar yadda yake zura ƙwallaye.

''Gaskiya na zaɓi Haaland saboda kusan a duka wasa sai ya zura ƙwallo a raga, to indai ya tafi a haka zai yi wahala bai lashe kyautar ba'', in ji shi.